← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 87

Sashe 3

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Har yanzu baka gaya min dalilinka ba." Ishaq din ya sake fada a lokacin da yake tura kofar wani waje, don yaji karar da kofar ta bayar a cikin kunnensa kafin ya fara magana.

"So nake naga iya abinda zasu yi shi yasa na Wauki wannan matakin Ishaq, Hamida ´ata ce, idan har zan rike ta it should be in a respectful way, bana son wani yaga cewa nayi amfani da ™arfi ne na karSe ta har ita Rukayyan kuwa, don idan hakan ta faru wasu abubuwan zasu biyo baya ka sani.

Shi yasa ba zanyi wani yunkuri ba Ishaq, don kamar yadda ka fada ne a yanzu doke shari'ar zata fi karkata ne a Sangarensu ba. Wannan wasan nasu ne su suka kawo ™arar nan don haka mu basu filin da zasu taka rawar su ba tare da mun Sata musu ba, Cox idan na tashi nawa shirin Ishaq, ina tabbatar maka zanyi komai ne ta hanyar da za'a sami fahimta tsakanina da kowa, tunda a yanzu ina gujewa duk wani abu da zai jawo min tashin hankali Ishaq."

Tun daga farkon bayanin, aganganun ™arshe su suka Wauki hankalin Ishaq ba duka sauran abinda ya faWa ba.

Kalmai ne kaWai, amma tasirin da suka yi a zuciyar Ishaq suna da yawa, don shi ya san waye Ma'aruf, yana tare dashi tsawon lokaci tun daga shekarun farko na ciwonsa har zuwa yanzu, kuma a baya babu irin naci da ™orafin da baiyi ba akan ya dinga duba yanayin ciwonsa kafin ya aikata abubuwa, amma rashin yin hakan shine babban abinda ya kawo su ga matakin ciwonsa na yanzu.

Sai dai ya fahimci cewa tunanin Ma'aruf ya fara canjawa tun daga ranar da ya farka a London ya gaya masa matakin da ya kai a cutarsa, ya lura ya fara canja abubuwa da yawa a rayuwarsa tun daga wannan lokacin, kuma a yanzu da yayi wannan auren nan, ya ™ara fahimta cewa yana samun nutsuwa tare da yarinyar nan fiye da aurensa na farko, duk da har yanzu ba zai iya cewa ga takamaimai tunaninsa game da ita ba.

Sun ™arasa wayar yana yarda da tsarin Ma'aruf Win ba wai don zuciyarsa taso ba ko kuma a matsayinsa na lauya hakan ya san hakan daidai ne, sai don ya san cewa kome zai faWa a wannan lokacin ba zai canja tunanin Ma'aruf din ba.

****

*Karfe biyar da rabi na yamma.*

˜afafun Amina suka fito daga cikin toilet Win Wakin bayan ta gama yiwa kanta faWa da gargadin wankan yamma, amma babu yadda zata yi ne, don a yinin ranar kaf wannan shine kaWai lokacin da ta iya samu na yin wankan, wankan da take jin kamar ya zame mata dole ne  don karkade tarin abubuwan dake yawo a cikin kanta, sai dai duk yadda ta kai ga goge jikinta tare da zubar ruwan bata jin ko kalma guda ta fara koWewa a cikin dubunnan dake kanta balle tasa ran cewa zasu fita.

Idonta ya kai kan wayar dake yashe a gadon Wakin, wayar Ma'aruf ce da ya bata a safiyar yau bayan yasa ta debe masa nambobinsa zuwa cikin daya wayar tasa, bai ce ya bata ba har yanzu, amma zuciyarta na ayyana mata cewa hakan ce zata kasance.

Ta zauna daga gefen gadon ta Wauko ta, ™irar Samsung ce kamar sabuwa ma, ta tuna yadda tayi nacin samun wata Samsung kamar ba gobe lokacin da take ganin hotunansu a wayar Aminu, amma yau gata da Samsung Win a hannu kila ma wadda tagi waccan amma zuciyarta fayau take, babu Wigon wani abu da zata iya dorarwa akan wayar koma wani abun a gefe.

Ta dawo ta tarar Tvn gidan ma an hada ta, an siyo reciver da komai jiya da basa nan an haWa, Samirah ce ke gaya mata a Wazu da ta shigo kawo mata jakarta da ta manta a Sangarensu, don a Wazu bayan fitowarta daga dakin Hajiya Kikishi rike da magungunan nan a hannunta, bata jin jijiyoyin dake cikin kwakwalwarta sunyi aiki mai kyau har ta iso ta dawo bangarensu.

Allah ne kawai ya taimake ta bata hadu da kowa a hanya ba kasancewar sagiya ce, in banda masu wanki da ta jiyo tarin hayaniyarsu daga can gefe da kuma su Mama Rabi dake shiga bangaren Inna Danejo suna gyara kasancewar yau zata dawo kuma cikin sa'a dukkansu basu kula da ita ba.

"Tarko biyu ta Wana miki Amina."

Abinda Amma ta fara fada a wayar kenan bayan ta ™araso ta kira ta kuma ta gama sauraren dukkan bayaninta.

"Baki fahimce ni ba na sani kamar yadda kika kasa fahimtar hakan tun lokacin da kina gabanta.."

Muryar Amman ta cigaba da fitowa a lokacin da hatta yawun bakinta ya tsaya cak! saboda ruWani.

"Tace miki a yanzu magungunan sa sun dawo hannunki Amina, amma ta Wauko sauran  da yake sha ta baki su? Ko kuma shi ta gaya masa cewa zai dinga karbar maganinsa a hannunki?"

Kuma tambayar ta wuce da wani shiru mai tambarin nazari kafin ta iya amsawa a a hankali.

"A'a Amma, wadannan din kawai ta bani."

"To kiyi tunanin ki gani Amina, da sunan maganin me zaki dauki waddannan ki bashi kai tssye? Wane bayani zaki yi masa da zai gamshe shi ya karSa? Idan ma ya karSa Win yasha kuma ciwon nasa ya biyo baya me kike tunanin zai faru? Daga shi har sauran jama'ar dake kewayensa me zasu yi tunanin akanki Amina?"

"Kowa zai zarge ni Amma."

Amsar ta fito kai tsaye tun daga zuciyarta, don babu wuya ta za™ulo ta daga cikin tarin abubuwan dake yawo a cikin kanta, kuma kai tsaye itama Amman ta cigaba.

"Tabbas kowa zai zarge ki Amina, ai babu wani kewaye-kewaye akan hakan. Kilishi mugun ice ce na gaya miki, irinsu ne mutanen da zasu sa ka kashe kanka ba tare da ka san kana soka wu™ar ba, kuma na gaya miki tun farko, dole ki maida ™wa™walwar ki ta koma irin tata Amina, dole ki dinga tunani irin wanda take yi idan ba haka ba a kurkusa zata dulmiyar dake ba tare da kin ya fahimta ba.

A yanzu ta baki iya wadannan magungunan ne  don ta gwada ki, taga ta yadda zaki cika umarninta kuma ki kare kanki a lokaci guda, taga ta yadda zaki iya bashi magungunan ba tare da kin shafawa kanki jan fenti ba kema. Tunaninki take son ta gwada, taga idan har zurfinsa ya kai ta saka ki cikin lamuranta, sannan kuma a lokaci guda ta tabbatar idan har da gaske kin goyi bayanta kamr yadda kika ce, kuma ina tabbatar miki Amina, idan kika fadi ko guda daya a cikin wadannan tarkon nata biyu, shikennan kin fara rusa darajarki a wajenta.

Ba zata kore ki a lokaci guda ba, amma zata dauki wani mstakin kwatankwacin yadda tayi wa Aminu don ta ™ara tsorata ki, sannan zata ™ara gwada ki, idan akayi rashin sa'a a karo na biyu kika sake faduwa shima, zata juyo kanki ne a lokacin, zata lahanta ki ta yadda zaki ji a jikinki ki san da gaske take sannan ta sake gwada ki...."

Muryarta ta Wan tsaya kafin ta cigaba.

"... a karo na karshe ne Amina, idan ta sake baki wani abin kika kasa, ina tabbatar miki da cewar Kilishi zata iya rufe kawar dake gabadaya!"

A wannan lokacin Amina taji sanda zuciyarta ta buga a kirjinta kafin fatar bakinta ta shiga maimaita kalaman hasbunallahu wa ni'imal walkil da fatar babu tsayawa, kuma sai da Amman ta tabbatar kalaman sun gama shigewa cikin kanta wucewar wasu sakanni sannan ta cigaba.

"Amina, wannan abin da nake gaya miki gaskiya ne, don mutane irin Kilishi suna aikata abinda yafi haka ba tare da sunji ko War! a ransu ba, shi yasa nake son tun a yanzu ki tattara hankalinki waje guda ki saurare ni, kiyi duk abinda nace, ki yarda da maganata ta cewar da kifi ake kama kifi, kin fahince ni ko?"

Ta san ta Waga kanta a lokacin kamar Amman na kallonta, amma bayan hakan ba zata iya tantance yadda zuciyarta ta dinga tsere a ™irjinta ba, ta san kawai ta dam™e wata kwalbar turare dake gefenta a lokacin don tattara dukkan nutsuwarta, kuma bata san ya akayi hakan yayi tasiri ba, don tayi nasarar ture  dukkan hargitsin daje cikin kanta ta cigaba da sauraren mahaifiyar tata.

"Ki narka magungunan a cikin lemo Amina ki bashi yasha ba tare da ya sani ba, ki kwantar dashi kamar yadda ta gaya miki ba tare da shi kansa ya sani ba Amina, ki nunawa Kilishi da gaske kike kin goyi bayanta, ki buWe mata zuciyarki ta yadda zata sakanksnce ta karSi yardarki, ki nuna mata zaki iya, zata ga hikimarki, zata jinjina miki, kuma zata jawo ki jikinta. Wannan shine matakin farko da zamu fara cin nasara akanta Amina."

Ta sani cewa ta yarda da dukkan maganganun mahaifitar tata, ta san haka ne, ta san gaskiya ne... Ta san wannan itace sahihiyar mafitarsu, amma zata iya?  Zata iya? Idanun Ma'aruf kawai idan ta hango sai zuciyarta ta ™ara nanata mata cewar ba zata iya ba, ba zata iya ™arawa akan wahalar da yake sha yanzu a rayuwarsa ba, idanunsa kadai idan ta kalla tana jin kamar zata iya tsinto tarin abubuwan dake damunsa Waya bayan Waya, yana yawo dasu a kirjinsa da kuma kafaWarsa.

To ta yaya kuma zata iya zama karin wata matsalar bayan duk bayanin da yayi mata jiya cewa yana son samun sau™i a wajenta? Bayan haka ma idan tana tare dashi ta lura cewa ™wa™walwar ta bata iya tuna duk wannan hargitsin sosai mantawa take da komai kawai sai shi da ka nasa maganganun.

Wani abu ya wuce ta makogwaronta da ba ta san meye ba, taji hannayenta da ta rike wayar dasu duka biyun suna rawa, sai kawai ta ajiye ta a gefe sannan ta mike, man da take shafawa tun zuwanta gidan ta dauko akan mudubi, har zata bude sai kuma ta tsaya tunanin anya ba fari yake sata ba kuwa, don ita kanta taga ta canja kwana niyu sannan ma Aminu yana ta tsokanarta cewa tayi haske, kuma ta san wannan ba sharrinsa bane.
Chapter 3 · 0% Book details