← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 87

Sashe 44

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Awwalu ya kai ™arshen dogon bayanin yana kallon fuskar Hajiya Salamatun da ko sau daya bata yi kokarin katse shi ba, kallonsa kawai take ui da idanunta da har yanzu basu canja ba, basu canja daga yanayin da suke tun a lokacin da ya fara magana ba har zuwa yanzu, kallonsa take yi kamar kalma guda kawai ya furta tana jiran ya fara bayanin ne.

Amma a cikin kanta hotuna ne kawai suke wucewa, hotuna masu tarin yawa, tun daga wadannan shekarun da Awwalun ya dauko, lokacin da ta haihun aka shaida mata cewar ta rasa danta, lokacin da ta rike gawar yaron a hannunta, lokacin da take jin wani daci na sauka daga makogwaronta yana mamaye dukkanin jikinta, har lokacin da aka raba ta da abinda take tunanin shine natan, da yadda ´anuwanta suka taya ta wannan bakin cikin da fuskar Kilishi da tafi kowa nuna alhinin hakan,da irin hidimar data sha akanta don ganin ta dawo daidai.

Da yadda jama'a hatta ysnuwanta suka dinga yabawa abotarsu, da yadda bayan shekaru biyu ta kamu da wata matsananciyar rashin lafiya bayan tayi barin wani cikin, rashin lafiyar data taba mata mahaifa, da hoton fuskar likitsn dake yi musu bayani a wancan lokacin cewa da wuya ne idan har zata sake hsihuwa a rsyuwarta.

Da tarin rigingimun da tasha da wannan mijin nata kafin ya sake ta da cewar ba zai zauna da juya ba, wani abu da ya zamo mafari kuma tushen tsanar maza a zuciyarta har ta kai duka aure biyun da tayi bayan nan ta kasa tsaida zuciyarta wajen hakurin zama musamman da mijinta na ™arshe Alhaji Shamsu. GaSar da har ta kawo ta cikin wannan rayuwar da take kai, rayuwar da tun iyayenta na da rai suke kokarin hana ta har suka koma ga mahallincinsu.

Ashe duk wannan abin, aminiyarta ce sila? Kilishi ce silar da kalolin rayuwarta suka bambanta da buri da kuma tarin mafarkanta na zama uwa kuma mata a gidan mijin da zata taso da nata ikon itama, ashe zalunci da kuma cin amanar Kilishi da kullum take yiwa hangenýÿÿÿ

!"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ nesa ba'a kan kowa ya fara ba illa ita?

A lokacin ne ta rufe idanunta a hankali, tana jin zuciyarta na bugawa, da wani irin bugu da bata danganta shi da komai ba sai na cewar ita uwa ce yanzu, ita uwa ce... Ta zama wannsn uwar da a kodayaushe taje mafarki, Allah ya mallaka mata wannan dsnar ya dawo mata da matsayin da kubce daga hannunta tsawon shekarun da taje jin nauyinsu a kirjinta. Kuma abinda ta sani a wannan lokacin shine ko zata ga dan nata ko ba zata ganshi ba, zata yi abu guda daya ne da take jin kamar Allah ya bar mata numfashinta tsawon wannan lokacin don ta zama sanadinsa.

_... haka kurum nake jin cewa kamar jibin nan ba zata karasa ba wani abu zai faru._

Kalaman Kilishi a dazu da suka yi waya ya dawo cikin kanta, tabbas ta yarda da kalaman Awwalu, ta yarda Kilishi kamar wani rabin shaidan be ya fado duniyar nan, jikinta ya bata wani abu zai faru tun kafin Awwalu ya shigo gidan nan tun kafin ita ta san komai.... Abinda kawai bata sani ba shine ashe ta hanyarta din, ta hanyar ita din da take gayawa karshenta zai fara.

Zaren labarin ya fara ne tun daga wannan ranar da tazo cikin gidan nan take gaya mata sauran tsarukan da take shiryawa, tun daga wannan lokacin da suke wannan dariyar take jin zuciyarta na yin wani iri akan al'amarin aminiyar tata duk kuwa da a sannan tana jin cewa ba zata taSa iya tona mata asiri ba, sai gashi ba'aje ko'ina ba a wannan Wakin, a wannan Wakin dai da suka zauna tare nan Win shi zai zama mafarin ™addarar da bata taSa lissafawa da ita ba.

"Na san da wuya ne ki yarda dani..."

Muryar Awwalu ta cigba da magana, sai kawai ta girgiza kanta a hankali tana katse shi, kuma tare da ta buWe idanun nata ba, kalamanta bakinta suka fito, sautinsu ya fito da wani amo a hankali amma kuma wanda ya karaWe falon...

"Ka kaini muje ™auyen Awwalu, idan har na tabbatar da abinda kake faWa, zan taya ka mu tonawa Kilishi asiri a idon duniyar nan...!"

Ta faWi haka a daidai lokaci guda da adadin mintunan kiran dake tafiya a cikin wayar Hajiya Salamatu ya katse dib!

***

*No 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*

Karo na biyar kenan da Ru™ayya ke sake kiran nambar, amma da ya tafi kamar zai shiga sai ya katse kawai, ba sai wani yayi mata bayani ba, ta san ya rufe layinta ne daga shiga cikin wayar tasa, tunda dazu ta gwada da wani sabon layin ta kuma ya shiga, sai dai ba'a dauka bane.

Sai kawai tayi wulli da wayar kan gadon da take kai, ta tafi kamar zata fadi zuwa Waya karshen sai kuma ta tsaya bata karasa ba, hannunta ya dauko daya wayar tata dake gefe, ta sake lalubo nambar Jawad din a ciki, har zata sake danna nambar da niyyar kira sai kuma ta tsaya, wata zuciyar ta gaya mata cewa babu dalilin da zata cusa masa muryarta idan har ya nuna cewa baya so, sanin cuwon kai a rayuwa ma wani abu ne.

Don haka ta nufi bangaren rubuta sako, cikin abinda yake kasa da minti guda ta rubuta dalilin nemansa da take yi. Sakon ya tafi a daidai lokacin da mshaifiyarta ta turo kofa ta shigo dakin.

"Wani abu kike yi?"

Ba shiri ta girgiza kanta tana kallonta, sai ta gyada kanta sannan ta karaso ciki,da kowanne taku da take yi Ru™ayya na jin zuciyarta na bugawa sanin cewa bata da amsar abinda tazo nema din.

"Yazun nan muka gama waya da Hajiyan Sudan, ta gaya min cewa ta gama shirya komai tafiyar taku jibi ce."

Cewar Hajiya Nafisan va tare da ta zauna ba, daga kan gadon daga inda kafafunta suka lume gabadaya a cikin lallausan bargon Rukayya ta daga kanta sannan tace.

"Nima ta gaya min Maamah, Wazu da safe ta kira ni a waya ta ce min tayi settling komai sai tafiyar mu kawai."

"To kin fito da kudin?"

KuWin. Abinda take gudu kenan, tambayar da take gujewa kenan, kwanaki hudu kenan da mahaifiyar tata ta tuna mata da wasu kudi da ta taba bata ta ajiye mata a bankinta, kudade ne masu yawan da a yanzu ta manta ainihin lissafinsu, sai skayi rashin sa'a a lokacin ta samu matsala da bankinta na ajiyar kudi, don haka ba tare da tunanin komai ba ta bawa Jawad da cewar shi ya saka a Waya daga cikin bankunansa zuwa sanda zata tashi nema.

Ya karba din tun a lokacin kuma ya ajiye, sai dai daga shi har ita sunyi mantuwa da hakan ta sigar da bata sake tunawa ba sai a yanzu. Sai a yanzun da mahaifiyarta ta gaya mata cewa ta fito da kuWin dasu zasu yi komai, shi yasa a yanzu bata san ta yaya zata fara yi mata wani bayani ba da ta san ba fahimta zata yi ba, don haka ta gyaWa kanta da sauri sannan tace.

"Anjima zan fita Mamah, anjima zan dauko su gabadaya."

Sai ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan tace.

"Yau Daddynku zai dawo kin sani, ki saki jikinki ki nuna masa kin hakura a yanzu da zancen Hamidan, idan ba haka ba kuma zai Wauki matakin da zai lalata mana al'amari kin sani. Kuma kar ki sake ko da wasa ki bari ya san da zancen tafiyarki, ni na san abinda zan ce masa."

Sai tayi kokarin fito da wani guntun murmushi daga siririn lebbenta sannan ta gyada kanta.

"Ba zan yi komai da zai kawo matsala ba Mamah kin sani, idan nayi haka na san kaina na Sata."

"Sannan duk wanda ya kira ki da zancen Hamida kice musu kawai ta fara zuwa wajen mahaifinta ne hutu. Kar ki kara komai daga haka."

"Me yasa ma sai an gaya musu hakan Maamah, ba dai daga Sangaren Daddy bane masu tambayar, ni babu wayar wanda zan daga."

Hajiya Nafisa tace.

"Na gaya miki ne ko da zaku yi magana da wani..."

Bata karasa ba wayar hannunta ta shiga kara, don haka ta dauka ta kara a kunnenta sannan ta juya ta fita daga Wakin taiba magana, Rukayya ta bi ta da kallo, wani abu ya zarce a makogwaronta, ta san halin mahaifiyarta sarai, ba son dukkan wata mu'amala da ta danganci Ma'aruf take ba, kawai tana yin komai ne saboda ita kawai don haka idan har zata yi saken da za'a kasa samun kudin nan akan lokaci,komai zai iya tsayawa m, zata iya yin wasa da damarta ta ™arshe a yanzu.

Ta jawo Waya wayar tata ta duba tarihin asusun da take dashi a yanzu na banki, kudin ciki basu fi rabin abinda Hajiyan Sudan ta nema ba, babu mai bata kudi a cikin ´anuwanta ta sani, Ashraf ne kadai zai iya kallonta da wannan rahamar amma shima a yanzu wannan fetsararriyar matar tasa da baya yin komai sai da shawararta ba zata bari ba.

A wajen mahaifinta ne kadai zata iya samun wani abu amma shima ta sam wanda bai taka kara ya karya ba, don tunda yayi ritaya ya shiga hsrkar buga-bugar kwangila baya son fitar da kudi sam wanda hakan halinsa ne tun a baya, kawai suna da wadatar da ba'a ganewa ne... Kuma hakan ba daya daga cikin wani babban dalili da yasa mahaifiyarta ke dagewa kan ta auri mai kudi, don su samu ta wani Sangaren tunda ita mai son busasha ce.

Ta dafe kanta da duka hannayenta biyu, yatsun hannayen nata na shiga cikin gashin kanta, Jawad ya sha bata kudi, yasha bata kudin da tana tarawa ta san ta wuce wannan lissafin a yanzu, amma bata karba din ne da hujjar cewa ba lada take nenya a wajensa ba, don ta yarda da cewar mu'amalarsu na tafiya ne saboda haka take so, saboda ita take amfani dashi ba shi ba, saboda kuma bata son ya kalle ta da wani ™as™anci ko na kaWan.
Chapter 44 · 0% Book details