← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 87

Sashe 4

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don haka ta shiga duba jikin robar kuma gabaWaya babu inda aka rubuta hakan sai ma wasu abubuwa dake shaida mata tsadarsa, har yaushe zata dinga tunawa ne cewa masu kudi ta aura? Don tabbas a cikin wannan auren nata mazajen biyu ne, Kilishi da Ma'aruf sannan matan ma biyu ne ita da Amma, kuma kowa da irin rawar da yake takawa.

Sai kawai ta cije lebbenta da murmushi tana tuno kalaman Hajiya Kilishin na ™arshe kuma mafiya tasirin da suka fi zama a zuciyarta.

_Ba zan hana iya Ma'aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma ba zan dauki wani abu wai shi ciki ba...!_

Bata shaidawa Amma wannan zancen ba don ta yarda daga Kilishin har Amman wannan ba huruminsu bane, wannan ya™inta ne kamar yadda Amma ta gaya mata, kuma ta yarda ba komai Amman zata iya mata ba, don kamar yadda ta fada mata ne ita hanya kawai take nuna mata amma duk wani taimako da zata yiwa kanta yana hannunta, dole ne sai ta tsaya da kafarta ta fuskanci nata yakin, don haka ba zata dorawa Amma wannan nauyin ba.

Kuma Hajiya Kilishi bata isa ta yanke irin wannan kaddarar tata ba, wannan huruminta ne, hakkinta ne, idan ta yarda da Ma'aruf, bata jin akwai wani mutum kuma a gefe da zai gaya mata yadda zata yi da jikinta ko ma abinda zai zama rayuwarsu a gaba.

Wani murmushin ne ya sake subucewa a bakinta da wannan tunanin, wai rayuwarsu? Ma'aruf din da har yanzu bata dan me take ji game dashi ba, ta san dai kawai zuciyarta ta narke jiya da tayi bacci a cikin hannunsa, kuma bata gama bushewa ba sanda ya sake rungume ta a yau, amma a cikin wannan gulbin zata tsinto cewa tana tsananin ganin kwarjini da kuma girmansa, watakila shi yasa take manta komai idan yana gabanta.

Wata doguwar riga ta Wauko (flowy and Maxi) kalarta fara ce, a jikinta anyi mata prints Win lilac flower kalar Pink da kuma Pitch, hannunta ya bude har zuwa rabin nata hannun, kalarta tayi kyau sosai da kuma Waukan hankali, amma ita ba wannan yasa ta dauko ta ba, rashin nauyin ta ne tasa ta zabo ta don shafal take sosai, tana daga cikin kayan da Aunty Safiyya ta bata, kuma ko sanda ta bata Win sai da su Aunty Ma'u suka yi ta Waga ta suna fadin laushi da kuma rashin nauyinta.

Don haka abinda ta tuna kenan a yanzu ta lalubo ta, don tare da nauyin dake zuciyarta dama cikin kanta bata jin zata iya da wata atamfa ko makamancin hakan. Tana da mayafi shi fari ne gabadaya, ta sake taje gashinta ta daure shi sannan ta daura mayafin akanta.

Hannayenta har yanzu rawa suke, amma ta san tunda basu yi komai ba tun sanda tana girkin da tayi da kyar a cikin tarin tunaninta, to yanzu ma babu abinda zai same su.

Bata ko saka slippers din da take yawo dashi a cikin gidan ba ta fita daga Wakin, sanyin tiles din gidan na ratsa fatar ta har ta isa falo, idonta ya kai kan ´ar jar fitilar Tv da ta kama tana tuna mata cewa zata iya kunnawa a yanzu, amma bata hango kallon ko a ™arshen lissafinta na yau, don haka ta juya Kitchen don karasa abinda ke gabanta.

_....ina son Wanwake ma._

Shine abinda ya gaya mata jiya a cikin abincin da yafi so, shikenan sai ya zama saukinta itama, Samirah kawai ta kira a waya tace a taimaka mata da kanwa da kuka, nan da nan kuwa ta gama abinta, dama tana da yaji mai daWi da Samiran ta kawo mata tun kwanaki, ta yanka vegetables a gefe guda don bata sani ba ko yana so, sannan ta hada haddadden zoSonta da ta kusan shanye rabi kafin ta zuba a jug.

Yanzu ma fridge ta buWe ta sake debo shi a kofi da niyyar ta koma Waki ta fito da kayan da ta tara na wanki kafin magriba tayi, kuma ta fito daga kitchen Win daidai lokacin da taji ™arar ™wan™wasa kofar gidan, ™ara guda uku da yatsa daya, don haka ta riga ta san ye duk kuwa da cewar bata ji karar bude gate ba.

Sai kawai ta ajiye kofin hannunta a gefe Tv wata zuciyar ta gaya mata cewar ta kwance mayafin ta yafa shi amma wata zuciyar ta kore hakan kai tsaye.

****

Da wuri ya bar Office yau, don yana yin sallar La'asar ya fito tunda sun riga sun gama dukkan abinda zasu yi na yau, dawowar Baffa a gobe kawai ake jira a gabatar masa da komai kafin su fara fuskantar wasu sababbin ayyukan.

Kuma bayan shigowarsa gida kai tsaye ciki ya nufa, yayi minti goma da kyar a Sangaren Hajiya Maimuna  kafin ya fito ya nufi inda yafi wayo, a falo ya kuwa tadda Mamin ita kadai tana zaune tana waya da wani faffadan murmushi a fuskarta, kuma har ya zauna bata gama ba sai dai ya lura bata ™ara cewa komai ba bayan sauraren da take yi.

Ta ajiye wayar yana tsokanarta cewa Allah yasa kwanýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹ŒŽ‘’“”•–—˜™š›œžŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿgila ta samo musu kafin su gaisa, sunyi hirar shari'ar Hamida dake shirin faruwa a jibi inda ta dage akan cewar kar ya yarda ya mayar musu da ita gwara ya dawo da ita wajensa kamar yadda ta jaddada masa tun farko, kuma haka kurum sai ya samu kansa da amsa mata kawai ba tare da ya baiyana mata irin tsarin da yayi ba.

Daga nan suka shiga hirar wani sabon gidan gona da take son buWewa, tana cewa zata Wora shi a matsayin manajan wajen yana ro™onta ta taimaka ta rufa masa asiri abubuwan dake gabansa sun ishe shi.

"Mami Slides Wina ne zasu haWe dana kaji, sai nazo ina presentation a meeting kawai in buWe kaji suna cin abinci. Baffa will sack me for days."

Dariyar da take ™yal™yale da ita, dariya ce dake fitowa tun daga ™asan zuciyarta, kuma shi kansa ya sani cewa ko tare da Baffa bata irin wannan nishadin balle kuma duk wani wanda zai biyo bayansa, shi daban ne a lissafinta ba sai ya rantse ba ya sani, ya san Mami na kaunarsa da dukkan irin ™aunar da uwa ke yiwa Wanta, wani abu na gaya masa cewa zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da yake zaune a gabanta irin haka, shi yasa a kullum yake addu'ar Allah ya bashi ikon faranta mata a tsawon rayuwar da zaiyi.

Ya baro cikin gidan da wannan farin cikin a zuciyarsa ya iso bangarensu, kuma har zai buWe ™ofar da mukullin dake jikin na motarsa, sai kuma ya fasa kawai ya kwankwasa, sau daya biyu, uku yayin da yake tsaye dab da ™ofar hannayensa harde a kirjinsa. Kuma ba'a wani jima ba, aka murWa handle din a hankali sannan jikin ™ofar yayi baya.

Ba shiri Ma'aruf yaji wani murmushi ya sauka a lebbensa, don duk yadda zuciyarsa ke hassaso masa yadda zai dawo ya ganta, a yanzu ta wuce hakan, a lokaci guda kalolin rigarta dama yadda ta rigar ta zauna a jikinta suka Wauki hankalinsa, yaji wani abu ya motsa a cikin kirjinsa, sai kawai ya cije lebbensa yana murnushin kafin yace.

"Assalamu alaikum."

"Wa'alaikum salam."

Ta amsa a hankali tana sakin hannun ™ofar, ™afarta tayi taku biyu zuwa ciki amma sai ya cigaba da tsaiwa bai shigo ba, kuma har tana kokarin juya ciki jikinta ya bata cewa a tsaye yake don haka ta juyo ta sake kallonsa, yana tsaye a yadda yake, ya harde hannuwansa a ™irji yayin da wayoyinsa da kuma mu™ullin motar da ya rike ya fito ta kowanne gefe, mamaki ya nuna akan fuskarta don haka ta dawo ta tsaya kuma kafin tayi magana sai kawai yace.

"I'm sorry, ina neman wata ne mai suna Amina, ance min anan take, zaki ganta wata ´ar ™arama haka tana da idanu masu kyau, kuma ta iya murmushi."

Ba shiri murmushin ya suSuce a bakin Amina, murmushi da ya fito tun daga zuciyarta saboda da gaske ya bata dariya, yadda yayi da fuskarsa idan tare da wani ne zai rantse cewa da gaske kwantancen yake yi, kuma haka kurum sai taji wani abu a cikin ranta yana wucewa, don haka ta girgiza kanta a hankali tace.

"Bana jin na santa."

"Saboda me?" Muryarsa ta fito tare da godiyar biye masan da tayi.

"Saboda ni kaWai ce Amina anan, kuma ni duk ban kai yadda ka fada ba."

Ta sake faWa a hankali tana murza yatsunta. Ya kalli yatsun nata sannan yace.

"Zaki yi mamaki idan nace miki a yanzu kinfi ™arfin kwatance na ma, you look stunning Masha Allah."

Amon muryarsa na fitowa da zurfi.

Murmushin ta ya ™aru a lokacin da take kallonsa har yanzu da mamaki a fuskar ta, sai  kuma yayi saurin girgiza kansa kamar ya tuna wani abu sannan yace.

"I'm really sorry na manta ban tambaye ki ba idan Aminar da nake nema matar aure ce, kar in kwana a inda ban shirya ba."

Murmushin ta ya sake karuwa kafin ta Waga kanta sau biyu tana cije lebbenta.

"Ya Salam!" Ya faWa yana sakin hannayensa.

"Saurin me kika yi haka? Me yasa zaki yi aure tun yanzu?"

Sai da ta zare idanunta tana dariyar da bata san daga ina take fitowa ba kafin tace.

"Saboda me?"

A lokaci guda ya karaso, ya tako zuwa cikin falon, ya tsaya dab da ita sannan yace.

"Cox I want you, bai kamata ki auri wani ba, ko Allah ya san nine mijinki."

Sai da Amina ta cije lebbenta sannan ta rufe idanunta tana murmushi, kuma kafin ta buWe idon ya sunkuyo daidai gefen fuskarta yace.

"I apologize if this is a little bit forward, but you just look so.... Woww!"

Abinda taji kenan kafin taji ta a cikin hannayensa. Numfashinta ya yanke daga huhunta a lokaci guda, ™afafunta suka karbi hannayenta wajen rawa, zuciyarta ta sake komawa ruwa, ta sake komawa irin duniyar jiya, duniyar da take manta komai sai Ma'aruf kawai da irin abubuwan da yake nuna mata.

Ya tallafi fuskarta kaWan yana sawa ta kalle shi, don ko kaWan ta kasa rufe idanunta ma yanzu, idanunsa cikin nata yace.
Chapter 4 · 0% Book details