Sashe 40
Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shi yasa bana son zuwa ai, kin san ni duk inda za'a wulankanta ni ko a raina ni ba son zuwa nake ba, wallahi ko da su Amma suka tafi Jigawa kai Aminun nan da muka je gidan Kawu Mallam baki ji yadda na dinga ji ba, na tsani a dinga min iko da abu."
Sanin wannan halin nata sarai yasa Amina bata ja zancen ba tace.
"Allah ya taimake ki kar Baba ya miki irin nawa."
Sai ta girgiza kanta tace.
"Wallahi ba zan iya ba Yaya, ba zan taba iyawa, nifa kinga ko kayan gidanki da na san da yawa nasu ne, zasu sa zuciyata ba zata nutsu wani ya shigo ya gaya min magana...Don ma dai Hajiya Kilishi ce, da sauki ta saba mana alkhairi, shi yasa ma banji komai sosai ba ko a wannan tafiyar dasu Baba zasu yi."
Amina tana murmushi tace.
"Allah ya shirye ki Maryam."
A wajenta dukkan wannan abin da take faWa tatsuniya ce kawai, don bata san tarin kalolin da rayuwa ke haskawa Wan adam ba.
Daga haka idonta ya jai waje inda Amma ke zaune da kwano a gabanta da kuna Hafsa da ta shigo a lokacin daga islamiyya tana tambayar.
"Har yanzu su Yaya suna nan?"
"Wai ina Aminun yake ne ma?" Amina ta tambaya.
Maryam ta tabe bakinta tace.
"Abokanansa ai ba sa kyale shi tunda ya dan ji saukin nan, yanzu zaki ji sallama sun shigo sun gara wheelchair din sun fita dashi musamman yanzu da suka san jibi za'ayi tafiyar nan."
Kafin Amina tace wani abu Hamida dake kan cinyar Maryam din ta taso da sauri tana nuna mata kunshin da aka gama da murnarta.
"Babydoll yayi kyau?"
Wani abu ya ratsa cikin kan Amina, ta rasa ta yadda zata yi yarinyar nan ta daina kiranta da haka, Ma'aruf ya vuvi kwakwalarta da yawa, kuma kagin ta amsa idon ta ya gano mata Hafsa, sai kawai tayi wajen da sauri tana fadin,
"Aunty Hafsa come look, zo ki gani me aka min
..."
Mamaki ya kama dukkaninsu. Maryam ta gyada kanta tace.
"Ina gaya miki Hafsa ta ™ar rashin mutunci yarinyar nan, yanzu wai daga zuwanku har ta san ta gaya mata sunanta Aunty Hafsa...? Bari Adam yazo kuma mu ji Uncle Adam."
Dukkaninsu suka yi dariya Amina na fadin,
"Ni na san kamar fuska kawai muke yi da Hafsa ai, amma ina zan iya da halinta."
Maryam tana mikewa tace.
"Yarinyar nan zata kunyata ki a cikin mutane watarana, gwara ma ki gaya mata ba sunanki BabyDoll ba..." Ta dan yi shiru sai kuma tace.
"...Amma kuma ya iya zabar suna."
Dardumar dake gefenta Amina ta Webo ta cilla mata tana faWin.
"Ranki zai Saci wallahi...!"
Wayarta tayi kara a lokacin, Fatiman da take ta jira ce.
"Haba Fati, wai bokiti guda ake soya mana ne?"
Daga cikin wayar, a gaban ™awarta dake soyar waina Fatiman tace.
"Kin san mutanen da aka tsallake ake yi mana ne kike ta kwala min kira, to wallahi ko sun zo daukar ki ne sai sun tsaya mun ci wainar nan Allah."
"Wa ya gaya miki tun yanzu zan tafi? Ni kawai na ™agu ne, bakina sai tara yawu yake."
Fatiman tayi dariya tace.
"Ki cewa Wan Baban yayi hakuri, gani nan a hanya."
A lokaci guda kalaman Fatiman suka tafi cikin kan Amina dake zaune suka buga wani abu, wani abu da taji dirarsa har cikin ™irjinta, wani abu da yayi mata kama da tashin hankali a lokaci Waya, taji ma'anarsa na yin fadi a cikin zuciyarta tana so tafi karfin kalmar kokwanto.
Hannunta ya kai kan cikin ta a lokaci guda da kalmar Fatiman ta furta akan lebbenta, kwana biyu bata jin dadin jikinta sam, tana ta yin komai ne amma bata fahimta ba sai da ta fara jin tashin zuciya, haka kurum take ji kwana biyu bata son kamshin wasu abubuwa,ko a yanzu ma zogalen da Amma ke haWawa ne yasa ta kasa tashi taje wajenta, tun daga nan take jin cewa bata son ™amshinsa, sannan kuma yadda take ji kamar wani abu a cikin cikinta na rawa na jiran wainar fulawar da Fatiman ta tafi siyo musu, yafi karfin yadda take son wainar a kodayaushe.
Amma tsaya, haka da wuri komai yake faruwa? Kai tsaye kawai? Idan zata tuna lokacin da Aunty Ma'u ta sami cikinta na farko ba irin wahalar da ita da mijinta da kuma Amma basu sha ba.
Don ta kusa sati uku kwance a asibiti, kuma Amman ce mai kwana da ita a lokacin, to ta yaya ita yanzu tana zaune komai zai faru ba tare da ta ma sani ba? Sai kawai ta ture zancen Fatima a gefe ta mike ta fito daga falon lokacin da ta kula Amma ta rufe kwanon zogalen.
".... Suna gidanmu gabaWaya, zaki zo? Har da Barbie nake da."
Ta jiyo Hamida na lissafowa Hafsa kayan wasan ta yayin da take zare ido cike da Woki tana kallonta. Tana juyowa suka haWa ido da Inna dake kallonta tunda ta fito daga falon sai dai kafin tace komai Maryam ta fito daga Waki da hijabi tana fadin ta tafi.
"Ina zaki je?"
"KuSewa zata siyo anan bayan layi gidan su Aisha, ita kaWai ce ba'a samo ba a kayan naki."
Amma ta faWa tana jawo wata leda mai yalo da ba™i da aka cika taf da kullin bakaken leda.
"Ga Kuka anan, wannan kuma busashshen zogale ne ga yajin sannan ga dakakkiyar citta da tafarnuwa anan..."
Ta shiga lisaafin kowacce leda daga ciki yayin da Amina ke kallonsu, zuciyarta na bajewa da wani daWi da kuma ganin daraja ta girman Uwa, tabbas dole ne wanda ya rasa ta yayi kuka da idanunsa kullum a duniya, don ™arya ne ka sami mai kulawa da kai tun daga ™asan ruhi a duk duniyar sama da ita, sai dai kuma ubangiji kan Soye wasu tarin hikimomin nasa ga rayuwar wadanda ya karbi tasun, hukuncinsa daidai ne a kodayaushe.
Šazu kafin ta tafi gidan kitson a hira kawai take tambayar idan har yanzu gidan wata mata mai suna Salamatu akan layin nasu tana sayar da kuSewa, tace duk ýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹ŒŽ‘’“”•–—˜™š›œžŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿbata dasu sai gashi har Amman ta tanadar mata komai a yanzu. Da murmushin da godiyar ba zata misaltu ba tace.
"Madallah, Allah ya saka da alkhairi."
Amman ta amsa da Ameen sannan hannunta ya dauko kwanon zogalen nan ta mi™o mata, bata ko bude murfin ba, amma ™amshinsa ya tafi a tsaye har cikin hancinta, ba shiri ta juyar da kanta da sauri, sannan ta shiga girgiza kanta.
"Amma madallah, Fati zata kawo mana wainar fulawa yanzu."
Amman ta kalle ta na wasu sakanni kafin ta dauke kwanon tace.
"To ita zaki iya ci?"
Da murmushin ta ta kalle ta tace.
"Amma wainar fulawa ce fa."
"Wannan ma ai zogale ne kuma kina cin sa a da."
Fassarar da Amina ta yiwa kalaman Amma daban a cikin kanta, don haka a lokaci guda idanunta suka kaWa ta shiga sake girgiza kanta.
"Wallahi Amma ba wani abu nake nufi ba, kawai ji nayi bana son ™amshinsa, ya za'ayi in ™i ci haka kawai..."
Amman ta gyada kanta tana katse ta.
"Na sani ai, na san da lalurar shi yasa na tambayeki... Kin fada masa ma tukunna? Don ban ga alamun kun je asibiti ba?"
"Asibiti?..."
Amina ta tambaya kai tsaye tana kallon mahaifiyar tata, idan ka shigo a wannan lokacin ka kallesu, su biyu zaune akan tabarmar nan, zaka yarda an ™ir™iri wani mudubi ne dake zabge shekaru yana kuma ™ara du a lokaci guda, don kamarsu daya sak, yanayin sirantar jikinsu da idanun da hancin, dama yawan gashin kan mai laushi duk da na Amina ne kawai a buWe, banbancinsu kawai shine shekaru da kuma hasken fatar da Aminan tafi Amman a yanzu.
"... Lafiyata kalau fa Amma ba abinda ya same ni..."
Murmushin da Amman tayi shi ya katse ta daga sake magana, ta juya da kanta bata kalle ta ba sannan tace.
"Baki san kina da ciki ba?"
A lokaci guda tambayar ta janye Amina daga gangar jikinta, ta jita tana tashi zuwa wata sama mai nisa, tana barin gidan, tana batin unguwar, tana barin garin tana barin ™asar, tana barin nahiyar ma gabadaya... tana ganin kowa da kuma komai a cikin kanta kafin ta faWo a lokacin guda, ta taho tun daga wannan lulukin a tsaye, babu wani hijabi har inda take zaune, kuma ™arar dirar tata ya cika kunnwanta bakidaya!
***
A cikin motar dake tafiya, Ma'aruf ya kalli Faruk dake zaune a gefensa bayan ya ajiye wayar da suka yi da wani jami'in ´an sanda yace.
"Yana da wayo Faruk, ko waye Awwalun nan yana da wayo, tunda har daga wadannan mutanen har Mr. Okafor bai taba waya tare dasu ba."
Faruk ya girgiza kansa yana komawa da baya ya jingina sosai da kujerar da yake zaune kafin yace.
"Shi yasa na gaya maka zama zamu yi sosai kawai mu fara sabon bincike, gobe dole ka fito early, sai mu ga ta inda zamu fara."
Dawowarsu kenan daga Police headquarters na Bompai inda aka garkame duka mutane hudu ma'aikatan prison din dake da sa hannu akan fitar wannan mai laifin, inda har a yanzu daga mutumin har da mutanen kowannensu ya tsaya akan rantsuwar wani mutumi mai suna Awwalu kawai suka sani akan al'amarin, a yanzu haka an sami nambar da suka yi magana da shi Awwalun a lokacin, an mika ta hannun IT department, kuma zuwa gobe suke sa ran samun bayani daga wajensu idan har za's iya tracking wani waje da za'a iya samun Awwalun ko kuma wani bayanin da zai ksi su gare shi.
Ma'aruf ya dunkule hannunsa akan bakinsa kafin yace.
"Kana tunanin mu shigo da Yakubu wannan Sangaren shima?"
Faruk ya girgiza kansa.
"Yakubu ya iya aiki B, amma ka san yana da nasa matsalolin... Yana aikin ne tare da mutane da yawa kuma ban san me yasa ba amma haka kurum jikina yake bani cewa neman Awwalun nan yana bukatar sirri, sannan ya gaya maka cewa akwai aikin da yake yi yanzu haka shi yasa har zai cigaba da kula da wannan Mr. Okaforn, ka ga we have no time da zamu jira shi kenan.