← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 87

Sashe 60

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya jikin nata? Hajiya tace har yanzu bata farka ba."

Hannunsa daya ya mi™a cikin barbajajjen gashin kansa sannan ya rufe idanunsa gabaWaya yana jingina da kujerar motar.

"Bata farka ba, amma soon insha Allah."

Amina ta gyada kanta, tana zaune ne akan kujerar falon gidan tare da Hamida tmda tayi bacci akan cinyarta, basu dade sosai da dawowa daga cikin gida ba, don kamar kowa suma kusan a zaune suka kwana ana jimamin abinda ya farun, a yanzu ma ta dawo ne ta yiwa Hamidan wanka ta kuma bata abinci, wanda bayan ta gama ne bacci ya dauke ta.

"Kana tare da ita ne?

Ta sake tambaya a hankali. Ya girgiza kansa a hankalin shima.

"Na fito,ina mota yanzu."

"Dan Allah ka dawo gida kafin ka tafi wani waje... Baka ci komai ba fa.." ta fada ksmar zata yi kuka.

Yayi shiru kaWan kafin yace.

"Kina ganin zan iya cin wani abu yanzu?"

Ta gyaWa kanta a hankali.

"Zaka iya Sugar, saboda babu abinda zai faru insha Allah, komai zai tafi daidai kawai jiran sakamakon ne mai wuya..."

Ya gyaWa kansa a hankali.

"Na sani Noor, da wuya sosai... Mami kamar mahaifiyata ce, ina jin ta har cikin raina wallahi hankalina ba zai taSa kwanciya ba ace wasu sun saka ta a cikin wannan halin, babu abinda ya same ta amma har yanzu bata farka ba Amina, bamu san meye matsalar ba har yanzu, amma kuma duk da haka ace gaan saka ´an sanda suna gadinta sun hana kowa shiga..."

˜wallar da ta cika idanun Amina ta gangaro zuwa kumatun ta, Allah ya sani tsoro take ji, tsoro take ji sosai na ranar da Ma'aruf zai san wacece Kilishi, don bata san yadda za'ayi zuciyarsa ta iya daukar masa hakan ba, bata sani ba ma idan har zai iya daukan...

Sai ta share su da bayan hannunta Waya sannan tace.

"Babu abinda zai faru Insha Allah Sugar, alkhairi kaWai Allah zai azurta rayuwarmu dashi insha Allah."

"Insha Allah." Ya faWa a hankali yana buWe idanunsa sannan yace.

"Zan aiko direba ya karSa min abincin, ba zan iya dawowa gida yanzu ba Babydoll, ayyukan dake jira na a office suna da yawa, yanzu ma na ga missed call din Faruk kusan biyar ban dauka ba."

Ta cije lebbenta kaWan na ba hakan ta so ba, amma tasirin uzirin da ta san dole ne tayi masa ya danne son ran nata don haka tace.

"Shikenan Allah ya kaimu yazo Win..."

"Kar ki sake yin komai, ki bar min Wumamen tuwon nan kawai."

Tayi murmushi jin daWin cewa har yanzu bai manta da tuwon ba sannan ta gyada kanta a hankali.

"Insha Allah Habibi albi."

Ma'aruf ya sake lumshe idanunwansa yana jin tasirin muryarta da kuma sabon sunan a jikinsa. Yayi shiru kawai ba tare da yace komai ba, itama tayi shiru bata sake cewa komai din ba, kuma a cikin shirun yake yake jin kamar dukkan gajiya da kuma damuwarsa suna bin iska ne, sai dai hakan baiyi nisa ba sakamakon shigowar kiran Faruq da ya sake shigowa, ya Wago da wayar ya kalla kafin ya sake maida ita kunnen nasa.

"Babydoll ki min hakuri please, zan Wauki kiran Faruq."

"Ba komai, kaje kayi aikin ka kawai, amma dan Allah ka turo direban da wuri."

"Insha Allah thank you so much for ur care." ( Nagode sosai da kulawarki.)

"Aiki na ne Sugar."

Ta faWi abinda ya saka shi murmushi ba shiri, murmushin da yake Wan mitsitsi amma ya taSo har cikin zuciyarsa.

Kiran Faruq Win ya Wauka ya kara a kunnensa.

"Faruq..." Ya furta muryarsa na fitowa yadda take.

"Ma'aruf kana ina?"

"Ina asibiti. Har yanzu bata farka ba."

Ya faWa yana kallon rubutun 'Amenity 4' Win dake can gabansa kamar yana son ya tabbatarwa kansa da hakan.

"Kazo office yanzun nan Ma'aruf, ga Brothernka anan yana buWe mana aiki..."

Ba shiri ya mi™e zaune sosai yana buWe idanunsa.

"Wane brothern? Waye? Me ake yi?"

Ya jero tambayoyin a lokaci guda harshensa da ma muryarsa na ™o™arin karyewa wajen tambaya.

Daga cikin wayar, Faruk yayi murmushi mai sautin da ya ji shi kafin yace.

"Brothernka da ya dawo jiya Abdurrahim, yaron nan wuta ne B, kazo ka ga aikin da yake yi, gabadaya forensic department din da muke dasu baza su iya ba B... Walkahi kowaye a bayan aikin nan, al™iyamarsa ta tsaya!"

Faruk ya faWi hakan a lokaci guda da  kwakwalar sa ta tuna masa abinda Baffa ya gaya masa da safoyar yau.

_"Abdurrahim ya fita yace zai fara zuwa kamfani, inaga daga nan zai zo ya ganta shima idan zasu bari ya shiga...!"_

***

A ™ofar wani ™aton Gidan ™asa Jawad ke tsaye a jikin motarsa, idanunsa na kan ™ifar gidan ne wanda tarin mutane ke ta fitowa ta cikinta kamar gidan tururuwa.

Har yanzu lissafi kwakwalar sa kawai take yi na yadda abubuwa ke faruwa dashi bi-da bi, yadda duniyarsa ke tsukewa tana waje guda tarin abubuwan na bayyana gare shi, Waya bayan Waya kuma kowanne baya yin nisa da guda.

Kusan minti talatin kenan a dazu da Zainab ta gaya masa cewa garinsu ya kawota, garinsu,inda gidansu yake kuma inda mahaifiyarta take. Mamakin hakan ya harba cikinnkwakwalwarsa da tasirin wani abu da bai san shi ba, tsayawa kawai yayi yana kallonta yayin da hannunsa ke kan sitiyarin motar yana kokarin juyawa, bayan sun rabu da Nura ne, wannan saurayin da yayi masa rakiya har gidan da ya samo lambar da bai tabbatar idan zata amfane shi ba.

A lokacin har sun sauke Nuran ya juya kan motar suna shirin barin garin, kanta yana ™asa tana wasa da yatsunta, sai kawai ji yayi tace.

"Dan Allah zaka kaini gida kafin mu tafi?"

Muryarta ta fito ne tana rawa, tana rawa sosai ta yadda da ™yar ya gane me take cewa, ku.a ba shiri a lokaci guda ya tsayar da motar, Allah yaso ba gudu yake  har a lokacin ba, ya juyo ya kalle ta har a lokacin kanta yana ™asa,

"Me kika ce?"

Ya tambaya da sauri yana kallonta.

"Gidanmu, a can hanyar yake babu nisa, dan Allah ina so in ga Naani."

Ta sake faWa wannan karon hannayenta na rawa fiye da Wazu. Kuma kalmar Naanin ta haska a kansa da wata ma'ana da ya taba sanin cewa ya rike a cikin kansa cewar haka take gayawa mahaifiyarta. Don haka ba shiri yace.

"Gidanku? Anan garin kike dama?"

Ta daga kanta.

"Nan ne garinmu, da muka zo nayi zaton gida Hajiya tace ka kawo ni, sai kuma naga ba haka bane... Wanda ya nuna maka gidan da kuka je sunansa Nura, shima na san shi, a gidan da mamana take aure yake."

Ba shiri hannunsa ya kai saman kansa yayin da bakinsa yake a buWe, kuma a lokaci guda ya tuno da ranar da ya fara tambayarta sunanta da kuma inda take...

_"Sunan garinmu Yakura, a kusa da Kaduna yake."_

Haka ta fada muryarta tana rawa, sai kawai ya gyada kansa yace.

"Zainab kin san shi? Amma ya akayi baki yi magana ba shima kuma baice komai ba?"

Ta kai hannu ta share kwallar da ta cika idonta a lokacin, sannan ta girgiza kai har a  lokacin bata kallonsa.

"Bai gane ni ba, bai sanni sosai ba, lokacin da na tafi ma baya garin ance ya tafi ci rani."

Sai kawai ya haWiye wani abu da bai san sunansa ba a makogwaronsa yana kallonta, yana kallon yadda take sunkuye da kan ta da kuma yadda take share hawayen fuskarta, bai san kukanta na meye ba amma ya fahimci tsoro take ji, tsoron tambayarsa take yi don taje ta ga mahaifiyarta, shi Win da ba kowa bane har yanzu a rayuwarta, wani abu da yake ji kamar ya fi tausayi girma shi ke gilmawa a zuciyarsa a lokacin haWe kuma da mamakin yadda abubuwa ke kasancewa bi da bi a rayuwarsa.

Ya murWe kan sitiyarin motar suka juya, kuma yana tambayarta da kwatance har zuwa ™ofar gidan da a yanzu yaje tsaye yana jiran fitowarta, yana jiran yayin da kwakwalwarsa ke cike da lissafi da kuma tarin tunanin abubuwan da bai san adadinsu ba.

A karo na ba adadi hannunsa ya sake danna wannan lambar da aka bashi, kuma ta shiga har zuwa bugu na ™arshe kafin ta katse kamar kodayaushe, tunda ya tsaya a wajen yake kira, zai iya ™irgawa kiran ya tafi kusan sau goma daga lokacin da ya fara zuwa yanzu, sai kawai hannunsa ya shiga bangaren sako ya rubuta abinda ya san ko waye zai karanta ba zai dauki neman da yake yi masa da wasa ba.

Kuma sai da ya tura sannan tunanin ko bai kwafi lambar daidai ba ya haska a ransa, sai kawai yasa hannu a aljihunsa ya zaro wannan takardar, ya kalli lambar jiki da kuma wadda yake kira yaga daidai ne sai kawai ya du™un™une ta yayi wulli da ita gefe, yayi wulli da ita daidai lokacin da ™afafun wani dattijo suka fito daga cikin gidan.

Sanye yake da riga da babba ´ar ciki wadanda suke daban-daban, fuskarsa a murtuke take babu alamun fara'a ko kaWan, kuma da kallo Waya da yayi masa ya fahimci wanene shi, Mijin mahaifiyarta, mijin mahaifiyarta wanda tace shine sanadin tahowarta aiki, naganganu da kuma hoton wannan ranar da ya fara tambayarta sunanta ya sake dawowa cikin kansa.

_"Waye ya kawo ki nan?"_

_"Abokin babana ne."_

_"Ina baban naki?"_

_A hankali tace._

_"Ya rasu."_

_"Ina babarki?"_

_Sai da ya lura ta hadiye wani abu sannan tace._

_"Tana nan, matarsa ce ita yanzu."_

_Kalaman suka daki kirjinsa da wani abu da bai san meye ba, amma dai ya san nazarinta yake yi, nazarin shekarunta da ya kasa ™iyasinsu._

_"Ita me yasa bata hana shi kawo ki ba?"_

_Sai ta sake dagowa ta kalle shi, idanunta na nuna wani abu da ya kasa tantancewa, idan ma tunani take cewa muryarsa ta fito da damuwa ne, zai goge mata hakan yanzun nan._

_"Bashi da kirki, Naani baza ta iya hana shi ba."_
Chapter 60 · 0% Book details