Sashe 76
Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ruwan ya cigaba da dukan rufin dakin da wani irin ™arfi fiye da kodayaushe. Karar tsawa da ake yi lokaci-lokaci tana cika iska da sautin da duk karfinsa baya disashe tarin surutun daje cikin dakin, tarin surutun dakin kurkukun wanda yake cike da fuskokin mata kala-kala. Manya -manya da yara farare da bakake, dattojai da yanmata wanda kowanne a cikinsu yake cigaba da rayuwarsa daidai kamar babu wanda yake da digon koda memory guda na wani abu daga bayan dogwayen katangar da suka zagaye su, kamar nan din shine mafari kuma farkon rayuwarsu, kamar basu san akwai wata duniya dake wanzuwa bayan su ba.
Rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kadan, wannan shine abinda Kilishi je maimaitawa a cikin kanta da fitowar kowacce rana da kuma faduwarta. Ta yarda rayuwa bata da adalci don babu abinda ke saka ta tsayawa, komai girmansa kuma komai kankantarsa ba abinda ke tsaida ita kamar dai ruwan daje zuba a yanzu, abubuwa suna cigaba da tafiya ne ba tare da wani ma yaje ko kusa da wajen da zai ji labarinka ba.
Damina ta dade da tsayawa ta yadda kusan kullum ake kwara ruwan dake daukar awanni, kuma a duk lokutan da ruwan ke sauka, Kilishi na samun waje ne dab da wata yar karamar taga dake can sama ta zauna, ta zauna tana kallon tasirin zubar ruwan da kuma nauyinsa da take ji a zuciyarta, tana ayyanawa kanta cewa hawayenta ne wannan ke zuba, don irin kukan da ya kamata tayi kenan tunda a kirjinta dama idanunta babu danshi ko kadan balle ayi tunanin hawaye.
Ta kan so ayi ruwan lokacin da suke fita waje don ta zauna a cikinsa ya sauka a jikinta, ya sauka akan fuskarsa ta yadda zata ji sosai kamar hawayen nata... Idanunta a tsaye kyam suna shsida kamannin da ta sani cewa ba nata bane, ba itace wannan Kilishin da tayi wata rayuwa da zata rantse da ubangijin da ya halicce ta babu wata mace a cikin kurkukun nan da tayi makamanciyarta.
Ba itace wannan Kilishin dake samun komai a zama daya da zuciya da kuma kwakwalarta ke sama mata mafita ba, sannan ba itace wannan Kilishin da ta shafe tsawon shekaru wajen gwagwarmayar samawa karshen rayuwarta tare da yayanta wata daddadar rayuwa da bata ko misaltawa ba.
A yanzu ita wata sabuwar halitta ce kawai, wata sabuwar halitta da ta rasa kowa kuma ta rasa komai, amma kuma zuciyarta ta kasa yarda ta karbi hakan, don idan ma zata yarda tana tunanin ya kamata ace ko da rabin mutanen duniya su jajanta mata, amma ba wai rayuwa ta cigaba da tafiya tamkar babu wani abu da ya faru ba.
_A tuhume ta akan kisan Wana kawai yallaSai..._
Tun da aka fara wannan tashin hankalin, wannan maganar ta Baffa ita kadai ce abinda ya fitar da hawaye daga idanunta bayan maganganun Ma'aruf, yace a ture dukkan wasu laifukanta a gefe, a tuhume ta kisan Jamal kawai wanda ta san yayi haka ne don ya tanadar mata wani abun daban.
Ko a lokacin da aminiyarta Salamatu ta baiyana a gabanta da tare da yanuwanta game da zancen raba ta da dan ta tsawon shekaru bata ji wsni abu sosai ba,don me take tunanin? Awwalu zai cigaba da lullube duk wani sirri nata da ya sani ne? Bakin cikinta daya ne ma da ya zamana akace Salanatun taga Wan nata, wani abu da duk da mamakin da ya bata sai da taji ciwonsa har cikin kirjinta.
Salamatu bata taba taya ta mugunta ko guda daya ba,hasali ma ta kan kushe mata wasu idan ta kawo su, amma duk da haka tare suka faro tafiyar tana gaya mata dukkan sirrinta da kuma abinda take ciki don haka ko yaya ne yaci ace itama ta karbi nata kamashon bakin cikin, ba'ace ita da Awwalun dai sune kadai zasu dandani zafin shari'ah ba.
A lokacin da dansandan nan yaki karbar tayin kudin da tayi masa, a lokacin da ya kalli nambobin da ta rubuta ya dago ya sake kallonta sannan ya girgiza kansa, a lokacin wata wuta ta kunno a cikin kirjinta, wata wuta dake zafi tana kona duk wani ragowar emotion da take dashi tana kuma kara zafin kunci dake cikin zuciyarta wanda karara yake nuna mata cewa da gaske ne tata ta kare babu wata sauran mafita kuma.
Daga wannan lokacin ta koma kamar wata gunki da aka sassaka ko kuma karfen dake motsi kawai, numfashi kawai take tana kallon tarin mutanen dake zuwa koyaushe wajen mata tambayoyin da bata ko fahimtarsu, ciki har da ´an jaridar da tayi zaton zasu watsa labarin nata zuwa kusufa-kusfar da zai sa duniya ta tsaya wajen jimanta mata, amma kamar yadda tace rayuwa bata da adalci, ba abinda ya faru!
Bata yi magana da kowa ba sai da akaje kotun sannan ta amsa dukkan tambayoyin alksli kai tsaye babu wani musantawa ko kuma kokwanto, tana bayar da amsar tana kallon idanunsu Baffa, Baba Usman, Ishaq, Abdurrahim da kuma tarin wadu yanuwanta da acikinsu har da mahaifin Amina, Alhaji Sulaiman.
To don me ba zata amsa ba, ai ba su kawo wanda zasu daure ta da jijiyoyin ta a jikinta ba, basu kawo wanda da yana wajen ta sani bakinta ba zai taba budewa ta amsa laifukan da aka zaiyano a cikin kunnensa ba... Ma'aruf!
Ya sani, ya san komai, ya san komai din da ya zamana ta san baya cikin haiyacinsa ma a lokacin, amma duk da haka da ace yana wajen, yana cikin kotun nan a lokacin da ake sauraren shari'ar, zata rantse da ubangijin da ya halicce ta cewa ko alkalin zai ce a kwantar da ita ana yankar naman jikinta Wai-Wai da Wai-Wai, ba zata taSa iya amsa wadannan laifukan a gaban idon Ma'aruf ba.
Amma har Baffa tana kallonsa ne kawai tana amsawa tare da tunanin abinda zai ji amma ba wai ita ba, har aka gama shari'ar aka yanke mata hukucin shekaru goma sha takwas bata jin ko da wucewar sakan guda taji nauyin wani daga vikin mutanen dake wajen nan.
A yanzu ma ´a´an ta kawai take tunawa, tana jin yadda rashin ganinsu ke Sangarar da wani abu a cikin zuciyarta, yanuwanta da yawa sun zo, musamman wadanda take yiwa alkhairi, wasu ma bata ko fita ganinsu saboda bata ga abinda hakan zai tsinana mata ba.
Don haka a yanzu rashin ganin yayan nata shine abu mafi tashin hankali da take fuskanta bata ko lissafin shekarun da zata kwashe a cikin wajen nan,don gani take kamar an fade su ne a kotun nan kawai, kamar an fade su ne kuma an rubuta amma baza su kasance a gaske ba... Gani take kamar zata iya fita, kamar idan ta yun™ura zata samu hanyoyin da zata fitar da kanta.
Amma matsalar shine har yanzu zuciyar tata ta kasa fahimtar komai a wajen na balle har ta fara tunanin hanyoyinta, Baffa yana kassarata da wucewar kowanne lokaci a duniyar nan wajen hana ta ganin fuskokin ´a´an ta, ita Kilishi ce, mai zurfin tunani da hangen nesa, shi yasa a lokacin da yace a ture dukkan wani laifi a hukunta ta akan abu daya kawai ta zubar da hawayenta.
Shi mijinta ne, ta san halinsa tsawon shekaru,ta san yadda yake iya hukunta mai laifin dake hannunsa cikin salama ba tare da kowa ya sani va, hukuncinsa mai sanyi wanda zai daskarar da jinin jikinka hankali kwance yadda duk ihunka babu wanda ya isa ya ji ka, shi yasa yake da kai zuciya nesa a komai na rayuwarsa, da wuya kaga ransa ya baci akan wani abu don idan har ya bacin to shi kansa ya sani cewa hukuncin da zaiyi daban ne,ta san wannan... ta san wannan tun a shekarun farko data aure shi.
Shi yasa zuciyarta take rabewa da kowanne motsawar lokaci idan ta tuna hakan, idan ta tuna yadda rayuwar kowa ke cigaba da tafiya babu ita kuma kamar ba'ayi ta din ba, don yanuwanta sun gaya mata cewa har sake gini anyi a gidan an rushe bangarenta.
Mamakin yadda rayuwa ke juyawa dan adam baya a lokaci guda shi ke dada cinye ta, kamar badu saba ba, kamar ba itace mai yarje mata komai ba, kamar ma bata santa ba, ace komai ya ™are a lokaci guda? Komai din da zai hada har da ya'yanta, banda wannan tarin dukiyar da ta shafe shekaru tana ajiyarta, shi yasa a kullum take fada tana karawa rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kankani....
Tana zaune ne kawai a yanzu ba tare da wata mafita ba, abu biyu kawai take hasashe shine watakila idan har ta mike da ™arfinta da kuma dabararta ba lallai ne ta kai wannan shekarun da aka gindaya mata a kotu ba, amma kuma matsalar shine bata da karfin, a kullum kuma a kowanne wayewar farin Allah Baffa yana kara kassarata ne da hukuncinsa na hana ta ganin yayanta... Shi yasa duk yadda ta kai ga ture wani tunani a zuciyarta tana ji kamar zata yarda dashi akan cewa.
Karshen tika tika dole TIK ne! Dole ne ta yarda cewa komai ya kare mata, kuma dole nrme ta yarda da abinda Ishaq ya kalli cikin idanunta ya fada mata a ranar da za'a kawo ta gidan nan...
*'Wata shari'ar sai a lahira Mami...!'*
Rugugin tsawar da ake yi ya cika iska a lokacin, walkiya ta haska tar ta kuma haskawa a cikin duhun hadarin, sai kawai ta sake Waga idanunta tana kallon zubar ruwan ta cikin tagar Wakin, ta cikin hayaniya da kuma dararrakin mutanen dakin, kuma ba tare da tayi zato ba a lokacin wata guntuwar ™walla ta cika idanunta tana gangarowa kan fuskarta, wannan shine karo na uku da taji dumin hawaye a kan fatarta, kuma wannan lokacin shine karo na farko da tambayar da ta™i bari ta yiwa kanta tun a zamanin farko ta Warsu a cikin zuciyarta... Wannan tambayar da take gujewa, tambayar da bata taSa lissafa ta ba balle ta yi tunanin matsayinta na Kilishi zai kai ta ga yinta....
Ta yaya zata mayar da rayuwarta baya shekaru goma da suka wuce?
Dana sani....! Yau Kilishi ce da dana sani!
Dana sani a lokacin da komai ya kure!
Dana sani irin wadda kowanne musulmi ke gudu a duniyar nan!