Sashe 79
Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hajiya gani nan, koma kiyi zamanki.."
Ta koma din a hankali ta zauna yayin da Jumman tayi gaba ta bude kofar, kuma da yake kujerar da take zaune itace daidai saitin kofar, sai ya zamana Jumman na buWewa hoton ™aninta Ashraf ya shiga idanunta a lokaci gyda da gabanta ya fadi zuciyarta ta buga a kirjinta, ba wai ganinsa ne ya haddasa hakan ba...
Don kusan kullum yana zuwa duba du ita da mahaifiyar tasu tunda suka tare a gidan, kusan koyaushe ya tashi daga aiki nan yake faraboyowa kafin ya wuce gidan nasa, don haka yanyin fuskarsa a yanzun shine ya tsorata ta, wani yanayi ne da rabon da ta ga irinsa a tare dashi tun a lokacin farkon ciwonta, sanda suna Niger kafin ma ayi transfering dinta zuwa asibitin da tayi kusan jinyar watanni biyu a cikinsa anan Nigeria, lokacin da ta farka ta tarar da sakon dashi da kuma Ahmad suka kawo na saki tsakanin iyayen nasu.
Wani abu da tunda ya faru daga su Ashraf din har ´anuwansu suke ta fafutukar neman yayi hakuri ya mayar da Hajiya Nafisan amma duk yadda akayi, duk kokarinsu baya sauraren kowa yace ya riga ya yanke hukuncinsa, tunda har zata iya rufe idanunta akan saSon Allah ta kuma tura ´arta har wata ™asa wajen neman magani don biyewa bukatun duniya, to tabbas bai ga amfanin zamansa da ita ba.
Ita kanta Rukkayan sau Waya yaje ya duba ta a asibiti, a ranar a gaban Hajiya Nafisan ya bata hakurin kuskurensa ma cewar bai bata uwa ta gari ba a matsayinta na ´arsa sannan yayi fatan cewa abinda ya faru zai zama izna gare daga yanzu wajen gane tarin laifukan da ita kanta tare kuma da mahaifiyar tata suka taya ta aikatawa.
Sannan ya gaya mata cewa ta dawo wajensa da zama duk ranar da aka sallame ta tunda duk wata dawainiya da tsadar asibitin ma shi yake biya amma bayan an sallane tan, sai wannan tausayin da ubangijinke halittawa tsakanin ya'ya da iyayensu musamman ma Uwa... Ya hana ta juya baya ta koma wajen mahaifin nata.
Ashraf ne ya kama musu wannan gidan acan hanyar Tarauni suje zaune, kuma anan mahaifiyar tata tayi jinyarta tare da yanuwanta dake yawan zuwa akai-akai suna taya su kwana, a yanzu ta sami sauki sosai har tana mi™ewa tsaye kuma maganarta ma ta fara fitowa sosai.
Sai dai har yanzu bata koma Rukkayyan da take a da ba, bata koma wannan kyakkyawar Rukayyan dake ji da kyan da take ganin ta hanyarsa zata iya samun komai a duniyar nan... Komai din da bai hada da Ma'aruf ba, wanda hakan sho ya rude ta wajen biuewa kowacce irin shawara da mahaifiyarta tata da ™awarta Hajiyar Sudan suka kawo, tunda ko a karon farko ta sani cewa da ™yar ta same shi a rayuwarta.
An kawo Hameeda kusan sau uku tazo ta duba ta daga can gidansu Ma'aruf din da a yanzu Baffa ya aiko an shaida musu karara cewa yarinya ta dawo hannunsu tunda su suka kawo ta da kansu amma lokaci bayan lokaci za'a dinga kawo ta suna ganinta, kuma itama yarinyar ko kadan bata nuna tana sha'awar zama ba musamman ganinsu a wani sabon gidan ba inda ta saba ganinsu ba.
Sannan kamar kusan kowa, sun ji labarin abinda ya faru a gidan su Ma'aruf game da Hajiya Kilishi, tayi mamaki amma ba wani sosai ba don tun lokacin da ta zauna a gidan dama ba wani shiri suka yi sosai ba, don haka ta yarda duk abinda aka fada din zata aikata. musamman da su ma suke ji da tasu matsalar sai basu wani daukaki abin sosai ba.
Ashraf ya shigo a lokacin da wannan yanayin na fuskarsa, yanayin da ba ita kadai ba hatta Jamilan da ta buWe masa kofa a hankali ta rufe sannan ta juyo ta fita daga falon tana basu waje.
"Sannun da zuwa, ya aikin?"
Rukkayan ta faWa a hankali tana kallonsa bayan ya ajiye jakar hannunsa.
"Alhmdlilah, bata nan?"
Ta san wa yake nema don haka ta girgiza kanta.
"Tana wanka yanzu zata fito..."
Ta fada sai kuma ta sake cewa.
"Me ya faru?"
Don zuciyarta ta kasa tsayawa waje guda da tunanin abinda ya farun, shima kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya mika hannu ya bude zip din briefcase din da ya shigo da it, hannun nasa ya zaro wani envelope da a lokaci guda ya sa zuciyart bugawa, yaba tuna mata da emwanda ta gani na karshe a hannunsa shi da Ahmad, na sakin mahaifiyar tasu.... Yanzu kuma me ya faru?
"Daddy ne zai yi aure Rukyya,ga kayin daurin auren nan, sati mai zuwa...!"
Ya fadi hakan daodai lokacin da Hajiya Nafisa ta shogo falon, sakon kuwa ya shiga kunnenta yana sa zuciyarta nugawa ta kuma tarwatse a kirjinta!
Rukayya ta hadiye abinda bata san sunansa ba a makogwaronta, shikenan! Kamar ita Mahaifiyarta tayi biyu babu akan mutum guda, ta rasa mahaifinsu ta sake rasa shi kamae yadda itama ta rasa Ma'aruf sau biyu a tata rayuwar... Da gaske Daddy yake kenan, da gaske ba zai mayar da ita gidanta ba...
Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce ka kiyayi zuciyar mai hakuri lokaci aka kaishi karshe.... Mahaifinsu mutum ne mai tsananin hakuri da kuma kawar da kai akan tarin abubuwa, shi yasa tun farko mahaifiyar tasu ta samu sake yin abubuwa da yawa da taga dama... Tunda sau da yawa ma zasu yi abu har su gama bai ma sani ba balle ya hana, baya takura musu baya takura mata, ko lokacin da tayi aure har biyu bayan Ma'aruf, yanuwansa sai da suka nuna bacin ransu na ganin bata wani dadewa take sake fitowa amma shi bai ce komai ba, bai yi mata ko ™orafi ba ba balle faWa.
Idan kayi laifin da zaka bashi hakuri ma wani lokacin ba ma sai ka furta ba, alamun niyyar ka kaWai kan sa ya yafe ma tun kafin ma kace wani abu... Don haka ba ita kadai ba, tabbas kowa ma ya sani cewa da gaske mahaifiyarsu ta kai shi ™arshen da ba lallai ne ya dawo ba.
A lokaci guda wata kwalla mai dumi ta gangaro kan kumatunta, tana tuna mata da tarin lokutan da suke cikin jin dadi da fantamawa son ransu... Rayuwa bata da adalci...
"Rukayya.."
Ashraf din ya sake kiran sunanta yana sska ta Wagowa a lokacin da Hajiya Nafisa ta karaso cikin falon ta dauki envelope din katin daurin auren tana dubawa, ta a duba sunan wata mai sa'ar da rayuwa ta zaSo ta wajen bata kyakkyawar damar da ita tayi rikon sagegeduwa da ita.
"Naga anyi posting daurin auren Jawad a facebook, kin sani?"
Kalaman suka tsayar da tunani dama numfashin Rukayya cak a lokaci guda... Taba jin wani abu na yawo a cikin kanta da bata san menene ba, jiri ya debe ta daga inda take zaune, kanta ya zagaya ya sake zagayawa a cikin Wakin kafin idanunta su dawo dashi kan Ashraf dake kallonta har a lokacin, sai kawai ta girgiza kanta da ™arfi a yanzu kwallar dake fitowa daga kowanne idonta tana tarwatsewa a iska...
Tabbas Rayuwa bata da adalci! Musamman ga mata irinta wanda basu da hankalin fahimtar cewa duk kwaSewar al'amari, namiji yana da damar tsame kansa ya bar macen a cikin rauninta wanda ba zai iya kaita ga matsayin wasu damar dashi zai samu ba...
Zai barta a cikin ™uncin da zata zauna tana maimaita kalaman Rayuwa bata da adalci!
***
*Abuja.*
*New Horizon Street, Wuse 2.*
*05:30pm.*
Iska ta kaWa farin labulen ™aton windon dake manne da wani ™aton falo, wanda yake a saman benen gidan. Tagogin windon gabaWaya a bude suke, an wangale su ta kowanne gefe yayin da sassanyar iskar daminar da ake yi ke kada labulayen dake jikinsa kalar ruwan toka, kalar da ta dace da kusan komai na cikin falon da yake da sassaukan ado, (Grey &ash) sai kuma tsilla-tsillan abubuwan da suke kalar baki kamar sauran kayan electronics.
Mintuna basu fi goma kenan ba da Wauke ruwan samn da aka fi kusan awa guda ana zabga shi, don haka garin a lulluSe yake da duhun hadari da kuma na yamma wanda a lokacin ™arfe biyar da rabi ne.... Koina a jike yake sharkaf dauke da danshin dake komawa sanyi-sanyi yayin da bishiyun dake harabar wajen ke ta rangaji a cikin iskar na jin dadin yanayin da kuma jikewarsu.
Falon dogo ne wanda a can ™arshensa ya hade da wajen dining da kuma kitchen duk a ciki, iri Waya sak da tsarin gidajen turawa kamar yadda akayi ginin a haka tun daga waje.
Akwai matattakalar bene daga gefe wadda akayi kusan rabi na jikinta da gilashi fari kamar yadda mafiya abubuwa suke a gidan, matattakalar zata kai ka zuwa sama inda anan zaka tarar da kofofin manya-manyan dakuna guda uku masu dauke da hadddun toilets da kuma walk-in wardrobes...
A watannin farko da suka zo gidan, Amina zata rantse ta shafe fiye da wata guda kafin ta gam sanin komai na gidan ta kuma saba da tsananin kyawunsa da take gani. Har faduwa ta taba yi har kasa watarana data yi alwala ta fito daga toilet saboda tsabar santsin marbles din dake gidan wanda ko mai ta shafa a a kafarta tana jin kamar zata zame.
Watansa hudu kenan a ciki, amma komai yana nan da kyallinsa kamar sabo, hatta kayan kitchen wanda su tafi komai tabawa a gidan balle kuma sauran dakunan da ta kan yi kwanaki biyu ma bata leka ba. Hatta doguwar kujerar falon da Ma'aruf kullum yake kwanciya akai bata taba nuna alamun nauyinsa na nunawa ba, ko kuma tace nauyinsu tare...
Daga cikin falon, Amina na tsaye a jikin sink din dake tsakanin drawers na kitchen din, ta kunna fanfon tana wanke wani farin kwano data dauko yayin da sassanyar iskar daminar ke shigowa tana kada ´an kananan gashinta da suka taso sama saboda laushinsa, babu dankwali akan nata sai gashinta da ta daure da wani yalon ribbon, rabon da ta taje shi ma kusan kwanaki biyu kenan.