← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 87

Sashe 66

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abu da ya sake tsorata ta kenan don tun sanda tazo gidan ko sau Waya bata taba tashi cikin dare ba, hannayenta na rawa ta samu da kyar ta bata lemo sannan tayi shiru kwance a jikinta, abinda ya hana ta sake tashi kenan saboda tana tsoron idan ta yi motsin da zai tashe ta ba lallai ne ta sake komawa ba, kuma zaman waje Wayan yasa dukkan tarin bugun da zuciyarta ke yi da kuma saka da warwarar dake ranta bacci ya sace ta a cikinsu wanda bata farka ba sai yanzu.

Sai a yanzu da idanunta da kuma zuciyarta suka cika da wani irin nauyi da bata taSa jin sa ba a rayuwarta, ta mi™e da sauri wanda hakan ya farkar da Hamida da kanta ya sauka daga jikinta.

Karfe bakwai da minti uku na safe...

Lokacin da agogo ya nuna a ciki idanunta kenan, ta kalli ko'ina a falon, su kadai ne har yanzu babu Ma'aruf kuma babu alamun wani ya shigo, wani abu ya zarce ta makogwaronta yana ™o™arin zana kalar tashin hankalin da take shirin fuskanta a cikin kirjinta, wajen da ta bar wayarta ta tabbata su Samira zasu gani, idan komai lafiya kamar yadda Baffa yace ya kamata ace su Samira sun kawo mata wayar, ko ma wani ya shigo ya gaya mata dalilin rashin dawowar Ma'aruf din.

Wani tunanin ya daki kwakwalar ta a lokaci guda, me yake shirin faruwa ne? Ko ma me ya faru din? Sai yanzu take ganin me yasa Inna Danejo zata ce a rako su su dawo gida a jiya bayan su Baffan basu iso ba? Idan da gaske ne komai lafiya yake me yasa har yanzu Ma'aruf bai dawo ba? Ko kuma a kawo mata wayarta? Manta ta tayi ma ko kuma me ya faru?

Ba shiri bugun zuciyarta ya karu a lokaci guda, duk wata alama da zata tabbatar mata da cewar ranar yau daban ce ta shiga haskawa a idanunta, hatta yanayin hasken ranar ta ganshi daban da yadda ta saba saninsa a irin wannan lokacin, me yake shirin faruwa ne? Mutuwa akayi? waye ya mutu? Hajiya Kilishi? Idan ita ce me yasa za'a boye mata.... tsaya! Ko dai Ma'aruf ne?

Ba shiri ta Waga kafafunta zuwa daki don ta dauko hijabinta tayi nufi cikin gidan,don duk da hankalinta na neman barin jikinta ta sani ba zata iya fita a haka ba, rigarta bata ko kai gwiwa ba, duka kayan baccinta haka suke, haka take saka su don ta fahimci cewa zata iya raba soyayyar da Ma'aruf yake yi mata da kuma wadda yake yiwa kafafunta daidai.

Sai dai me? Tana motsa kafar tata wani irin jiri ya Webe ta, da kyar ta iya ™okarin tsayawa akan kafafuwanta kafin ta fahimci yunwar da take ji, don siraran yatsunta har rawa suke yi banda jikinta da take jinsa yana komawa kamar fallen takarda, ba shiri ta fasa tayi hanyar kitchen Hamida da ta farka  a lokacin itama ta biyo tana mutsikka ido.

Tana shiga kitchen din ta buWe fridge ta zaro container da ta zuba abincin a ciki, jollof din shinkafa da taliya ne sai tayi sauce din nama da vegetables, bata ko tuna da sauce din ba a yanzu ta nufi tukunyar da tayi girkin da ita jiya, har yanzu tana kan gas din bata wanke ba sakamakon kiran da Samira tayi mata a jiyan cewa an sake shiga da Hajiya Kilishi tiyata.

Sau Waya ta dauraye ta Wora ta akan wuta, ta zuba abincin akan na ciki wanda ya kama, jikinta na rawa ta tsaya tana kallonsa kuma sai zuciyarta ta gaya mata cewa ba zata iya jira ya ™arasa ba don kamar za'a zare numfashinta haka take ji, sai kawai ta kashe wutar  sannan ta dauko tukunyar gabadaya ta zauna a kasa, akan tiles din wajen tasa hannunta ta fara cin abincin a haka tana ci hannunta na rawa bata ko jin sanyin dake jikinsa.

"Mammy zan ci nima.."

Hamida ta fada tana zama itama a gabanta har da tankwashe kafa, ta shiga bata a baki da hannunta, babu wanda ya gama wartsakewa a cikinsu babu wanda yayi ko brush, wani abu da yasa hawayen da bata da tabbacin na meye suka gangangaro kan kumatunta duka biyu a lokaci guda, babu abinda ta gani, babu abinda taji amma ta riga ta sani cewa ba sai wani ya gaya mata ba, ba sai ta jira komai ba, faruwar al'amari irin wannan da kuma yadda jikinta yake mata tun a jiya alama ce ta cewar wani babban al'amarin ya faru... don ko a wasan kwaikwayo ta sani cewa abubuwa basa tafiya daidai idan komai yazo ™arshe.

Tasa Waya baya hannunta ta shiga share hawayen amma kamar ta ziga shi ne sai yawansa ya ™aru, ya cika idanunta taf ya zama bata ko iya ganin Hamidan dake gabanta sai dishi-dishinta tsayuwarta a wajen, sai kawai ta kifa kanta a jikin tukunyar ta fashe da kuka gabaWaya.

Kukan da a cikinsa da kuma tambayoyin Hamida ta tsinci bugun kofar da ake yi daga waje.... Ba shiri ta ajiye tukunyar ta sauko daga saman da take, Kafafunta na sassarfa ta fita daga kitchen ta karasa cikin falon.

Bata san me take jira ba kuma bata san me ta zata ba har sanda hannunta ya bude kofar, kuma siffar mutane biyun dake tsaye a waje, Munaya tare da wata ´ar uwar Hajiya Maimuna da suke kira da Auntyn Sama, kallon da suke mata kadai yasa zuciyarta ta kulle tamau waje guda, komai ya tsaya a cikin kanta cak!

Ba abinda take iya gani sai fuskar Auntyn Saman da take a birkice da kuma kumburarrun idanun Munayan dake shaida cewa har a lokacin kuka take itama... Shikenan! Abinda take hasashe ya faru....

Sai kawai kafafunta suka kasa daukanta ta sulale a lokaci guda zuwa dandaryar ™asan wajen.... Kuma kafin komai ya Wauke daga idanunta tana iya tuna cewa taga fuskar su Munayan akanta suna girgiza kai cike da ™arin tashin hankalin da ya ninku a idanunsu sannan taji muryar Hameeda na kiran sunanta.

***

"Babu wani labari har yanzu..."

Abinda Baba Usman ya faWa kenan a cikin wayar dake kare a kunnensa, ya gyada kansa sau Waya sannan yace.

"Eh, shi DSP Win yanzu yace an samu mutum daya yanzu a can wajen hanyar kura da yace yaga wucewar motar, wai wani mai mashin ne ya dan hada go-slow akan hanya to idan motoci sun taho suna tsayawa amma yace ita motar taba zuwa kawai sai tayi kwana ta biyo ta cikin mutane, yace ta kan kayayyakin sa da yake siyarwa anan bakin hanya tabi ta kai shi yasa har ya iya ganin lambar dake jikinta, shi kansa ma yace sauran kwanansa a gaba ne yasa bata bi ta kansa ba..."

Yayi shiru yana sauraren bayanin da ake yi a cikin wayar kafin ya sake cewa.

"To, yace dai an saka ´ansanda a kan hanya har zuwa Kuran, to amma tunanin da muke yi shine ba'a sani ba idan iya nan suka tsaya, ko kuma sun wuce ma Kuran..."

Ya gyaWa kansa sannan yace.

"Gaskiya ne... Yanzu dai alfarma muke nema ka saka baki a sake bamu wasu ma'aikatan kamar na division biyar haka, babu matsalar payment, za'a basu ko nawa ne."

Ya fadi hakan daidai lokacin da Ishaq ya shigo cikin falon na Baffa.

Kuma ko daga nesa idanunsa kadai zaka kalla ka san cewa duniyarsa ta birkice ne a lokaci guda tsakanin joya da yau, yana cikin tashin hankalin da zai rantse har da ubsngijinsa za'a samu fiye da kutane dubu da zasu zo duniya su gama rayuwarsu har su koma ga mahaliccinsu ba za su taba fuskantar irinsa ba.

Jiya watarana ce da babu daya daga cikinsu da zai yi tunanin zata shafe daga tarihin rayuwar ahalinsu bakiWaya ba ma su kaWai ba.

Faruk ya kira su a waya bayan lokacin da ya kira Ma'aruf yake shaida masa result din da aka samu game da tiyatar da aka yiwa Mamin da suke wajenta tun safe, bai samu wata kwakwarar amsa a wajen Ma'aruf din ba wayar ta katse, bayan kamar minti goma a lokacin da su Baffa suka gama da likitan nan suke shirin komawa gida, a lokacin Faruk ya kira shi da rokon cewa kar ya bari su Baffa su tafi ya kawo su Kamfani a yanzu-yanzu...

Kuma da ™yar ya samu su Baffan suka yarda suka bishi, a cewarsu halin da ake ciki da kuma jiran da mutanen gida suke yi zai tsayar da ko meye a kamfanin, sai da Baba Usman ya saka baki da cewar ya san su Ma'aruf baza su kira su akan wani abu da bashi da muhimmanci ba sannan Baffan ya yarda suka tafi.

Yana tuna yadda suka shiga cikin administrative office Win suka same su komai a barbaje, koina kaca-kaca kafin ma su kai ga fahimtar abinda ke faruwa, kuma shi kansa a yanzu ba zai iya banbance tsakanin bayanin mutumin da suka tarar wa a cikin Office Win mai suna Awwalu wanda ya san su Ma'aruf sun dade suna nema da kuma bayanan muryar Hajiya Kilishi dake cikin wasu tarin CD's da Abdurrahim yayi ta sakawa Waya bayan Waya wanne ya fara ji ba.

Idan wani zai ce ya kwatanta tashin hankalin da ya shiga da kuma mamaki a wannan lokacin ya sani cewa a matsayin sa na lauya shi kansa ba zai iya kare kansa ba,
Balle kuma su Baffan da ya san al'amarin yafi shafarsu akansa, kowannensu kasa magana yayi, baya iya tuna kalma guda da wani ya furta a wannan lokacin banda Baffa da ke maimaita 'Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un' cikin amon muryarsa dake ratsa zuciyarsu ta kowanne bangare, bayan haka kuma sai lokacin da Faruk ya kira ´ansanda a waya da cewar su tafi da Awwalun da ya kammala yiwa su Baffa duk bayanin da zai yi a lokacin.
Chapter 66 · 0% Book details