Sashe 23
Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da dan guntun murmushi a lebbanta ta cigaba da kallonsa, ya gyaWa mata kai yayin da Hamida ta juyo tana kallonsu. Wani abu yake ji a lokacin kamar wuta ya harba daga tsakiyar bayansa zuwa kafafunsa, yaji yana so ya rungume ta kamar yadda yayi wa Hamidan, kuma kai tsaye zai iya yin hakan amma bai san yaya zata karbi hakan ba a yanzu.
Ta juya ta koma can wajen wardrobe din rike da rigar nan a hannunta sanda Hamida ke cewa.
"Daddy, wannan Auntyn tace ta bar min kai ba zamu yi sharing ba, kawai zata dinga dafa mana abinci."
"Haba dai?" Ya tambaya da sauri da kuma alamun mamaki, sai kuma yace.
"Wasa take miki, kice wasa kike mata dan Allah Doll.
Yadda muryarsa ta fito, yadda amonsa ya furta wannan sunan da kuma taushin muryar tasa ya taba har fatar kunnenta ba ma can ciki ba, ta juyo ta kalle shi tana dariya kuma kafin shi da ita su sake cewa komai, Hamida tace.
"Sunanta Doll?"
Ya gyada kansa yana cigaba da kallon ta.
"Eh mana amma ba wanda kika sani ba, wannan special one ne."
Sai ta gyada kanta itama alamun ta gane kuma daga wannan ta shiga tambayarsa yaushe zai sake maida ita wannan creche din da ya Wauko ta, tana gaya masa cewa su je kitchen taga irin bowl Win da ake zuba mata abinci a creche din, kuma da haka ta ja shi suka bar dakin tana ji taba gaya masa cewa wai jini ne a cikin bowl din har ya bata mata kaya.
Sai ta hadiye wani abu da bata san sunansa ba a ma™ogwaronta, har yanzu ta kasa samun Amma a waya, Allah-Allah kawai take anjima tayi ta kira Baba idan ya koma gida, don duk da ta ™ona wannan layar dazu a bayan fulawoyin gidan har yanzu hankalinta bai kwanta ba, har yanzu zuciyarta bata nutsu ba.
Ta zazzage dukkan kayan Hamidan yafi sau biyar tana sakewa, tun tana tambayarta me take nema har ta gaji ta tsaya tana kallonta kawai, sai da ta gaji ta tabbatar babu wani abu da ta sake gani sannan ta zauna suka shiga ninke su suna saka su a kasan drawer.
A yanzu ta riga ta sami amsar da kowa bai sani ba, ta gane dalilin da yasa suka kawo yarinyar haka kwatsam bayan faruwar komai, akwai wani abu da suke son cimma ne wanda bata san takamaimai asirin akan waye ba, amma duk da haka bata jin cewa ya dace ta sanar da Ma'aruf tun a yanzu, shi yasa take son samun Amma a waya ta shaida mata komai don ta san yadda zata Sullo musu suma, don ta yarda idan har zasu yi yunkurin cin galaba akan Kilishi to wannan ma ba komai bane, kawai tsoronta shine kar ya zamo da wani abin da bata sanshi ba ko kuma bata yi daidai ba wajen ™ona layar nan.
Lokacin da ta gama ta koma falon, Hamida na zaune ita kadai tana kallo, don haka ta fahimci Ma'aruf yana dakinsa kenan, sai kawai ta koma kitchen ta debo dukkan kayan abincin data hada ta fito dasu falon, Hamida tace ba zata ci tuwon nan ba, don haka tayi mata wata ´ar jollof din taliya da kifi. Kuma tana miko mata ta karba ta fara ci,ta fahimci yarinyar tana son abinci kawai dai bata iya ci da sauri bane.
Sai dai tana fara ci din tace a cire mata ™ayar kifin, don haka ta bar sake kokarin kiran su Amman da take yi tazo ta zauna daga gefenta a kujera tana kokarin cire mata ™ayar tsakiya na kifin da fork din da take ci. Kuma a lokacin ne Ma'aruf ya fito, ya canja zuwa wata gogaggiyar jalallabiya kalar milk data fito da Wan hasken fatarsa kadan, yayi fresh din da ba sai yayi bayanin daga wanka yake ba, amma duk da haka Hamida ta tambaya.
"Kayi wankan?"
"Yes, nayi wanka."
Ya amsa yaba tahowa idonsa akan kafafunta da ta rasa me yake gani a jikinsu yake kallo, jallon da yasa zuciyarta tayi fayau a kirjinta.
Ya ™araso a hankali ya tsugunna a daidai gabanta hannunsa ri™e da wani abu da bata gani sosai ba, kuma tun kafin yace wani abu Hamida ta sake fadin.
"Daddy naku tuwo ne kai da Auntyn, ni bana ci shi yasa nake cin wannan."
"For real?"
Ya dawo da ganinsa kan Aminan, don shi har ga Allah ya manta da zancen tuwon da yayi.
"Da gaske na samu tuwon nan?"
Tana murmushin yadda yake tambayar ta gyada masa kai, sai ya zura hannunsa daya a cikin gashinsa yana kallonta ba tare da yace komai ba.
Sai kawai tayi murmushi ta mike zuwa wajen da ta ajiye food flasks din tana gaya masa cewa har da na dumame ma duk zai samu, yayin da Hamidan ta shiga tambayar meye Wumamen.
"Eeeewwwww!" Ta fada da karfi bayan Ma'aruf yayi mata bayanin.
Suka yi dariya dukkansu kafin Ma'aruf ya taso zuwa wajen da take zuba masa abincin, kamshin miyar ya ratsa hancinsa yana yaba girkin tun kafin ya kai bakinsa don ko daga yadda miyar bata yi mai sosai ba ma hakan ya burge shi, kamar ta san yadda yake son komai.
Ya tankwashe ™afafunsa a gabanta yana kallonta yana kallon yadda take zuba miyar, yadda take komai... Allah ya sani baya jin gar ya bar duniya zai taba manta wannan alkhairin na Mami na kawo masa Amina cikin rayuwarsa.
Wannan wani alkhairi ne da yake tunanin har a kabarinsa zai tuna shi.
****
"˜arfe tara da rabi.*
Hamida tayi bacci a lokacin, kuma har a sannan Amina bata sami damar samun su Amma ba don wayar Baban shima bata shiga yanzu.
Ma'aruf ya shiga cikin gida wajen Baffa, kusan awa guda kenan, tun daga masallacin isha'i yace mata zai wuce. Ya gama cin abincin yayi santi kala-kala da tun tana daurewa har ta dinga dariyarta a fili, kuma bayan hakan ya gode mata lokacin da ta kwashe kayan zuwa kitchen.
A cikin kunnenta ya dinga raWa wasu abubuwa da ita kanta idan ta tuna yanzu sai ta runtse idonta don kunya, Ba wai maza ta sani sosai ba amma ta yarda Ma'aruf daban ne, shi da kansa yau ya gaya mata cewar baya ji, kuma itama ta yarda da hakan.
Babu wanda zai yarda zai aikata dukkan abubuwan da yake yi, idan ka ganshi a fuska very responsible and so stiff akan dukkan abinda ya yanke, amma yafi kowa sanin tarin hanyoyin da zai ruWa mace a lokaci guda.
Kamar kullum wajen da ya ri™e ta har yanzu tana jin kamar shatin yatsunsa a wajen, kamar lokacin da ya ri™e ta yatsunsa sun ™ona wajen ne sai a yanzu iska ke kaWawa tana son dawo da fatar tata daidai.
Ta ajiye abin sallar da ta idar da isha'i a lokacin, gyaran kitchen din da tayi ta kuma tsaya yiwa Hamida Brush da canja mata kaya tana gyangyadi shi ya cinye lokacinta sai yanzu ta samu na sallar.
Ta tafi zuwa gaban mudubi ta dauko wani kwando tana kwashe dukkan abinda ta san Hamida zata iya sawa a ido ko ta bata jikinta dashi, tana yi tana yabawa kanta yadda tayi kokari wajen kula da yarinyar da kuma sawa ta sake a gidan ysu daya kawai, Surayya na cewa sati guda, idan ta shigo gobe zata sha mamaki.
A lokacin ne kuma kofar dakin ta bude, ta dago da idonta ta cikin mudubin tana kallon Ma'aruf din da ya shigo, fuskarta ta haska da murmushi tana masa sannu da zuwa.
Ya karaso a hankali yana zuwa inda take, kuma ba tare da ya jira komai ba ya rungumeta ta baya, kansa ya sauka a gefe wuyanta sannan ya karkato da kansa gefe yayi kissing kumatun ta kafin yace.
"Har guda nawa zan dinga samun wannan sannu da zuwan ne?"
Tayi kokarin tsaida numfashinta a hankali.
"Duk lokacin da ka fita ka dawo, kana da guda daya?"
Sai ya gyada kansa sannan ya ™ara karkata shi zuwa cikin wuyan nata, ba shiri ta damke kwandon nan dake gaban mudubin, tana jin kamar wannan karon kusan tayi yawa.
"Yaya jikin naka?"
Ta tambaya a hankali don ji take yi kamar har yanzu da Wumi a jikin nasa. Yayi shiru jamar ba zai amsa ba tsawon wucewar sakanni sannan yace.
"I'm sorry Doll."
Mamaki ya dan kamata.
"Na me?" Ta tambaya.
Sai kawai ya mike tsaye sosai ya juyo da ita tana fuskantarsa, sannan yace.
"Sorry da nake saki damuwa akaina."
Ya sunkuyo a hankali ya sake kissing daya gefen fuskar tata sanan ya sake cewa.
"Sorry da zuwan Hamida."
Ya sake kissing gefen bakinta.
"Sorry da dukkan flaws din da kika zo kika tarar a rayuwata."
Wannan karon saman bakinta ya sake kissing sannan ya Wan matsar da fuskarsa baya kaWan yana kallon idanunta yace a hankali.
"Sorry da na bata miki dukkan rayuwar da kike tunanin zaki samu idan kinyi aure..."
Kafin ya ™arasa, kafin ya sake cewa wani abu tasa hannunta da sauri ta rufe bakinsa sannan ta girgiza kanta.
"You don't have to be... Babu abinda na taba tsarawa a rayuwata a wannan stage din, babu wani hasashe da na taba yi, so dukkan abinda ke faruwa a yanzu shine duniyata kuma shine fantasy dina."
Ya rike hannunta da ta rufe bakin nasa dashi, yayi kissing cikin tafin hannun nata kafin ya janye shi a hankali.
"Ban gane ba Amina, ki kara yi min bayani sosai."
Sunanta da ya fito daga bakinsa da kuma yadda sautin muryarsa yake yasa jikinta yin rawa kadan, ta hadiye wani abu a makogwaronta har yanzu tana kallonsa sannan bakin ta ya furta.
"Ma'aruf Mansour Bakori, kai ne duniyata kuma kaine duk wani fantasy dina a yanzu, I really love you so much and I mean it."
Kuma da haka bata jira komai ba ta kara tsawon kafafunta tayi kissing gefen bakinsa kamar yadda yayi mata dazu,da farko bai ko yi motsi ba, yana tsaye ne kawai kamar baya numfashin amma tana kokarin maida kafafunta ta koma taji ya furta kalma guda biyu rak!
"Ya salam!"
Kuma da haka bai jira komai ba yasa duka hannunsa biyu ya jawo ta jikinsa.