← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 87

Sashe 34

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:55 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*12*

~~~~~~

_ You don't always have to make sense of it all, sometimes you just follow your happiness._ _-Unknown._

***

*Bayan wasu kwanaki.*

"Ayiryiryiryiriiiiiiiiiii.....!"

Wata tsohuwa ta rsngaWa guda a lokaci gyda da jama'ar dake dawowa daga wajen daurin auren suka shigowa gidan, mazs ne fal samari da dattijai suna ta sauka daga motocin dake shigowa suns parking a harabar compound din, kusan kowannensu sanye da fararen kaya sai fara'a suke yi yayin da ksmshin turarensu ke gaurate iskar wajen yana haduwa dana matan dake waje suma cikin kwalliyarsu da kuma wadanda ke fitowa don tarar angwaye biyun dake zagaye fal cikin abokansu.

Kidan algaita da kuma kirari ga angwayen dama guda kawai kake ji a tsayar hayaniyar da wani baya jin wani.

Daga cikin morarsa wadda yayi parking a can gefe bayan ya shigo gidan, Jawad ya tsaida idonsa akan screen din wayarsa yana kallon lambar da har a bayan kwakwalarsa bai taba tunanin ganin kiranta ba.

Barbiee ( Rukayya.)

Missed call daya ne, daga shi babu kari balle kuma sako ya biyo baya, ya cije lebbensa a hankali, mamaki yake na yadda skaui har yanzu nambarta take cikin wayarsa s tunanimsa ya goge tun a ranar da ya baro waken da suka hadu na karshe, amma kuma sai ya tuna cewar yayi saving nambar tata ne fiye da sau biyar a wayar tasa da garafai daban daban.

Don haka kai tsaye tafi zuwa kan nambar, ya danne ta ya goge, sannan ya koma vikin layin contact din nasa, ya nemo dukkan harafan da yayi saving nambar tata ya goge su gabaWaya.

_"... Ka taimaki kanka ka manta dani Jawad.."_

Haka tace, haka ta gaya masa, dune harafan da suka fi kowanne Wagawa a cikin maganganun da ta fada masa, sune harafa da a kowacce rana zuciyarsa ke maimaita masa su fiye da kirgensa, kuma tun daga wannan lokacin zuciyar tasa ke neman abun da zai sa ta manta da ita din, kuma Allah ya sani ya gwada tarin abubuwan da bai san iyakarsu ba tun daga wancan lokacin a ciki har da ™udirinsu shi da Haro na shirin daukar fansa akan Ma'aruf, amma duk cikin tarin abubuwan nan, babu wanda yake jin yana tafiya har cikin zuciyar tasa kamar yarinyar nan.

Tsanar da yayi mata mai yawa ce a kwanakin baya, amma yanzu baya jin hakan ko kadan, wani abu yake ji da bai ma gama lissafa shi ba, abinda ya sani kawai shine, duk sanda zai gan tan zai ji kawai yana son ta cigaba da kasancewa a wajen, shi kadai ya san yadda abinda ke zuciyarsa ya dinga bin iska shekaranjiya daya tsare ta taci abincin nan a Sangaren sa, kuma bai san me yazo kansa ba sanda ya ri™e hannunta ya maida ita baya lokacin da take kokarin fita shi kuma ya hango wani Wanuwansu Ahmad da yazo zai shigo Sangaren nasa.

Ba abinda zai faru don ya ganshi da ita, ba abinda ya isa yace, amma haka kurum yayi saurin kamo hannunta ya dawo da ita ciki, kuma itama hango shin da tayi yasa bayan ya dawo da ita, ta shige bayan ™ofar ta tsaya jikinta na rawa.

Kuma bayan ya sallami Ahmad din ma da kyar ta fito, ta tsorata sosai bai san me yasa ba, watakila shi yasa tun wannan lokacin bata kara bari sun haWu ba, tun wancan satin ske bikin amma sau daya ya ganta kawai daga windon dakinsa taba hoye dawani yaro sannan ga wata yarinya kuma a hannunta tana yi mata wasa.

Kwankwasa kofar gilashin motar da akayi ya katse tunaninsa, ya juta yaga wani ™aninsa ne Mukhtar, sai ya zuge gilashin ™asa a hankali, tarin hayaniyar wajen ta shiga kunnensa a lokaci guda.

"Nace dan Allah akwai mutanen da zaka Wauka a motarka ne?"

"Zuwa ina?" Ya tambaya da mamaki.

"Wajen reception din, yanzu da angwayen sun fito za'a juya ai."

Sai kawai ya girgiza kansa.

"Bana jin zan je, sai dai in baku motar."

"Thank you so much bro, su Na'im zan dauka dama wallahi na rasa mota."

Da haka ya fito, ya mi™o masa mukullin motar sannan ya nufi cikin gidan, a ™a'ida bangarensa ya kamata ya tafi ya kwanta don tunda aka fara hayaniyar bikin ya manta yaushe rabon da ya samu wani isasshen bacci ba, amma haka kurum tunaninsa ya gaya masa cewa ya tafi bangaren mahaifiyarsa ya nemi abinci, babu mai kawo masa a cikin wannan hayaniyar, ba tunawa dashi zasu yi ba ya sani.

Ya isa Sangaren yana fara cin karo da kanmensa mata da kuma tarin kawayendu fal a falo, har yanzu ya kasa lissafin yadda kowa ke dokin wannan bikin, shi mutun daya kawai ya gaiyata wani Wan office Winsu, shima ba gayyatarsa yayi ba akan table dinsa ya ga katin yace masa shima yana da Waurin aure a masallacin kuma a ranar don haka zai zo, kuma bai ganshi ba ma.

˜awayen su Khairat din suka hada baki wajen sirranta muryoyinsu su suna gaishe shi, ya amsa jai tsaye sannan ya nufi wajen wasu cousins din nada mata dske wajen dining, a cikinsu har da Ibrahim wanda aka yi masa maganar ya nemo nasa aiki, bayan sun gaisa da kowa suka shiga magana da Ibrahim din akan interview din da zai zo yayi, yana fada masa abubuwan da ya kamata ya duba.

Kuma sanda Ibrahim din ke masa wani bayani ne ta fito daga dakin, Zainab... Hannunta dauke da wani ™aton tray da ta ciko tarin plates da kuma cokula a ciki.

Ta yo hanyar cikin falon alamun fita zata yi, daidai sanda wata mata da bai san wacece ita ba ke cewa.

"Zainab har yanzu kina nan? Kowa ya shirya ke baza ki je ki shirya ba gashi har ´an Waurin aure sun dawo..."

Da murmushinta a fuska tace.

"Maman Nasir yanzu zanje, kwanukan nan na tsaya debowa idan ba haka ba yanzu zan neme su in rasa."

Kwata kwata bata lura dashi a wajen ba, dai da wata Maryam daga bayansu ta kora sunanta.

"A kawo mana alala idan ya gama."

A lokacin ne ta ganshi, idonta ya shiga cikin nasa kuma ya haska da wannan tsoron fiye da wannan lokacin da yabi ta a baya, wannan karon babu mamakin, wani abu ne kamar tsoron kawai shi kadai, irin tsoron da ya gani lokacin da ya riko hannunta da kuma sanda ta tsaya daga bayan ™ofar nan, sai kawai ta Wauke kanta da sauri tana amsawa Maryam Win, kuma ba tare da ta jira komai ba ta nufi hanyar ™ofa da niyyar fita amma kafin ta kai ga fitan ya kira sunanta shima yana tsayar da ™afafunta a lokaci guda.

Da tazara mai dan yawa tsakanin wajen dining don da yake tsaye da kuma can bakin ™ofar, kuma ba daga murya yayi ba, amma a cikin hayaniyar dakin ta jiyo shi tsaf kuma ta sake juyowa a hankali, sai dai wannan karon bata kalle shi ba, idanunta na kan kwanukan data ri™o ne.

"Ki kai min abinci side dina yanzu."

Ya fadi abinda banda ita, bai shallake tunanin kowa ba.

***

Kusan minti goma kenan yana zaune akan kujerar falonsa yana jira, hayaniyar gidan ta ragu sosai don mazan duk sun tafi wajen reception, sai kiWan ™warya kawai da yake juyowa daga can nesa.

˜ofar Wakin ta buWe a lokaci guda, a hankali tana gaya masa waye tun ma kafin ya Wago ya kalla.

Kuma bayan tayi sallama bata ce komai ba tayi kwana ta nufi hanyar dining da kayan dake hannunta, shima bai amsa sallamar ba ya mike yabi bayan nata, ko ta san yana binta bata juyo ba sai da taje har gaban teburin ta ajiye tray din hannunta tukunna.

"Why are you avoiding me?"

Kai tsaye ya tambaya yana lura da cewa hannayenta rawa suke tun kafin ma yace komai.

Sai ta juyo da sauri tana ™ara yin baya da ™afafunta saboda yadda ya tsaya dab da ita, kuma tuna cewar bata fahimci abinda yace din ba yasa shi saurin gyara zancen nasa.

"Me yasa kike guduna?"

Kanta na ™asa ta shiga girgiza shi.

"Wallahi ban ganka bane tun rannan, aiki nake tayi kullum... Mutanen da yawa."

"Kuma ke baiwar kowa ce da sai kinyi musu duk abinda suke so?"

Kai tsaye ya sake tambaya.

Ta sake girgiza kanta.

"Yawanci Wawainiyar yaransu ce, kuma yaran ne suke ta zuwa waje na."

Ya tuno sanda ya ganta da goyo da kuma wata yarinya a hannu, sai a yanzu tunanin Allah kadai ya san yaransu da take goyawa a rana ya kama shi, ba shiri yaja tsaki mai ™arfi.

"Kar na sake ganin kin dauki yaron wani daga yanzu."

Bata ce komai ba yace.

"Kin ji ni?"

Muryarsa na Wagawa kaWan, sai tayi saurin daga kanta alamun ta gane, har yanzu hannayenta rawa suke, yaji kamar ya kamo su ya rike a cikin nasa, amma kwakwalarsa ta gaya masa cewa bayan ™ara rikita ta da zai yi watakila zata iya yi masa ihu ma idan yayi hakam. Don haka sai kawai ya canja zancen da abinda yake son tambaya.

"Kinyi wanka?"

Tambayar ta tayar da wani dan karamin bom a cikin kan Zainab da yasa ba shiri ta Wago ta kalle shi tana zare ido, kuma shima ya lura da hakan don hannunsa Waya yasa ya sosa ™eyarsa sannan yace.

"Ina nufin me yasa bakya canja wannan kayan, me yasa kowa yayi kwalliya banda ke?"

Sai tayi kokarin hadiye wani abu a makogwaronta sannan tace.

"Ba komai dama... dama yanzu zanje in shirya."

Tunda bakinta ya furta 'dama' har sau biyu ta san ya fahimci ™arya take yi, ilai kuwa ba shiri ya hade ransa irin yadda take tsoro sannan yace.

"Zaki gaya min gaskiya ko kuwa?"

˜walla ta taru a idanunta kafin tayi ™arfin halin fada masa sbinda ke cin ranta tun kwanaki, maganar da ta kasa gayawa kowa tunda bata da wanda zai saurare ta sai shi din da ta san ba zai yarda da karyarta ba.

"Bani da kaya ne."

"Baki da kaya?..." Mamaki ya fito a cikin muryar tasa.
Chapter 34 · 0% Book details