Sashe 74
Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Su waWanda muka tarar anan sun ce ai tun kafin ma su san wannnan al'amarin aka kawo ta asibitin. Komai ya rikice ne kawai Ma'u don ita kanta Tantin da muka yi waya ban iya gaya mata wani abu ba tunda har yanzu su ma babu wanda ya gama sanin abinda ake ciki, Munayan tace min sun san dai an tafi da ita Kilshin wajen ´ansanda daga asibitin nan, shi kuma an kwantar dashi."
Aunty Ma'u ta gyada kanta.
"Irin wannan sai an kwana biyu dama za'a san me ake ciki tunda su kansu yanzu hankalinsu ba'a jikinsu yake ba."
Amma tace.
"Duk sun taho ma, har da ´arta daya Sameerah, suran ne suke can gida tare da wasu yanuwansu don Mama Rabin da na hadu da ita tace gidan ya zama kamar na makoki daga safiya zuwa yau..."
"Allah ya kyauta, ni wallahi banyi mamaki ba Amma, a wannan zamanin jama'ar da suke da fuska biyu wajen cutar al'umma suna da yawa, kuma ba ma wai sai a wani babban abu ba, wani ko ba zai samu komai ba idan ya nuna baya kaunar ka a bayan idonka zai ji daWi, kawai dai ita nata yayi yawa ne, cuta da kuma zaluntar ciki tafi karfin tunanin mutane ire-irenta da yawa.."
Amma ta yi shiru kafin tace.
"Zancen babu daWin ji Ma'u, iya wanda ya fito a yanzu kaWai balle kuma abinda zai fito daga baya, ´an uwanta ma wasu basu yarda ba, abin ne kamar mafarki, kamar labari... Sai dai addu'a kawai."
"Allah ya kyauta, Allah ya basu hakurin Waukar hakan ya bi musu hakkinsu, sai a godewa Allah don watakila da lokaci ya ja, zata iya aikata fiye da wanda tayi ma a baya."
"Wannan haka yake, don al'amarin yafi karfin tunaninki, Allah ya bata fikira da kuma dabarar da ta bari shaidan ya karbi linzaminsu."
˜walla ta cika idanun Amina a lokacin tana hana mata ganinsu bakiWaya sannan tunaninta ya cilla kan maganganunsu tan son fahimtar da kanta abinda bata gane ba... su waye suka yi hatsari? Wanda take nufi an kawo asibitin Ma'aruf ne? Abinda su Munaya zasu gaya mata kenan? Abinda ta kasa tsayawa ta ji kenan? An kama wani? Hajiya Kilishi ce? To ta yaya hatsarin ya faru? Komai yazo ™arshe kenan? A wane hali su Samirah ke ciki? Baffa... Sauran mutanen gidan.... Ma'aruf ma...
Wadannan tambayoyin su suka yi ta haskawa a cikin kanta har lokacin da taji Amman tace.
"Bari na sake lekawa can inda aka kwantar dashi naga me ake ciki dama jiran ™arasowar ku nake kar a bar ta ita kaWai."
Ta faWi hakan sannan ta mi™e tsaye ta juya kan wata kujera daga can jikin bango ta ajiye yarinyar.
Amina bata ga sanda ta fita ba ta dai ji ™arar rufewar ™ofar da kuma muryar Aunty Ma'un bayan nan tana kwatance wa su Tantin da suka kira ta a waya, don haka bata bude idanunta ba sai a daidai lokacin da ta kai ™arshe a wayar wanda hakan yasa tana bude idon ta kula da ita
"Alhamdlilah, Amina kin tashi? Sannu..."
Ta faWa kai tsaye tana ™arasowa gaban gadon.
"Sannu Amina, sannu...."
Ta sake faWa tana rike hannunta wanda ba'a saka masa allurar drip Win da take ji a jikinta ba, sai tayi kokarin mi™ewa a hankali tana kama hannun Auntyn Ma'un sosai.
"Sannu..."
Ta ™ara faWa tana ri™e ta.
Bakinta a rabe yake kaWan amma bata ce komai ba... Wani abu ya wuce ta ma™ogwaronta tana ™o™arin gyara zamanta.
"Bari in zubo miki abinci ki iara jin kargin jikinki.."
Aunty Ma'u ta sake faWa tana ™o™arin juyawa, sai tayi saurin kamo hannunta da sauri tana kallon ta.
"Aunty me ya faru? Su waye suka yi hatsari?"
Muryarta ta fito a bushe kamar yadda lebbenta yake. Aunty Ma'u ta girgiza kanta.
"Bari ki fara cin wani abu Amina..."
"Aunty dan Allah..."
Ta katse ta tun kafin ta ™arasa. Tana jin yadda wani abu kamar kwalla na kokarin cika idanunta yayin da bugun zuciyarta ke dokawa ta yadda bata tunanin ko yawu zai iya wucewa ta makogwaron nata.
Sai kawai Aunty Ma'un ta dawo ta zauna a gefen gadon ba tare da ta saki hannunta ba sannan tana kalonta sosai tace.
"Ma'aruf ne yayi hatsari tare da Hajiya Kilishi Amina, amma ba wani abu ne ya same shi ba, jikin nasa da sauki, kar ki daga hankalinki sun ce babu abinda ya same shi... Ki samu ki ci wani abu yanzu, Amma tace za'a iya sallamar ki a yau, sai mu je ki ganshi...."
Abinda ta fada mata kenan, abinda ta rude ta dashi har ta kwantar da hankalinta ta iya cin wani abu a abincin da ta kawo ba tare da ta san cewa babu zance Waya daga da yake gaskiya ba a duk abinda ta fada.
Don bayan Amma ta dawo har kuma an kira likita ya sallame ta, tun daga hanyar zuwa wajen ta fahimci cewar al'amarin yafi karfin yadda ta lissafa shi... Babu kowa a wajen lokacin da suka isa, su Hajiya Maimuna da duk dimbin jama'ar da suka taru a wajen lokacin da aka kawo shi duk sun koma gida, can gidan da a yanzu ya koma kamar gidan zaman makoki saboda ™arancin tashin hankalin da ya wanzu a cikinsa.
Don haka ita kadai aka bari ta shiga wajen yayin da su Amma suka tsaya daga waje... Kuma Amma ce ma ta danyi mata bayanin abinda ya same da taji daga wajen su Hajiya Maimuna lokacin da tazo ta same su... Likitocin sun ce bugun zuciyarsa baya tafiya daidai, sannan ya farka sau biyu amma duka ba'a haiyacinsa yake ba... Sannan bayan haka numfashinsa ma baya iya fita daidai (Respiratory insufficiency).
Bata san tsawon mintunan da ta shafe tsaye a wajen ba,ta san dai kawai lokaci mai tsawo ya tafi zuciyarta na ta sake-sake da tunanin ayyana halin da Ma'aruf ko kuma sauran ahalin gidn ke ciki kafin wata Nurse ta gaya mata cewa su Amman dake waje suna jiranta.
˜afafunta suka dauke ta zuwa waje, dogon koridon asibitin inda t barsu a zaune, dogon hijabi ne a jikinta na Maryam wanda Baba ya dawo daga baya ya kawo mata, ta fita daidai lokacin da su Amman ke gisawa da Ishaq da kuma Abdurrahim wanda suka ™araso a lokacin, kuma kallon Ishaq din kawai tayi taji kwalla ta cika idanunta don haka kanta a sunkuye ta karaso gabansu sanda suka shiga gaishe ta da jiki shi da Abdurrahim Win da kawai Wago mata hannu yayi.
Ta share hawayenta da bayan hannu sanda Amma ke gaya musu cewa ta kira su Hajiya Maimuna babu wanda ya Waga idan yaje yace musu zasu tafi da ita gida zuwa jibi don ta kara jin daWin jikinta tunda Hamida ma na can tare dasu Maryam, Ishaq Win ya amsa amma ko daga muryarsa kaWai Amina ta san cewar har yanzu ba'a haiyacinsa yake sosai ba, tashin hankalin da shi da kuma zagayen al'ummar dake gefensa ke ciki ya isa ya sa shi a kowanne irin hali.
Kowanne irin halin da mutum guda daya yayi sandinsa ga tarin mutnen da a yanzu ita kanta bata san adadinsu ba....
Kilishi....!
****
Tana zaune akan kujerar da teburi ya raba ta da wadda Wansandan dake kallonta ke zaune.
"Hajiya gwara ki buWe baki kiyi bayani kawai, komai yazo karshe, mun kama duk wani wanda kike mu'amala dashi a harkar ki, hatta sabon yaron ki Sadik Awwalu yayi mana kwatance munjeun taho dashi, sannan mun kama likitan da kika hada baki dashi a asibiti ma da cewar kin makance, so ki bude baki ki yarda da laifinki, Shari'a sabanin hankali ce da za'a iya yi miki rangwame, baki da kowa kuma baki da komai a yanzu, don bana tunanin koa cikin iyalanki ko kuma yanuwanki akwai mai bin goyon bayan ki a yanzu.... Zai fi kyau ki sallama ki saukaka mana aiki Hajiya..."
Dan sandan yayi dukkan wannan bayanin yana kallon Hajiya Kilishi, yana kallon fuskarta da take manne da baneji a wajaje da yawa da kuma karyayyen hannunta wanda aka sakale shi ta wuya bayan anyi mata gyara, idanunta a tsaye suke cak!
A tsaye tana kallonsa, tsawon sakan Waya biyu, uku... Kafin ya mayar da kansa kan file din dake bude a gabansa wanda akan farar takardar dake kai, jerin laifukan da ake zarginta dasu ne wanda tun farkon suka rubuta bayan an tabbatar da kama ta da kwayoyin nan da kuma wanda a yanzu suka ™ara samu daga bakin yanuwanta bayan hatsarin da ta samu na biyu.
Baki da kowa kuma baki da komai...!
Sune kalaman dake maimaitawa a cikin kwakwalar Kilishi, suk sae dawowa suna komawa baya a lokacin... Tun bayan lokacin da Ma'aruf ya fitar da ita daga asibitin nan, tun daga lokacin tunaninta ya tsaya, komai ya faru ne a idanunta kamar tatsuniya, kamar wani mummunan labarin dake faruwa a cikin mafarkin yaro, bata gama warware zaren daya kulle ta a cikin al'amarin cewa yansanda na jire da ita suna nemanta ba, batagama lissafa hanyar mafitar ta da ta fara budewa ba,bata yi komai ba,tana cikin zagaye guda daya nesa kuma ga abinda zata ya kira da tashin hankalin duniya da kuma lahira ya riske ta.
Jiya rana ce da bata taSa tunanin tunanin Allah zai haiccce ta ba a duniyar nan, a dukkan tsare-tsare da kuma lissafin da a tsawon rayuwarta bata taSa hangen irin abinda ta gani ba a jiya, tana tsara komai kuma komai din yana tafiya daidai, kawarta Salamatu ce ma kawai kan tuna mata da cewar a duniya take ba'a aljanna ba cewar wani abun zai iya zuwa mata a karkace, amma ko yazo din, tana daga kwance take sa hannun guda ta gyara shi.
Alah ya bata tarin nasarori a rayuwar nan, bata jin akwai abinda ta taba zanawa zuciyarta da bai faru ba, bata jin ta taba ko da hasashen manufarta ne kuma hakan bai kasance ba, to dan me yasa sai a yanzu da rana tsaka kawa komai zai gargitse mata kuma ta yarda?