← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 87

Sashe 58

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi Malam, bani da masaniyar komai, ni ban san me suke nema a wajenta ba, ban san ma me yi musu kwatancena ba..."

"Ina zaki sani Talatu? Dama ina zaki sani... Muna zaune a majalisa kawai mota ta faka aka ce wai gidana ake nema, kin kunyata ni a cikin jama'a, ace ina zaune a gida da mata amma wasu maza daga waje suna zuwa nemanta? Wallahi darajar Malam da na karbi aurensa a wajenki kawai kike ci Habiba, amma anyi na farko anyi na biyu, na rantse da kabarin ubana aka sake samun wani Wan kaza-kazan da zai zo nemanki sai kin bi shi, billahillazi kafar sa kafarki, na gama zaman aure dake..."

Talatu ta gyada kai cikin amincewa da sauri sannan kafafunta suka durkusa har kasa cikin kasar wajen tana neman afuwa. Kuma sai da ya gama cikarsa ya bayse sannan yayi kwafa yace.

"Šauko hijabinki, suna soro muje inji me ke tafe dasu."

Sai ta girgiza kanta, tana kallonsa tace.

"Wallahi Malam ba sai na fita ba, waWancan mutanen da suka zo sun bar lambar wayarsu suka ce in kira su idan na samu wani labari, to indai suma Hanne suka zo nema zan basu lambar su nemi waWancan su gaya musu komai, ka yarda dani Malam wallahi bani da wata ala™a dasu."

Muryarta na rawa cike da tsoro yayin da yake kallonta idanunsa na haskawa da dimbin bacin rai da kuma fushin da a zuciyarta take kirga adadin kwanakin da zasu wuce kafin ta sake samun fuskarsa.

Muryarsa cike da ba'a, yace.

"Akwai abinda zasu nema ne da ya wuce Hannen? Duk danginku akwai mai jawo muku tsiya ne kamar ita?"

Talatu bata ce komai ba tana tsugunne a gabansa, hannayenta dake tallafe da goyon ´arta na rawa a ™asan goyon, kuma bata san lissafin da yake yi ba tsawon wucewar wasu mintuna kafin yace.

"Tashi ki Wauko lambar, wannan shine na farko da kuma na ™arshe a lamarin nan na gaya miki Talatu..."

Ba shiri sai ta mi™e tsaye, kuma bata ko damu da karkaWe kasar da ta Sata kafafunta ba, ta mi™e da sauri ta nufi ™ofar Wakinta, kuma cikin abinda bai wuce minti guda ba ta dawo ri™e da wata farar takarda da take a mi™e samSal, ya fizga tamkar zai yaga sannan ya juya ya nufi hanyar fita.

A ™ofar gidan ya tadda Jawad da kuma Nura dake tsaye suna jiransa, ya juya ya kalli motar da suka bari a can gaban gidan, wannan yarinyar dake ciki har yanzu tana nan, ta juyo tana kallonsu idanunta na na kallonsu a zare, sannan ya kalli tarin yara har da matasan da suka tsaya daga can nesa suna kallo su, don labarin ma™udan kudin da aka bashi ya danna a aljihu bayan ya fara fadan babu mai ganin matarsa ya kusa biye kunnen duk wanda ya sanshi a lokacin.

Ya ja tsaki mai tsawo yana fadin.

"Allah wadaran munafukai...!"

Sannan ya juyo ya sake kallon Jawad Win dake a gabansa.

"Yallabai, matata tace bata da wani bayani da zata yi maka don Hanne ta rasu shekaru shida da suka wuce, amma ga wannan lambar, idan ka kira watakila zaka sami wani bayani a wajensu, don suma kamar kai sun zo nemanta kwanaki."

Idanun Jawad na kallonsa har yaje karshen zancensa, ba haka yaso ba ko kadan, yaso akalla yaga Talatun yaji bayanin komai daga wajenta, tunda sun sha tambaya tare da wannan matashin Nura amma babu wanda ya gane Hannen da suke nema sai da kyar aka samu wanda ya faWa musu cewa matar ta daWe da barin garin amma akwai wata Talatu da zata iya basu labarin inda take.

Kamar zai yi magana, amma sai zuciyarsa ta shawarce shi da cewar yabi mutumin a haka, don ya lura idan ya matsa za'a iya samun matsala, yau ya fara nema ba lallai ya samu komai a yau ba dama... Don haka sai kawai ya gyada kansa sannan hannunsa ya karSi takardar kafin bakinsa ya furta godiyar da bai san ta wace sigar kalamai suka fito ba... Idanunsa suka manne da suna da kuma nambobin dake rubuce a jikin takardar lokacin da mutumin ya juya yana zagin jama'ar dake shirin taruwa a kodar gidan bunun.

Hajiya Salamatu.
080673....

****

Ruwan da ya sauka akan fuskar Awwalu mai tsananin sanyi ne fiye da na farko da Šantaro yasa aka watsa masa awanni kaWan da suka wuce.

Ya buWe idanunsa cikin tsananin firgita, yana kallon wadanda ke tsaye a gabansa, da farko inuwoyi idanunsa suka fara nuna masa kafin fuskar Šantaron dake saitinsa ta fito tar cikin hasken safiyar dake ratsawo cikin fankon Wakin da aka kawo shi aka kulle tun a daren jiya.

"Ni zaka yiwa shunen ´an sanda Awwalu? Ni zaka sa in aika yarana gidanka alhali ka aika ´an sandan can? Ni zaka yaudara Awwalu?"

³an sanda! Kalmar ³an sandan ta doka wata irin tsawa a cikin kan Awwalu a lokaci guda tana sa shi wartsakewar da ba shiri.

"³an sanda suka gani a gidan nawa?"

Muryarsa ta fito tare da shakku da kuma tashin hankali da baya neman tabbacinsa, kuma Šantaron bsi yi maganar ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yayi wa yaransa biyu daje tsaye da bokitai alama da su karasa zuba masa ruwan bokitan dake hannunsu wanda Waya na zafi ne Waya kuma na sanyi, mai rike da na zafin ne ya fara juye masa tun daga saman kansa sannan na sanyin ya kwara masa shima har ™asa.

Tasirin zafi da kuma sanyin da suja ratsa jikinsa suka sa dukkanin jijiyoyinsa ri™ewa bakiWaya, ya shiga kokawa da dawowar numfashinsa a kirjinsa kafin ya muryar Šantaron ta ratsa kunnensa.

"Kai baka isa ka tona min asiri ba Awwalu, wallahi, wallahi daga yau taka ta kare!"

Kuma ga mamakin Šantaro sai kawai Awwalun yayi murmurshi, murmushi mai fadi sannan ya girgiza kansa, don abinda Dantaron bai sani ba shine su duka biyun ne tasu ta ™are!  Tunda ya riga ya jawo shi jikinsa shikenan tasu ta kare gabaWaya!

***

_Me kuke tunani ya haWa Kilishi da Wan sanda?_

_Kuna tunanin hakan wani shirinta ne?_

_Shirinta na gaba wato kashe Baffa?_

_Ko kuma wata kaddarar ce daban?_

_Me kuke tunani ya faru lokacin da su Jawad suka shigo Garun Albasu?_

_Zainab bata shaida masa Garinsu bane? Ko kuma Nuran da yazo bai gane ta bane?_

_Jawad ya samu lambar Hajiya Salamatu, me zai biyo baya?_

_Mabudin komai dai, ya riga ya iso!_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:58 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*ýÿÿÿ

!"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*20*

_Inch by inch. Life is a cinch. Yard by yard. Life is hard._ _ John Updike, Rabbit Redux_

~~~~~~

*Tariyar Baya.( Flashback)*

"Hajiya akwai matsala fa, motocin ´ansanda ne gasu nan zagaye da gidan, na tsaya daga gefe ba zan iya karasawa ba...."

Muryar Sadik din ta faWi kalaman da a lokaci guda suka dako zuciyar Hajiya Kilishi da wani irin tasirin da tunda take a rayuwarta bata taSa jinsa ba.

Bugun zuciyar tata ya cika kunnuwanta a lokaci guda da sauran bayanin Sadik din ya Sace daga cikin kunnuwanta, ba shiri dukkan jikinta ya shiga rawa yayin da ta nemi gefen gadon nata ta zauna, hannunta daya da baya rike da wayar ya kamo zanin gadon don neman tallafi.

"Kana ina yanzu Sadik, ka bar wajen?"

Ta tambaya da sautin da taji kamar ba nata ba saboda ™arar buguwar zaciyar tata da shi kaWai take iya ji har a yanzu. Tun da rana da ta daga labulen dakinta ta kula da gajimaren da ya baibaye sararin sama,  ya rufe ta kusan bakidaya saboda haka babu kadawar iska sosai, amma bata tabbatar da hakan ba sai a yanzu da take jin gumi ko tawanne Sangare na lulluSe ilahirin jikinta.

"Ina daga gefe Hajiya, na le™a layin ne sai na dawo daga baya nake kiranki."

Wannan karon, muryar Sadik Win ta amsa tar a cikin kanta.

Sai ta mayar da wani abu dake shirin tasowa daga makogwaronta kafin tace.

"Motocin ´ansanda ne kaWai a wajen Sadik?"

Ya girgiza kansa.

"A'a akwai wata karamar mota kirar Accord."

Accord. Accord... Kalmar ta rangaWa a cikin kan Kilishi ta sigar tashin hankalin da ba'a saka masa rana ko lokaci. Accord motar Ma'aruf ce! Me yake shirin faruwa? Ta yaya zasu gano Awwalu? Ta ina? Ta ina tunaninsu zai iya samo Awwalu? Ba shi yaje ya mi™a kansa ba ta tabbata, don idan haka ne a ™ofar dakinta waWannan motocin ´an sanda ya kamata su tsaya ba'a gidan Awwalu ba.

"Sake komawa Sadik, sake komawa yanzun nan ka karanto min lambar karamar motar..."

"Hajiya..." Sadik ya furta muryarsa na shaida fargaba.

"Laifi ba'a manne yake a goshi ba Sadik, babu wanda ya sanka kuma babu wanda zai gane ka, ka koma ka karanto min lambar."

Yadda muryarta ta fito a kausashe tana shaida tsananin tafasa da kuma rudanin da take ciki yasa Sadik haWiye maganar dake bakinsa sannan yace.

"Shikenan, bani minti biyu..."

"Kar ka kashe wayar..."

Ta katse shi da sauri, don bata sani ba idan har kofofin hancinta zasu iya sha™ar iska tsawon lokacin da zata jira shi. Tana jin ™arar takunsa, zuciyarta na bugawa tare dasu har zuwa lokacin da ya isa wani waje da hayaniyar mutane ta shiga kunnenta a lokaci gyda, taji shi yana ratsawa ta cikin mutanen kafin muryarsa ta fito da harafan nambar motar Ma'aruf cikin amon muryarsa da Kilishi ta sani cewa har bayan ranta ba zata taSa mantawa da ita ba. Don a wajenta, a bangarenta wannan lokacin shine mafarin komai, shine mafarin wata rayuwar da a yanzu bata santa ba.

***

*Current Situation...* *( Halin da ake ciki.)*

"Ta farka?"

Sune kalamai na farko da suka fara shiga cikin kanta, sune abinda ta fara ji kuma cikin amon da yake mafifici a wajenta, amon muryar da take tunanin ko a bayan kasa take babu ta yadda za'a yi ta kasa tantamce shi. Ma'aruf. Ma'aruf...
Chapter 58 · 0% Book details