← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 87

Sashe 14

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tambaya amon muryarsa na fitowa a hankali yayin da yake kallonta, gashinsa a barbaje kamar yadda yake tun jiya sannan idanunsa ke lumshewa alamun fada yake yi da kansa wajen bude idon. Tausayinsa da ta kwana dashi a cikin zuciyarta ya sake tasowa a ranta, taga idonta na  nuna mata cewa kamar ya rame daga jiya zuwa yau kaWai.

Tasa hannunta a hankali ta gyara dankwalinta da yayi baya da yawa, ta jawo shi ta rufe gashinta sannan tace.

"Baka da lafiya, jiya su Ishaq suka kawo ka."

Taji muryar tata ta fito kamar wani yana karta farce akan katako don haka ta shiga kokarin yin gyaran murya kadan sanda ya girgiza kansa a hankali.

"I don't want to be here." (Bana son zama anan.)

Ta daga kanta a lokaci guda.

"Tohm, bari nayi wa Nurses din magana su zo sai mu tafi gida."

Ta fadi haka da niyyar mikewa amma a lokaci guda ya kamo hannunta, taji yatsunsa da suka dauka dsuka da sanyin A.cn sun ratsa sun nad hannun nata, numfashinta ya dan katse a kirjinta kafin ta dawo ta tsugunna akan gwiwoyinta sanda idanunsa sun sake rufewa.

"Kar ki kira su."

Bata ce komai ba, yayi ™o™arin sake bude idonsa sannan yace.

"Ina wayata?"

Tambayar tasa a lokaci guda ta tuna abinda Faruk ya fada a jiya cewa an dauke duka wayoyin nasa har dasu wallet, don haka sai kawai tace bata san inda take ba, ya sake yin shiru yana kallonta, lumsassaun idanunsa suka tsaya akanta ba tare da yace komai ko kuma ya kifta su ba, zuciyarta ta shiga tsere a kirjinta, don duk da ta san rashin lafiya ce tasa idanunsa suka koma hakan, tana jin tasirin yanayinsu har kasan zuciyarta.

"Kin goge numbers Win nan?"

Ya sake tambaya a hankali, tayi shiru na wasu sakanni tana son ta tuno wadanne nambobi yake fada kafin ta tuna ranar da yace mata ta kwashe wasu nambobi daga wayar da ya bata zuwa ta hannunsa lokacin da suna hanyar dawowa daga jigawa.

"A'a suna nan a cikin wayar har yanzu."  Ta faWa a hankali, kamar idan ta Waga muryar tata tana tsoron zata fama masa wani ciwon ne.

Kuma saboda kokari sai da ya daga kansa sau biyu sannan yace.

"Akwai number Ishaq a ciki, ki kira shi kice masa yazo ya fitar dani daga nan."

Ta daga kanta sau daya sannan tayi kokarin  zare hannunta daga cikin nasa a hankali kafin ta mike yayin da ya maida idanunsa ya sake rufe du.

Akan kujerar dakin ta ajiye wayar tun bayan da alarm din Asuba ya tashe ta, don haka ta dauko ta ta shiga nenan nambar Ishaq din. Bugu daya biyu, uku aka dauka.

"Ma'aruf..."

Taji muryarsa ta kira sunan da manaki da kuma kuma kokwanto bayan saurin dske cikinta. Sai idonta ta koma kan Ma'aruf din da har yanzu idanunsa ke rufe sannan tace.

"Ba shi bane,  amma dai ya farka."

Jin muryar tata yasa taji kamar yayi ajiyar zuciya kafin ya sake tambaya.

"Kin tabbata ya farka?"

Ta daga kanta.

"Eh, shi yace in kira ka ma kazo ka maida shi gida, yace baya son zama anan."

"Kin kira Nurses din wajen?"

"A'a kai yace in fara kira tukunna."

Yayi shiru na wasu da™i™ai kafin yace.

"Bashi wayar."

Sai ta taso a hankali ™afafunta na taka laushin carpet Win wajen kafin ta isa ta tsugunna daidai gabansa, kuma kamar yaji ta ya sake buWe idanunsa wannan karin sosai a cikin nata.

"Zaiyi magana da kai." Bata san lokacin da fatar bakinta ta fadi hakan ba.

"Kin gaya masa abinda nace?"

Har yanzu sautin muryarsa a hankali yake fitowa, ta daga kai tana kasa janye idanunta daga cikin nasan, sai yace.

"Ki kashe wayar kawai."

Ta dan tsaya kaWan don ta tabbata Ishaq din daje cikin wayar yaji, amma ga mamakinta sai kawai taji shima yace.

"Rabu dashi gani nan zuwa."

Daga haka bai kara cewa komai ba kiran ya katse. Ta ajiye watar a gefe tana ganin yadda fatar idanun nasa ke sauka a hankali girmansu na kara raguwa, amma kuma duk da haka ita yake kallo.

"Zaka ci wani abun? Ko tea?" Ta tambaya tana ganin wautar ta, don a yanayinsa kowa ya kalle shi ya san bai gama dawowa haiyacinsa ba, kuma sai ya sake girgiza mata kansa sannan yace.

"Just stay Amina..."

Abinda ya fada kenan kafin idanun nasa su ™ara rufewa a lokaci guda, ta tsaya kusan sakanni biyar tana kallonsa kafin tajo tana son sake rike hannun nasa, don bata san me zata yi ba ma idan ta tashi.

Don haka haka ta mi™o shi ta riko nasa  a hankali, kuma ga mamakinta sai taji ya kara rike su shima, yana ratsa yatsunsa tsakanin nata sanyin dake jikinsu ya ratsa farar ta kamar dazu, sai kawai ta matso da kanta ta kwantar dashi a gefe gadon itama, tana kallon fuskarsa yayin da idanunta ke ™iftawa a hankali.

***

*Awanni biyu bayan hakan.*

"Mami ni na san Ma'aruf, wallahi idan ya farka ya sake ganinsa a wajen nan abinda zai biyo baya zai fi muni akan wanda ya faru jiya."

Ishaq ya fada lokacin da yake tsaye a kofar dakin, yayin da daga ciki wasu Nurses ne guda uku matsbiyu da namji daya ke kokarin dora Ma'aruf akan wani gado mai taya da za'a fita dashi.

Amina na tsaye daga gefensu ri™e da jakar ´an kayayyakin da aka kawo musu idonta yabi hannun Waya Nurse din da ta riko kansa da kallo, tana kallon yadda hannunta ya nutse cikin gashin kansa, wani abu ya motsa a cikin zuciyarta.

Sai kawai ta juya tana sauraren Ishaq Win dake cigaba da yiwa Mami bayanin da yasa dole ya nemi sallamar wa Ma'aruf, yana rokonta akan ta kira Baffa tayi masa bayani akan cewar ya bari a dawo da Ma'aruf gida don yanzu suka gama waya dashi yan fadan cewar don me ya biyewa Ma'aruf Win yace a sallame shi, saboda kawai yace baya son zama a asibitin.

Kuma bai sani bane amma ita kanta Mamin bata so hakan ba, da zata sami dama nata ™orafin zata yi itama. Don kamar yadda ta faWa mata a yau ne zata aiwatar da koma meye kudirinta, kuma abu na karshe da zata so shine ace Ma'aruf  baiyi nisan daga gare ta ba ta yadda ba zai iya kawo mata giftawar wata matsala ba komai kankantar ta.

Ta maida wayarta jaka lokacin da Nurses din nan suka shiga tura gadon da suka Wora Ma'aruf Win dake bacci har yanzu, don tun bayan wannan farkawar, bai kara bude idanunsa ba.

"Amina."

Muryar Ishaq da ya karaso cikin Wakin bayan fitar Nurses fin tasa ta dawo dq hankalinta kansa.

"Bai ce miki komai ba bayan sakon da kika bani lokacin da ya farka?"

Ta girgiza kanta a hankali.

"Cewa kawai yayi in gaya maka kazo ka fitar dashi, kuma bayan kiran ya katse ma bai sake cewa komai ba."

Ta gyada kansa yana maida wayarsa cikin aljihu.

Shiru ya ratsa na dakika biyu kawsi kagin ymuryarsa ta sake fitowa.

"Mun gode sosai da abinda kika yi Amina, this is the first time da wani ya taba zama da Ma'aruf a irin wannan yanayin bayan ni."

Bata san me zata ce ba, don haka ta gyada kanta a hankali tana kallon jakar hannunta da ta rike. Ya juya ya fita daga dakin har a lokacin bata dago ba, rayawa take a zuciyarta cewa idan har daga yanzu za'a fara yi mata godiya akan duk abinda zata yi, watakila za'a zo lokacin da za'a rasa wajen ajiye godiyar ma.

****

Hajiya kilishi ta tsirawa sakon da ya shigo wayarta ta nambar Awwalu ido, ta karanta ta sake karanta yadda yake gaya mata dukkan tsarindu ya tafi daidsi lokaci kawai yske jiracda kira ta kafin wani irin murmushi ya subuce a bakinta.

Me yasa take mantawa ne wai? Itace fa, itace wannan Kilishin da ba ta taba saka abu a gaba bata cimmasa ba, to don me kuma a yanzu take iya saka kokwanto a ranta? Me yasa take yiwa komai tunani biyu bayan gashi Aminar ma ta riga ta sami kanta.

_Saboda faruwar komai yana sauri da yawa..._

Wani gefen tunaninta ya ambata mata amma sai tayi cilli dashi gefen da ya fito a lokaci guda, ai yarinyar ta gama tsorata da ita ta sani, ta gaya mata cewar taSa dan'uwanta da tayi ba karamin abu bane da ba za ta so a sake irinsa ba, don haka ta riga ta gama yarda da ita, tunda har ta iya aikata wannan umarnin da ta bata a kudundune, umarnin da yaci sunan lauje cikin nadi, amma kuma tsaf cikin hikimarta ta ware nadin ta fidda laujen cikin sauki.

Don haka bata da sauran matsala ta sani, ko an dawo da Ma'aruf gidan umarni kawai zata bata na cewar kar ta sake ta bari ya fito, da wannan ta san zasu iya gama komai ita da Awwalu kafin jibi, tunda ko Baffa sai gobe zasu dawo suma.

Ta sake wani murmushin a hankali tana hango lissafinta. Tazarar fa kaWan ce, saura kaWan su ™arasa ga ™arshe inda komai zai fashe, taji tana taya Amina murnar shigowa cikinsu, don wahalar da zata yi kadan ce, ita da Awwalu sun daWe suna tsarawa da gina komai bi da bi.

Wayarta tayi kara a lokacin, Awwalu ne, ta dauka ta kara a kunnenta,

"Hajiya ki fito yanzu komai ya kammala."

Ta gyada kanta ba tare da ta amsa a fili ba.

Ta kashe wayar tana wani murmushi sannan ta jawo mayafinta, ita da dawowa gidan kuma sai lokacin da ta kammala kaso mafi yawa na cikar burinta.

Abinda bata sani ba shine, ubangiji ya kadarta tafiyarta a wannan lokacin ne don faruwar wani abu da tunaninta bai taba hango mata ba.

****

*Karfe biyar da rabi na wannan ranar.*

Karo na farko a rayuwar Ma'aruf da ya taSa bude idanunsa cikin irin wannan yanayin yaga ´anuwansa zagaye dashi fal, Awa kusan uku kenan tun bayan farkawarsa amma har yanzu zuciyarsa ta kasa ™arasa yarda da ganinsu gabadaya tare dashi kuma ba a ko'ina ba a cikin gidansa.
Chapter 14 · 0% Book details