← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 87

Sashe 47

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryar Samirah da ta fito daga kitchen ta fada a gabanta tana dawo da ita daga tunaninta. Ta juyo ta kalle ta.

"Sati Waya kenan fa dana ajiye kudin nan Samirah,yanzu har kin karar dasu?"

Da murmushi a fuskarta tace.

"Wallahi Mami, abubuwan ne wannan week din da yawa, kinga munyi abincin sadakar uku na jikar Mama Rabin nan data rasu, sannan ga wannan shirye-shiryen dawowar Ya Abdurrahim Win kuma, surprise party muke haWa masa tunda ya hana kowa zuwa can.."

"Amma ni duk ban san da wannan ba."

"Mami kwana biyu fa ba kya ko zama a gidan nan, kamar wani abu yana damunki shi yasa kawai muka ™yale ki..."

Da murmushi a fuskarta sanda ta faWi hakan, amma da ta san tasirin da kuma yadda suka shiga cikin kan Hajiya Kilishi da watakila bata yi wannan murmushin ba.

_.... Kamar wani abu yana damunki shi yasa muka kyale ki..._

Wannan wajen ya maimaita a cikin kan Hajiya Kilishi fiye da yadda zata iya ™irgawa a cikin sakannni kawai, ´arta ce wannan, ´ar da ta haifa a cikinta... Itace take gaya mata cewa sun ™yale ta saboda tana cikin damuwa, sun ™yale ta ba tare da sun damu su ji abinda ke damun nata ba a matsayinta na mahaifiyarsu.

™wakwalarta ta tariyo mata wani abu a lokacin, tabbas ba zata iya tuna rana guda da wani a cikin ´a´an nata ya taSa damuwa da damuwarta ba, Ma'aruf ne kawai... Ma'ruf ne kawai ke taSa nuna damuwarsa akanta idan har wani abu ya same ta, ko a yau ma s gajiye ya dawo yadsa ta fahimta daga muryarsa, smma ssi da ya kira ya gaishe ta ya gsya mata ya gaji ba zsi iya shigowa ba kafin ya shiga gidansa, amma  a vikin yan shekarun nan ba zata iya tuna rana guda da ta taSa ganin wata damuwa mai zurfi daga wajen ´a´an nata ba har kuwa waWanda ta yiwa aure yanzu, su kan dauki lokaci basu kira ta ba sau da yawa sai dai taji su suna waya dasu Samira.

Wani abu ya wuce daga makogwaronta yana son dasa mata wani abu da ba zsta taba yarda ba, don haka sai kawai ta gyada kanta sannan tace da Samiran dake tsaye tans kallonta.

"Bari na kawo miki, har da na cefanen wannan watan ma jiya Baffa ya aiko dashi kun fita."

"Yawwa Mami, Madallah."

Abinda tace kenan kawai sannan ta juya tana gayawa su Zahra abinda zasu yi. Sai itama ta juya tana jin kamar zuciyarta tayi nauyi da abinda ya faru, amma kuma
kwakwalarta ta cigaba da gaya mata cewa hakan ba komai bane, da zarar lokacin da zata kammala komai yazo, su da kansu zasu gane gatan da ta daWe tana yi musu, yaushe aka taSa halittar ´a´an da suka juyawa uwarsu baya a duniyar nan? Shaidan ne kawai ke kokarin cin galaba akanta.

Ta isa cikin dakinta lokacin da idonta ya kai kan wayar da ta bari akan gado, mitunan kiran na da suka yi da Hajiya Salamatu na nunawa akan fuskar wayar har yanzu, mamakin yadda akayi bata kashe ba kuma itama Salamatun bata lura ba ya kamata, sai kawai ta ™arasa ta Wauke ta, har zata kashe sai kuma taji wani abu kamar murya na magana don haka ta kara ta a kunnenta kuwa daidai lokacin da ta jiyo muryar Hajiya Salamatun daga can ciki tace.

_...a idon duniyar nan...!"_

Mamaki ya gifta a ranta na ma'anar hakan, amma sai wani gefen tunaninta ya bata cewar watakila hirarta ce kawai da wasu mutanen tunda gidan nata baya rabo da jama'a, don haka sai kawai ta kashe kiran ta ajiye wayar akan gadon sannan ta tafi daukowa Samirah kuWin.

Da ace dan adam yana da ikon dawo da lokaci baya zuwa sanda yake so, da tabbas Kilishi zata so dawo da wannan ranar kuma wannan lokacin fiye da sau dubu a rayuwarta.

***

*˜arfe tara na safiya.*

Amina ta kunna gas Win da ta Waura frying pan da mai a cikinsa, idanunta suka tsaya akan man har lokacin da ya fara zafi, yayi zafin yama fara shirin ™onewa kafin ta farga ta zuba haWin ™wan da ta haWa akai.

Minti talatin kenan, minti talatin tun bayan dawowarsu daga asibiti, don a Wazu da asuban nan bayan ta gaya masa abinda take tunani yace ta shirya su fita, ya kira Munaya yace tazo ta dauki Hamida zasu fita.

Tun gari bai gama haske ba ta shigo ta dauke ta zuwa cikin gidan tana bacci ma bata san me ake yi ba, kuma tana ta tambayar inda zasu je amma bai ce mata komai ba sai da suka tsaya a gaban wani Wan karamin Private asibiti da a samansa aka rubuta 24hours, (awa ashirin da hudu.).

A asibitin aka haWa ta da wata Nurse bayan ya yi musu bayani, kuma minti takatin bayan hakan aka tabbatar musu da abinda suka zo nema cewar da gaske tana da cikin.

Ta sani, tunda Amma ta gaya mata ta yarda kuma tana ji a jikinta ma, amma a wannan lokacin sai take ji kamar wani sabon labari ne, kamar an tabbatar mata da wani abu ne da a baya yake yawo a iska, kuma tun a cikin asibitin nan ta sani kwatanta irin murnar da ta gani a idanun Ma'aruf, wani abu ne da bata tunanin yana da geji, sai kuma tazo ta tankwaSe komai a lokaci guda da ta gaya masa cewa bata so zancen ya fita ko'ina tafi son ya barshi a tsakaninsu.

Bata so ayi wani na ukunsu da zai sani, ta gaya masa tana da dalilinta kuma zai san hakan a gaba, amma bai fahimce ta ba, tayi kokarin ™ara yi masa bayanin amma sai kawai yace ta kyale shi kuma a wannan lokacin da ta kalli idanun nasa ta san babu abinda ya fi dacewa illa ta kyale shin, don ta kasa tantance tsakanin farin ciki da kuma rashin fahimtar tata wanne yafi yawa a cikinsu.

Ta ™arasa soya ™wan gabaWaya, ta fito da dankalin da ta soya a deep fryer, ta hada komai waje guda tare da kayan shan tea, sannan ta koma ta kwaba fulawa da kwai da butter tayi wani pancake da yayi taushi sosai guda uku.

A hannunta ta Wauko woven tray Win da ta jera komai akai tana barin flask Win ruwan zafin a kitchen din, kafafunta suka fita daga kitche Win har zuwa hanyar koridon Wakunansu, wata doguwar riga ce a jikinta ta atamfa, dinkin jikinta mysi kyau ne don ko ranar da ta fsra saka ts su Samirah sun yaba dinkin sosai, ta daura dankwalin kawai a gaban goshinta, bayan Waurin ya tokare da tudun gashinta mai laushi da yake a tsefe ya fito ko tawanne gefe ana ganin sa.

Fuskarta fayau take, don duk da halin da take ji suna ciki akwai murna kuma a ™asan ranta fal, godiya ga mahallicinta kawai take mikawa a cikin ranta, tana jin cewa kamar babu wani abu a duniyar nan da zai iya daukar irin farin cikin dake cikin zuciyarta.

"Assalamu alaikum..."

Muryarta ta faWa bayan ta murda kofar dakin nasa, labulayen da iska ke motsawa ta fara gani a idanunta kafin shi, yana zaune daga ™arshen gadon Wakin kusa da bedside drawer dake kunne da fitila akanta, hasken fitilar da shi kaWai ne a cikin Wakin, kasancewar labulayen windunan sun hana hasken ranar da ya fara fitowa a waje shigowa ciki kuma sauran fitulun dakin duka a kashe suke.

Faffadar kafadarsa da kuma bayansa su ke kallo ta yayin da kamar kodayaushe hannunsa daya na ri™e da wayar dake kare a kunnensa.

Taji kamar ya amsa amma bata tabbatar ba don maganar da yake yi ma bata jin ta sosai, kafafunta suka taka a hankali zuwa ciki kuma maimakon ta samu waje ta ajiye tray din hannun nata sai kawai ta tafi gabansa ta tsugunna gabaWaya da kayan a hannunta, idanunsa suka kalle ta kuma kafin ta gama tantance idan fushi yake yi ko akasin haka, sai kawai ya kamo hannunta guda daya ya ri™e shi a cikin nasa.

"Zuwa 11 na fito Insha Allah, ina ga muna da two hours kafin lokacin da zanje Wauko Abdurrahim..."

Ya fada a cikin wayar da ta san ba da kowa yake yi ba Faruq ne. Idanunta suk cigaba da kallonsa yana sauraren bayanin Faruq Win, ba ma sai yace mata ba, tana iya karantar cewa ransa a Sace yake a cikin idanun nasa da kuma yadda jijiyoyin gefen wuyansa ke fitowa suna motsi su kaWai, gashin kansa ma wani býÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹ŒŽ‘’“”•–—˜™š›œžŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿayanin ne ™arara, gabadayansu a hargitse wasu sun dur™usa kamar zasu yi sujjada.

Sai kawai ta zame farantin daga hannunta ta ajiye shi a ™asa sannan ta mi™e zuwa gabansa ta zauna akan cinyarsa a hankali, da yatsan hannunta da bai ri™e ba tta shiga shafa gefen wuyansa a hankali kuma tana jin yadda makowagronsa ke tamkewa da taSawar da take yi, sai kawai ta karya wuyanta ta cusa fuskarsa ta gabaWaya a cikin nasa wuyan, tana jiyo muryar Faruq Win dake bayani tar daga cikin wayar.

"... Yaron bashi da hankali B, yana gaya min wai baya tunanin nambar ma wani ya taSa yi mata rijista? Akwai layin da yake amfani babu rijista ne?..."

Hannunta ya tafi daga wuyan nasa zuwa bayansa kuma a hankalin ta shiga zana masa harafan da ba lallai ta san ya fahimta a lokaci guda ba, don haka ta shiga yi tana ™ara sakewa... SORRY.

Har a lokacin kanta yana cikin wuyansa, tana jin yadda ko'ina a jikinsa ke amsawa da abinda take yi amna kuma bai ce komai ba, baiyi wani motsi ba ko kuma ya kalle ta tun bayan ri™e hannunta da yayi.

"Zan kira ka Faruk ina zuwa."

Taji ya faWa a cikin wayar muryarsa na fitowa wani iri, kuma tana jin wayar ta tsinke sai ta ™arasa da fuskarta daidai kunnensa tace.

"I'm sorry Sugar, dan Allah kayi hakuri."
Chapter 47 · 0% Book details