← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 87

Sashe 21

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kaWai ce a gidansu kowa yake shiri da ita, kuma tun a wannan lokacin ra'ayinta ya karkata sosai a kaina ta yadda take kyautata min fiye da kima har sai da kowa ya fahimci cewa she's interested in me. To sai wani abu ya faru a wannan lokacin da ya zama mafarin ciwo na, rayuwata ta canja gabadaya ta yadda na tashi daga yadda kowa ya sani zuwa wani abun daban.

Amma duk da haka bayan mun kammala karatu sai ta dage akan bakanta, and I've no right da zan iya cewa A'a, saboda ko Baffa a lokacin ya matsa da cewar inyi aure kuma ni ba wannan ne a gabana ba, ina wani bincike ne da nake ganin cewa zan iya gama shi a wancan lokacin saboda haka above all the girls a sannan sai Rukayya tafi kowa zama wadda ya dace na aura.

Bayan auren mu, da shekara biyu, sai zaman yazo karshe, lokacin Hamida tana Baby...."

Yayi shiru yana shafa hannunta akan kofin kafin ya cigaba.

"Na yarda na bar yarinyar a wajenta ne a lokacin saboda karama ce kuma ko baka haka ba dole a wajenta ya kamata ta zauna dama, sai dai duk da haka munyi wani sharadi a lokaci da zai bani damar Waukarta bayan na kammala abubuwan gabana.

Lokacin da ake shirin fara aurenmu dake, lokacin naga Hamida a wani waje da bai dace ba tare da wata Christian wai ita take kula da ita, da na dauke ta na kai ta wani creche ne tunda ba zan iya kawo ta gida a lokacin ba kuma a can ta zauna har bayan kin zo gidan nan.

Mami tace in dawo da ita nan amma banyi hakan ba saboda nafi son komai ya tafi a hankali, don ni dake ba mu gama fahimtar juna ba a lokacin, so I have my plans yadda komai zai tafi daidai amma sai gidan su Rukayyan suka kasa jira na suka kai zancen kara kotu wanda a jiyan ya kamata inje amma ban samu zuwa ba, Ishaq yaje kuma basu yarinyar kamar yadda muka san dama hakan ce zata faru.

Amma kawo ta da suka yi a yau ban san dashi ba Amina, Dukkaninmu babu wanda ya san dalilin da yasa suka yi hakan, abu daya kawai na sani shine, Hamida tazo wajena kenan Amina ba zata taba komawa hannunsu ba ko me zasu yi a duniyar nan kuwa."

Yayi shiru yana kallon yanayin fuskarta, yadda idanunta ke nuna cewa kwakwalwarta tana daukan dukkan maganganunsa a wani ma'auni da ya kasa tantance shi, don haka sai kawai ya karasa jawo ta gabansa a hankali, har yanzu kofin na rike a hannunsu su duka biyun. Kuma saura kadan goshinsa ya hadu da nata yace.

"Doll, zaki taya ni mu rike ta?"

Muryarsa a hankali ta fito, da wani amo da kamar auna shi ne ya tabbatar zai kassara kowanne abu mai kwari a jikinta da kuma cikin kanta, numfashinta kawai take ji yana fitowa da saurin da yafi daidai, kuma ta san ya fahimci hakan amna da yake a kowanne yanayi Ma'aruf shi din ne dai sai ji tayi yace.

"Idan tunani kike zata hana mu wani abin Doll kar ki damu, I will always find a way, na miki alkawari."

Bata san lokacin da ta ture shi baya da hannu daya sannan ta mi™e tsaye, ya rike kofin data bar masa, ya kalle ta da murmurshi a fuskarsa lokacin da wayarsa ta sake kara.

Ta juyo ta kalle shi kamar zata ce wani abin game da wayar, ya daga mata gira Waya yana kai kofin bakinsa, sai kawai ta kasa cewa komai din ta juya zuwa wajen wardrobe Winta.

"B, yanzun nan Waya daga cikin mutanen RTL ya sake kira, ya bamu details akan mutumin nan da yazo ya karbi kudin."

Abinda Faruk ya faWa kenan, bayanan layi biyu da a cikin sakanni biyu kawai da suka da suka yi ™o™arin goge duk wani dukkan hargitsin da ya tashi dashi a safiyar yau, bakinsa ya furta hamdalar da bai san lokacin da taji bakin nasa ba.

Yaji zuciyarsa na washewa da yakinin fawwalawa Allah al'amarinsa, a yau kaWai ya tashi da matsaloli har guda biyu wanda suke jigo kuma manya-manya a rayuwarsa, amma sai gashi tun kafin ya kai breakfast bakinsa ya fara samun rabi na waWannan matsalolin sun fara gushewa.

Idonsa ya sauka akan Amina data dauko wani farin abu dan karami ta karaso kan gadon daga daya gefen tana ™o™arin kara rufawa Hamida dake motsi kamar sanyin fankar dakin ne ke damunta.

"Alhmdlilah."

Ya furta a hankali yana cigaba da kallon halittu biyun da yake ganin sun zama wani jigo naduniyarsa a yanzu.

Abinda bai sani ba shine, akwai wasu lokuta da bawa ke kaiwa gabar da karshen wahalhalunsa a duniya ke karewa, akwai gabar da mutum ke zuwa inda komai zai tsaya, komai din da ya danganci dukkan wani kunci da hargitsin rayuwar da ya fuskanta, akwai gabar da mutum ke girbe tarin hakurinsa da ya shuka, akwai gabar da mutum ke fahimtar cewa Allah na karbar dukkan addu'o'in sa, sannan akwai gabar da mutum ke iya canja karin maganar bahaushe da cewar...

Rana dubu ta barawo... Rana dubu ma ta mai kaya!

***

_Ina ga mun tatttaro dukkan ksn matsalar mu a yanzu, so wa shiryawa fara samun revenge?_

_Waya shiryawa ramuwar gayya da ake cewa tafi ta gayyar zafi?_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:52 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*07*

~~~~~~

_She didn't love easily, it took alot for her to fall, but when she loved it was with such intensity it could be felt from a mile away, it shook the earth and made the ocean roar. And when he felt it,it made him questioned if he'd ever known love at all... - Unknown._

**

"Mammy bata ce wajenki zan zo ba..."

Hamida ta faWa tana kallon Amina dake gabanta, tashinta kenan daga bacci kuma sai da Aminan ta sha faman tambaya kala-kala kafin ta samu a yanzu tayi maganar. Maganar da a lokaci guda tasa Amina yin murmushi don in har ce wani abu to komai zai zo da sauki, saboda haka ta gyada kanta a hankali tana murmushin sannan tace.

"Na sani, wajen Daddy tace zaki zo ko?"

Sai ta gyaWa kanta alamun ta ™ara warewa daga baccin da ta tashi.

"Daddy ya fita yanzu Hamida, amma zai dawo anjima kadan kinji."

Bata ce komai ba ta cigaba da kallonta kawai, sai tace.

"Zaki ci abinci kafin ya dawo?"

Yanayin idonta ya canja da cewar maganar tayi tasiri akanta amma duk da haja sai da taji ta sake tambaya tukunna sannan ta daga kanta a hankali.

"To taso muje a wanke fuska tukunna tunda daga bacci kika tashi ko?"

Wannan karon a lokaci daya ta gyada kai sannan ta miko mata duka hannayenta biyu alamun ta dauke ta, Amina ta sake yin murmushi ganin hakan kafin ta mika hannu itama ta Wauke ta a jikinta.

Kamshin turaren ta mai daWi ya shiga hancinta a take, daga gani tabbas tana samun kulawa don haka tunanin dalilin da yasa suka kawo ta kamar yadda su Ma'aryf keyi ya Warsu a ranta, suka shiga toilet din dakin har a lokacin kallonta kawai Hamida take yi.

Ta ajiye ta a kasa tana fadin bari adebo ruwan kafin  ta samo dauko kofin dibam ruwa ta taro mai dumi kadan daga fanfon. Ta tsugunna a gabanta har ysnzu tana murmushi tace.

"Muyi wasan ruwa?"

Ga mamakinta sai ta girgiza kai.

"Mariya tace babu kyau wasan ruwa."

Sai murmushinta ya karu tana daga kai tace.

"Good, ashe kina da ™awa mai hankali."

"Mariya tsohuwa ce, ba ™awata bace"

Sai da Amina ta dan tsaya kafin tace.

"Babba ce?"

Ta gyda kai tana cigaba da kallonta. Sai ta girgiza kanta.

"Ba sunanta Mariya ba ai Hamida."

Alamun mamaki da kuma tsoron laifi suka nuna fuskarta kafin tace.

"To ai haka su Mammy ke ce mata."

Amina ta sake girgiza kanta.

"Su Mami sun manta ne amma Mama Mariya sunanta, watakila ma idan kinyi bacci suna fada baki sani bane kawai."

Bata ce komai ba, sai ta kara yin wani murmushin da tace.

"Tana da ´an yara ksmar kibharda mnya ma kamar su Mammmy da ni kinga ai ta zana Mama ko?"

Sai ta gyada kanta a hankali alamun ta gane amma bata ce komai ba, Amina tayi murmushi ta wanke mata fuskar sannan suka taho kitchen, acan yna ta dinga janta da ´ar hira a hankali har sai da ta fahimci ta dan fara sakewa da ita, duk da cewa tana ta tambayar inda Ma'aruf ya tafi da kuma lokacin dawowarsa, har Surayya da ta kawo ta ta tambaya tace mata itama zata dawo.

Ma'aruf ya fita a Wazu ne bayan yasa Faruk ya turo masa da direba yazo ya dauke shi da motar Oficce kuma duk kawaicinta sai da taui kokarin nuna masa cewa bai dace ya fitan ba saboda yanayin jikinsa, amma ya gaya mata cewar fitar tasa ta zama dole ne don abinda Faruk din ya samo, wani abu ne da a yadda yake jin kansa ya san ba zai iya barin kansa bai fita ba, sannan kuma du Baffa ma zasu dawo a yau, wanda ka'ida duk sanda suka yi tafiya doguwa irin wannan da sun dawo a kamfanin suke fara sauka tukunna kafin gida.

Don haka babu yadda ta iya dashi haka ya shirya ya fitan, bayan ya roke ta da Allah cewar tayi masa tuwo da miyar wake, don haka aikin da take tayi kenan yayin da Hamida ke zaune tana cin abincinta da kuma tea din da ta hada mata.

"Kema Daddyna daddynki ne?"

Taji ta tambaya lokacin da take kokarin wanke naman da ta fito dashi daga fridge, ta juyo ta kalle ta da murmurshi sannann ta Waga mata kai, amma sai Hamidan ta kara haWe ranta.

"Ni bana son inyi sharing Daddyna da ke."

Murmushin ta ya karu sosai don maganar ta bata dariya, sai ta gyada ksnta sannan tace.
Chapter 21 · 0% Book details