← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 87

Sashe 15

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samira ce ta gaya masa cewar Amina ce ta sanar dasu an dawo gida don haka tun da rana kafin ya farka suka zo har dasu Salma, Shukra da Safiyya wanda suka zo a ranar, ga dadin dadawa Inna Danejo da itama Mama Rabi ta rako ta tun daga cikin gidan har nan.

Tana zaune daga gefensa inda aka kwantar dashi a falon tana ta karanto tarin addu'o'i daga cikin carbin ta take ja tana gaya masa cewar rubutu zata sa ayi masa na Alkur'ani gabaWaya don  ita ta gaji da yawan maganin asibitin da har yau bata ga amfaninsa ba.

Kuma tun da Ma'aruf yake a rayuwarsa, tun daga lokacin da ya sami ciwon nan, idan har bashi da lafiya ya sani cewar sai dai ya farka ya ganshi a London asibiti ko kuma tare da Ishaq a gefensa.

Ko lokacin da yana tare da Rukayya baya bude idonsa ya ganshi a gida kuma ko shi a baya bai taba ganin wani abu game da hakan ba, don idan ba zai manta ba a cikin hira Mami tasha gaya masa cewar hakan shine daidai, bai kamata ya dinga mu'amalantar kowa ba har sai yanayinsa ya sauko ya daidaita.

Shi yasa a karo na farko da ya farka a yanzu yaga mutane zagaye dashi sai yake jin wani iri a zuciyarsa, wani irin yanayi da bai san dame zai fassara shi ba, kallonsu kawai yake yi tun bayan da ya bude idanun nasa, kowanne da murmushi a fuskarsa suna tambayar lafiyarsa da kuma yadda yake ji.

"Ya MB kace min ka warke dan Allah, ni ban san haka ciwon ka yake ba wallahi, ban taba ganinka a haka ba."

Shukra ta fada tana gyara glasses din dake fuskarta tana kallonsa. Kuma sunan da ta kira shi dashi ya tuna masa da dadewar da yayi bai gansu ba tun bayan aurensu, ya san dai kowaccensu ta kira shi sau daya sun gaisa amma bai kara jinsu ba bayan hakan, dukkaninsu sun canja, musamman Safiyya da tayi wata irin kiba a watanni biyu kawai tana gaya masa cewar da wuri zasu tsufar dashi idan ska kalle su aka cewa su kannensa ne.

Kuma maimakon ya bata amsar abinda ta tambaya sai kawai yace.

"Ya project work Win naki kuwa Kin gama?"

"This is your answer ya warke kenan, don ni na tabbata da yace miki da sauki to wallahi Yaya bai warke ba."

Cewar Salma tana karasowa rike da kwanon furar da Inna Danejo tasa taje har bangarenta ta dauko shi. ta zubo wani potate Win dankali a ciki daga kitchen, tana karasowar kuwa Inna Danejo dake gefensa ta karba tana fadin.

"Muhammadu juyo nan kasha wannan, na gaya maka ni ban yarda da wannan she*gen ruwan da ake sawa ba ace wai shima abinci ne, gashi nan tunda ka farka ai kake ta shan ruwa da yana aiki ai ko shi ba zaka nema ba."

Ya juyo ya kalleta, ta debo abincin da niyyar bashi, sai kawai ya girgiza kansa yace.

"Ni ba haka matata take bani abinci ba."

Su Salma suka kyalkyake da dariya ba shiri yayin da kafin Inna Danejo ta kai karshen salatin ta Surayya ta shigo tana fadin cewar ga wani likitan nan ya karaso da sakon cewar Baffa ne ya turo shi, don a dazu bayan farkawarsa sun yi waya da Baffan har ma da Baba Usman suna tambayar yaya jikin nasa, kuma a cikin muryarsu kaWai ya fahimci su ma sunji dadin yadda wannan karon ciwon nasa bai tsawaita ba.

Inna Danejo ta ajiye farantin hannunta tana fadin ace masa ya shigo, Ma'aruf ya juyo yana ce mata ta bashi furar tace ai kuma yayi wa kansa kenan ya zauna da yunwar cikinsa idan matar tasa tazo ta bashi.

A lokacin ne kuma yadso ya tambayi inda Aminan take don tun bayan lokacin da ya farka sau daya ya ganta sanda da ta kawo masa ruwan farko da ya tambaya, amma kafin ya bude baki Shukra ta matso tana dariya ta Wauki plate din tana faWin ita zata bashi.

A lokacin ne kuma Zahra da Sahla da suka fito daga hanyar koridon dakunan gidan.

"Ina Aunty Amina?"

Suka tambaya a tare muryarsu na shaida murna.

"Me kuka je ýÿÿÿ

!"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~kuka yi mata a daki?"

Safiyya ce mai tambayar tana kallon hannun Sahla data boye a baya.

"Babu komai, kawai tambayarta zamu yi wani abu."

Salma ta kalle su tace.

"Makaryatan banza ai idan bincike ne kun iya shi, na gaya muku duk ranar da zaku zo gidana walkahi ku gaya min kulle koina zanyi ku zauna a falo.

Munaya dake zaune a gefe ta kalle ta.

"Har yanzu baki san abinda ke tsakaninku da Samirah bane, shi yasa kike ganin na wadannan yaran wani abu suke yi."

Da sauri Salman ta juyo tana rokonta ta gaya mata abinda Samiran ta daukar mata amma tace ita ba zata fada ba ba,  ta bari duk ranar da Allah ya tashi tona mata asiri zata gani da kanta yayin da Inna Danejo ke fadan hada husuma babu kyau.

"Wai ina Samiran ne ma, ni tazo in bata sakon cupcakes."

Safiyya ta tambaya daidai lokacin da Surayya ta shigo tare dasu Faruk da kuma likitan nan, hannunta na dauke wani dan karamin yaro da a lokaci guda Ma'aruf ya gane cewar Aarif ne Wan gidan Faruk, kuma bai gama tunanin ba Shaida natar Faruk din ta shigo biye da sauran ´a´ansu biyu mace da namiji.

"Yaya, su Aunty Shaida ne duka zo."

Cewar Surayyan kasancewar dama ita tun da ta san Shaidar don yayar ™awarta ce.

Kowa ya amsa sallamar su da fara'a yayin da Munaya ta taso a lokaci guda tana  kokarin daukar Aarif din dake ta mika hannu zai koma wajen mamansa alamun kyuiya yake yi.

Shahida ta karaso har gaban Inna Danejo tana gaishe ta yayin da likitan nan ke kokarin cire allurar drip din daje hannun Ma'aruf din, shima ta gaishe shi sannan ta gaya masa cewa Faruq din yana waje tare da Ishaq wanda shima ya karaso a lokacin.

Da haka ta juya wajensu Safiyya tana gaishe su da tambayar Yaya mai jiki. Tambayar da tasa sai a lokacin hankalin kowa ya lura cewar Amina bata wajen kuma kowa ya tabbatar da cewar bai ga lokacin da ta fita ba.

Sai dai kafin hakan ya kai ga nisa, kofar falon ta bude, kuma Aminan da ake nema ta shigo a lokacin tare da Samiran da suka fita tare, sai dai duk wanda ke Wakin basu yake kallo a lokacin ba.

Wadda ke zaune akan kujerar da Samira ta turo zuwa cikin falon a hankali ce... Hajiya Maimuna.

Shiru ne ya ratsa ilahirin falon a lokaci guda kafin kowannesu ya rufe da kiran sunanta, hatta Inna Danejo sai da tayi murmushi tana kallonta, don a tarin jama'ar gidan kaf, kowa ya san kawaici irin na Hajiya Maimuna, ba karamin kokari Amina da Samira suka yi na sawa tazo ba, tunda tun rana ta san inda dukkaninsu suka taho amna bata ce zata zo ba.

Ma'aruf ya kasa rufe bakinsa a lokacin da yake kallon Hajiya Maimunan dake Samirah ke turota tana karasowa gabansa. Keken tayar ya hawo har kan carpet din ta iso daidai gabansa da kuma Inna Danejo wadda ke fadin taso Baffa yana gari yau yaga Maimuna a gidan Ma'aruf, don ko sanda yana tare da Rukayya har suka rabu bata taba takawa gidansa ba.

A lokaci guda wani abu kamar kwallar da bai san dalilinta ba ta cika idanunsa lokacin da  Hajiya Maimunan ta gama gaishe da Inna Danejo ta juyo tana tambayar yaya jikin nasa, bai ma san da wadanne irin kalamai ya amsawa tambayarta ba, ya san kawai a wannan lokacin idanunsa na kallon Amina ne dake can tsaye a baya da murmushi a fuskarta tana gaisawa da Shahida tana kuma kokarin daukar Aarif da ya gudo daga hannun su Munaya ya koma wajen Shahidan.

Zuciyarsa yaji tana gaya masa cewa ko da iya wannan alkhairin nata na yau kaWai, zai kyautata duniyarta da dukkan iyawarsa.

***

*˜arfe tara da rabi na dare.*

Kowa ya tafi a lokacin, hatta su Ishaq bayan ya takura musu sun shaida masa dukkan abubuwan da yayi missing dinsu a ranar, farko shine shari'ar Hamida da shi kansa ya manta da ita a yau,Ishaq din ya gaya masa cewar yaje ya dauko yarinyar ya tafi da ita kotun, kuma duk iya kokarinsa a gaban Alkalin, ba'a je koina ba alkalin ya yanke hukunci da cewar yarinyar ta koma wajen mahaifiyarta idan yaso tunda ya bada uzurin mahaifin nata bashi da lafiya, ya yanke hukunci cewar duk sanda ya warke zai iya sake shigar da kara sai a zauna a sake tattaunawa.

Na biyu kuma shine zancen haduwarsa da mutanen RTL din nan, Faruq ya gaya masa cewar babu yadda baiyi yayi contacting mutanen ba amma ya kasa samun su kuma suma basu ce masa komai ba. Sannan Ishaq ya shaida masa cewayasa snyi deactivating gabaWaya cards dinsa da aka Wauke kuma barayin basu sami danar fitar da komai ba.

Har suka tafi Faruk yana ta kokarin ya kwantar da hankalinsa akan cewar ya san ba wani issue ne babba ba amma har suka kammala zancen suka tafi jikinsa bai bashi haka ba, kawai ya ajiye zancen ne a gefe sanin cewar idan ya saka a ransa tabbas abin zai hadu ya dame shi tunda wancan case din ma har yanzu basu karasa shi ba, don haka ya hakura ya barwa karin samun saukinsa komai.

A yanzu gidan daga shi sai Amina ne, kowa ya tafi, su Salma tare suka koma cikin gida tare dasu Inna kuma ya san zuwa yanzu ma duk sun tafi. Kuma Hajiya Maimuna da har ta tafi fara'ar fuskarta bata Soyowa, kuma yana jin sanda taje ta addu'a da sawa Amina albarka daga can bakin kofa inda suke sallama.

Hatta Faruk sai bayan da suka yi sallar Isha ma sannan suka tafi don suna ta hira tare da Ishaq, yayin da Amina ke tare da Shahida a kitchen don dukkaninsu basu tafi ba sai bayan da suka ci abincin dare, har Samira ta dawo daukan wayarta da ta manta tana ta korafin me yasa basu kirata ta taya su ba.
Chapter 15 · 0% Book details