← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 87

Sashe 38

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kamar yadda ka sani Yallabai ni mai shara da goge goge ne a kamfaninka,to watannin baya da suka wuce, sai wani abokin aikina mai suna Sani ya same ni da labarin cewa ya samo mana hanyar da zamu yi kuWi mu daina wannan bautar, ya gaya min cewa akwai wani mutumi mai suna Isa, bayarbe ne amma kuma musulmi, yana harkar computer hacking da duk wani abu da ya shafi harkar technology na yanzu.

Rana Waya yazo yace min wai wasu mutane sun same shi da rokon cewa zasu bashi miliyan daya idan har ya shiga ofishinka ya samu wasu nambobi a cikin computerka, to shi bai san harkar komai na computer ba shine yazo ya same ni yace zai bani rabin kudin dubu dari biyar idan har na taya shi aikin, ya gaya min sau Waya cewar sunan mutumin da ya saka su aikin shi da Isa Awwalu amma bayan nan bai kara gaya min komai akansa ba.

Kuma sai a ranar da nake da aikin gyaran ofishin naka ne sannan muka yi waya da daya mutumin mai suna Isa, shi ya kwatanta min inda zan shiga a computer taka in kwafo wasu security numbers wanda sune na account din kamfanin, kuma na sami sa'a har naje na samo nambobin ba'a kama ni ba.

Kuma Sani ya gaya min cewa da wannan nambobin suka yi amfani akayi hacking account number kamfanin har aka turo muku da alert din ™arya alhali kuWin sun tafi ne zuwa wani account daban, kuma sunyi haka ne ta hanyar da ko banki baza su gane balle idan kun je ku sami wata gamsashshiyar amsa daga gare su.

Bayan mun gama aikin da sati Waya sai shi abokin aikin nawa ya kawo min kuWi dubu dari kawai yace min wai shima basu bashi yadda suka fada ba, amma idan sun bashin zai ciko min. Daga nan bai ™ara yi min mgna har tsawon lokaci kuma na tuntube shi amma yaki saurarata.

Ni kuma hakan sai nayi kokarin Waukan matakin da zan tsorata su su bani kudina, shi yasa naje na sami sbokin aikin ka Yallabai Faruk na gaya masa cewa ina da masaniyar abinda ya faru, nayi recording hirar mu a wayata sannan naje na sami abokin aikin nawa Sani da niyyar in nuna masa hakan.

Sai dai ina zuwa gidansa na tarar ya mutu har ana jana'izarsa. Sai na tsorata na dawo gida, bayan kwana biyu sai Isa ya kira ni da cewar inyi hankali watakila wadanda suka kashe Sani suna da alaka da wadanda suka samu aikin nan, a wannan ranar ne kai kuma kazo gidana Yallabai, sai dai bamu samu munyi magana ba ka dauki wannan yarinyar ka tafi.

A washegari kuma na tsinci labarin mutuwar Isa shima, shi yasa ba shiri na haWa iyalaina muka gudo nan garin ranka ta daWe, kuma nayi maka rantsuwa da kabarin babana tun daga wancan lokacin ban ™ara jin wani bayani daga kowa ba ranka ya daWe."

Mr. Okafor ya kai ™arshe a lokacin da Ma'aruf da kuma Yakubun suka cigaba da kallonsa, kallon da Ma'aruf ke yi masa daban ne, kallonsa yake yana kuma saurarensa da dukkan wani abu mai hankali dake jikinsa, kwakwalarsa na fahimtar kowacce kalma dake taruwa tana fitar da jimla guda a bayanin nasa, kuma bayan ya kai ™arshe, abu na farko da ya fara yi shine jawo wayarsa. Hannayensa suka lalubo nambar Martha a lokaci guda.

"Ki duba min a kananun ma'aikatan dake aiki akwai wani Sani da ya mutu kwanakin baya?"

"Okay sir." Ta amsa da sauri fahimtar cewa shima saurin yake yi a cikin muryarsa, kuma daga inda yake zaune yana jin karar keyboard din computer ta da take dannawa, cikin abinda bai fi rabin minti ba tace.

"Akwai yallabai, sunansa Sani Madugu, wani danuwansa ne yayi reporting mutuwarsa wata hudu da suka wuce, kuma har an bawa iyalinsa garatutinsa wancan watan."

"Thank you."

Kawai ya faWa sannan ya ajiye wayar, idonsa ya sake dawowa kan Yakubu da kuma Mr. Okaforn dake jiran abinda zai ce ta cikin computer, zai so kwarai yace a sake shi ya tafi ga iyalansa amma ba zai iya ba, bayani kawai suka samu daga wajensa babu wata shaida ko kuma kwakwaran bayanin da zai kaisu ga wani abu har yanzu, don haka sakinsa zai zama tamkar saki na dafe ne wanda ba zai fara hakan ba.

Saboda haka yayi ajiyar zuciya mai nauyi kamar ta cikinta ne zai fitar da tarin abubuwan da yake jin nauyinsu a cikin kansa sannan yace.

"A cigaba da rike shi Yakubu, amma kar ku sake taba shi..."

"Sir pleeeease, pleeese sirrrr, abeg naaaa, help me sirrrr pleaseeeeee....."

Magiyar Mr. Okaforn ta sake cika oficce din a lokaci guda kafin Yakubu ya daga murya ya kira mutanen nan, kuma suka shigo a lokaci guda suka Wauke shi suka sake fita dashi yana ta magiyar yana rokon  Ma'aruf.

"Kar ka damu, duka iyalan nasa ma suna nan tare damu, zan cigaba da rike su har lokacin da kace, 'Cox ina da wani aiki da zsn yi anan garin ma."

Ma'aruf ya gyaWa kansa.

"Nagode sosai Yakubu it's a pleasure to work with you.  Zan sake turo maka da wasu kudin insha Allah to keep things going."

Yakubu ya gyada kansa shima sau biyu a jere sannan kiran ya katse. Ya katse a lokaci guda da sa™on Amina ya shigo wayar Ma'aruf dake gefe, ya dauko ta ya duba, abinda ta rubuta dan guntu ne.

"Sugar, zanje kitso dan Allah..."

Yana gama karantawa wani sa™on nata ya kara shigowa akai.

"Ba nisa..."

"Kusa da gidansu Fatima ne..."

Gidansu Fatima, wannan kawar tata da yake yawan ji tana faWa, dazu tare suka fito ya sauke ta s gidansu tare da Hamida kafin ya tajo office, shima ya shiga ciki sun gaisa da kowa, don saura kwana biyu kawai tafiyar mahaifinta da kuma kaninta Aminu zuwa India, har da kansa ya yiwa Mami godiya da yaji labarin cewa ita ta Wauki nauyin tafiyar, ´anuwanta ne ya sani amma haka kurum sai yaji kamar saboda shi tayi hakan, shi yasa shima a yanzu da yaje yayi musu irin tata kyautatawar wanda da kyar suka karSa, abinda basu sani ba shine, zuciyarsa na gaya masa cewa zaiyi tarin abinda yafi haka ma indai akan Amina ne.

Saboda haka kafin wani sa™on ya sake shigowa ya shiga typing amsar sa da take jira.

"Ki tabbatar an rubuta sunana a jikin kitson nan Doll."

Sakon ya tafi a lokaci guda tare da shigowar kiran Faruk, don haka ya fasa cigaba da rubuta abinda yayi niyya ya Wauka.

Muryar Faruk Win ta fito a lokaci guda da ya kara wayar a kunnensa.

"Muna High Prison, mun sami mutumin nan B, yana ganinsa ya gane shi, yanzu haka ma ya fadi duk wadanda suka saka shi ya fita daga Prison din suma an tafi za'a fito dasu don dukkaninsu ma'aikatan wajen ne."

"Alhmdlilah, Alhmdlilah, Alhmdlilah...."

Itace kalmar dake fitowa daga bakin Ma'aruf tunda yaji abinda Faruk Win ya faWa na farko. Ya mi™e tsaye a lokaci guda ya fito daga kujerarsa ya dawo tsakiyar office din hannunsa a cikin gashin kansa yayin da zuciyarsa ta kasa tsaida kanta waje guda a tsakanin murnar wannan nasarar da kuma taraddadin abinda yake shirin tambaya.

"Ya gaya maka wani abu Faruk? Any clue na su waye mutanen da suka sa shi aikin kafin yaje ya karbi kudin?"

Ya tambaya muryarsa a tsaye kyam!

A can bangaren,Faruk ya girgiza kansa yana kallon hayaniyar dake faruwa a gabansa wadda ma'aikatan Prison Win suka tayar na Cewar baza'a tafi da ogansu ba kasancewar har da sa hannunsa al'amarin,tarin ´an sandan da suka zo dasu na ta ™o™ari wajen hana su haurowa inda su suke tsaye ana shirin fito da mutumin, sai ya girgiza kansa a hankali sannan yace.

"Ko waye Awwalu ya shiga uku Ma'aruf, don gayen yace min mutum daya ya gani da ya saka shi aikin, shi ya bashi wallet dinka da wayoyinka ya kuma fada masa duk abinda zaiyi, kuma yace sunansa Awwwalu."

"Awwalu." Ma'aruf ya furta ba tare da ya san ya fada ba.

"Awwalu." Ya sake faWa a hankali.

****

"Awwalu."

Hajiya Kilishi ta faWa tana kallon Aminiyarta Hajiya Salamatu.

"Ni Awwalu zai yaudara ya mayar mara hankali Salamatu? Wai har ni Awwalu yake kokarin cin amana a harkar nan?"

Ta sake faWa amon muryarta na fitowa cike da takaici. Suna zaune a cikin falon gidan Hajiya Salamatun ne,inda bayan su kaya ne fal na sabbabin atamfofi da kuma lesuna tsibiri-tsibiri an zube su kamar banza kasancewar dawowar Hajiya Salamatun kenan daga ™asar da take yo siyayyar kaduwancinta.

Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.

"Wannan ai ba komai bane Kilishi, ki duba fa ki ga yadda kike cin amanar wadannan mutanen dake tare dake, to har dan abokin aikin ki wanda kullum yake ganin abinda kike yi ya kwaikwayi hakan sai kiji wani zafi? Kamata yayi ace daman kin dayde da shirya masa.

Kilishi dake kallonta tace.

"Maganganunki sunyi zafi Salamatu, amma haka ne, tabbas abinda kika faWa haka yake, wannan ba komai bane don Awwalu ya nemi ya bauWe, daWin shine na daWe ina shirya masa dama, kuma a tunaninsa ya koyi irin taku na yana shirya hanyarsa bai san cewa sawun giwa ya take na rakumi ba kuma ko a gidan giya akwai babba, sannan sama tayi wa yaro nisa sai dai ya Waga kai yayi kallo."

"Wannan haka yake, nice ta farko da zan fara yi miki wannan yabon bayan ke Kilishi, yanzu ki gaya min a ina kuka tsaya tare dashi."

Kilishi ta kurbi lemon hannunta tana kallon Salamatu ta cikin gikashin kofin, kuma bata ajiye ba sai da ta shanye shi tas sannan tace.
Chapter 38 · 0% Book details