Sashe 5
Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"You are making my world so much more beautiful Amina."
(Kina kara ™awata duniyata Amina.)
Shikenan! Sai komai a cikin kan Amina ya sake rushewa, kalaman Hajiya Kilishi har ma dana Amma dake kokawar mi™ewa, dukkan wani abu mai hankali a cikin kanta ya shiga gaya mata cewar da gaske ne ba zata iya taba lafiyar Ma'aruf ba!
*****
A cikin dakin, a cikin wayar, muryar Hajiya Kilishi ta ratsa da tsananin ya™inin dake fitowa daga zuciyarta.
"Mahaifinta shine a lissafi Awwalu, munyi wata ya shaida min cewa sun dawo Wazu, don haka gobe zai fita aiki ina so ka fara bibiyarsa tun daga safiya, duk inda zaije ka kasance tare dashi kuma a shirye, wa'adin lokacin zuwa yamma ne kamar na yaron nan. Idan har ban sami abinda nake so zuwa sannan ba, zaka ga umarni na."
Daga cikin wayar Awwalu yayi dariya mai cike da mamaki yace.
"Mutumin nan fa shine Wanuwanki Kilishi, ina laifin ki sake taSa wani daga cikin ´anuwan nata kawai? kuma shi bashi da wata matsala ma naga, let the man be! Ki duba iyalinsa ki kyale shi."
Ko bai ganta ba ya san ranta a hafe yake sanda tace.
"Tun yaushe muka fara la'akari da wani abu a cikin lamuran mu Awwalu? Ka amsa min kawai, bana bu™atar dogon surutu."
Sai ya sake kyalkyalewa da wata dariya mai armashi irin tasa sannan yace.
"An gama Hajiya, umarninki shine abin aikatawa ta!"
**
_Ku gaya min cewa Amina tana shirin kaimu ta baro..._
_Ko kuma laifin na Ma'aruf ne?_
_Ga dai mafita tiryan-tiryan Amma ta fitar, amma kamar Amina kuma kuna ganin cewa da matsala?_
_To wace matsalar kuka zaba?_
_Ta Amma dake cikin mafitar?_
_Ko kuma ta Kilishi da zata biyo baya?_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:49 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*02*
~~~~~~~
_The act of love is Confession._ _- Unknown_
**
*Shekaru Goma da suka wuce.*
*˜arfe takwas na safiya.*
A bakin titi ne, daidai bayan dogon banki wajen da Babu mutane sosai musamman a safiya irin haks, motar da Hajiya Kilishi da kuma Awwalu take tana daka fake a gefen titi an zuge duka gilasanta da bakin tint mai duhun gaske, don musamman don wannan fitar Hajiya Kilishin tace da Awwalu yaje ya saka tint Win.
A cikin motar, Kilishin taja tsaki tana kallon agogon tsakiyar dashboard kafin tace.
"Mutanen nan sun fara vata mana lokaci Awwalu, saninka ne fa ko Baffa bai san na fito ba."
Awwalun dake gaba mazaunin direba ya gyada kai shima yana kallon titin yace.
"Ki bari kawai, ni kaina ina da aji ™arfe takwas Win nan, kuma wallahi mai muhimmanci ne."
"Aji?" Da mamaki a fuskarta ta tambaya.
Sai ya juyo ya kalle ta.
"Au na manta ban gaya miki ba, na koma makaranta fa, Bayero na samu ina yin English saura shekara Waya ma na gama."
Kilishi taji ranta ya kara baci, har tana shirin bude baki tayi masa korafin ta yadda har ya shekara biyu a University ba tare da ta sani ba sai kuma taga meye damuwarta a ciki? Rayuwarsa ce, zata hana shi ne idan har hakan ba shafarta zaiyi ba, kuma ma tun asali ta san Awwalu mai son karatu ne, don tun yana yaro farkon zuwansa almajiranta da kudinsa yasa kansa a makaranta har ya gama firamare kafin daga baya kakarta ta shiga tallafa masa, kuma shekaru biyu bayan ta gama shima ya fita daga sakandiren, don haka karatunsa bai kamata ya dame ta ba.
Ta juya tana kokarin kallon wani mai teburin shayi daga can nesa dadu dake ta kokarin hada wutar itacensa, amma itacen ya™i bashi hadin kai duk kuwa da iskar sanyin da ake hurawa a lokacin. Ba shiri taji murmushi ya subuce a bakinta, zuciyarta ta cika da jin dadin yadda dattijon ke ta goho yana firfita wutar, tana son irin wannan abin, tana son taga wani nata wahala akan neman bukatunsa har sai zuciyarsa ta ™e™ashe ta daina rauni, shi yasa ko kallo bata cika yi ba, don bata ganin amfanin yadda mutane ke tsara finafinan su cewa mai kirki ne zai ci galaba a kodayaushe.
Taja tsaki bayan wutar ta kama babu daWewa, ta dawo da idonta cikin motar tana ™o™arin lalubo wayarta, sai kuma ta tuna ai ta kashe ta don kar ma a neme ta, kuma a daidai wannan lokacin sai ga wata mota katuwa ™irar jeep Prado tazo ta sha gabansu, nesa kadan tayi fakin ta tsaya.
"Ina ga gasu nan Hajiya."
Cewar Awwalu yana kallon motar.
"Fita zanyi kenan?"
Ya gyaWa kansa.
"Ai bana tunanin shi ne zai fito."
Sai ta kuma jan wani tsakin.
"Mutanen nan suna cin alfarmarta da yawa Awwalu, ba don dole Jamal ya bar duniyar nan ta hanyarsu ba, bubu abinda zai hana ni zaba musu irin tasu ™addarar su ma."
Awwalun ya juyo yana kallonta.
"Ha™uri zaki yi Hajiya minti biyar ne ba su isa su sake ganin fuskarki ba har abada, harbin tayar mota tana gudu ba aikin kowa bane banda irinsu da suka san duk wani tactis na abin...."
Bata ko jira jin ™arshen zancen nasa ba ta sauke nikabin da ta daura a fuskarta sannan ta janyo wata ´ar madaidaiciyar jaka dake gefenta tare da wata farar takarda ta bude kofar motar ta fita.
Kanta tsaye ta isa wajen motar ta tsaya daga daidai ™ofar baya, kuma daga inda Awwalu ke zaune yana hango sanda aka zuge gilashin ita kuma tasa hannu ta sake Wage nikabin nata.
Wani mutum ne zaune a ciki, fari tas dashi irin farin da yake komawa tamkar zabiya, sannan ilahirin fatarsa kaf, koina akwai wani Wigo-Wigon bakin wani ciwo da ya fito ya warke. Idanunsa na sanye da wani katon gilashi ba™i ta yadda ba'a ko ganin kwayar idanunsa, a lokaci guda yayi wani murmushi da ya baiyana jerin ha™oransa wanda rabinsu suna rufe da ™arfe ne irin wanda ake cewa hs™orin makka kalar ruwan gwal don haka sun haska tar a cikin hasken safiyar.
"Barka da zuwa Hajiya, sai ha™uri da irin aikinmu na gaya miki ni bana mu'amala da jakada, shi yasa kika ganni nima da kaina."
Hajiya Kilishi bata yi murmushin ba, tana kallonsa idanunta a tsaye tace.
"Tun da har ka ganni anan ai ka san wannan maganar ta wuce kuma."
Sai ya Waga mata girarsa daya cikin duniyanci irin nasa sannan ya nuna jakar hannunta yace.
"Sune wadannan?"
Sakan Waya biyu tana kallonsa hankalinta na kokarin danne takaicin dake yawo a zuciyarta kafin ta Wago jakar ta miko masa, ya kuwa karSa ya zura ta cikin motar sannan ya buWe, idanunsa suka yi nazarin kuWin dake ciki.
"Kince yau da misalin karfe tara zai fita sannan shi kadai ne a motar ko?"
Ta gyada kanta sau Waya sannan ta mika masa wannan farar takardar hannun nata.
"Ga lambar motar koda wancan text Win ya gige."
Ya karbi takardar ya kalla sannan ya sake Wagowa ya kalle ta.
"Hajiya zan so ace babu magana biyu a cikin wannan al'amarin namu, zamu ™irga kudin nan idan sun cika zaki ga aiki, idan kuma akwai matsala, to kuwa za'a sami matsalar da gaske."
Sai da ta Wauke kanta gefe cike da takaicin yadda yake mata maganar sannan tace.
"Idan kuma har babu matsalar ta yaya zan tabbatar da cewar zaku yin?"
Ta dawo da idonta kansa lokacin da yake sake wani murmushin.
"Tabbaci kike nema?"
Bata amsa ba, shima kuma bai jira amsar ba, sai kawai ya Waga yatsansa Waya a iska yana cigaba da murmushi.
Kuma bata gama tunanin me Ke shirin faruwa ba lokacin da ta wata irin ™ara ta ba™unci iska, tsananin karfin ™arar yasa duk dauriyarta sai da ta firgita, kafafunta suka yi baya yayin da tasa hannayenta duka biyu ta toshe kunnuwanta lokacin da idonta ya kai kan wasu maza da suka juya da gudu bayan sun karyo kwana, sannan ta hango wannan mai shayin ma ya kwanta a gaban teburinsa yana kakkarwa, tabbas ™arar ta bindiga ce ba wani abu ba.
"Wannan shine tabbacinki Hajiya, yarana basa wasa da aikinsu, hannu kawai nake Wagawa shikenan duk abinda nace zai wakana ko akan waye kuwa."
Bayaninsa yazo daidai da lokacin da idonta ya sauka akan tayar motarsu ta gaba, gabadaya ta dagargaje ta kuma wargaje a lokaci guda, motar ta tuntsira tayi gefen titi, yayin da Awwalun dake ciki ke kokarin buWe kofarsa don ya fito kar ta kara hantsilawa dashi.
"Na barki lafiya."
Ta sake jin muryar mutumin kuma ko kafin ta juyo ta kalle shi, direbansa yaja motar sun yi gaba da wani irin saurin da har sai da tayar motar ta gurzu da titi ta bada wata irin ™ara.
Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Hajiya Kilshi karo na farko a wannan safiyar, tabbas ta bakin Awwalun ne, mutanen nan sun iya aikinsu, rainin hankalinsu ne kawai a gefe. Taji murmushin nata na sauka har cikin zuciyarta da tunanin cewa ba za'a samu akasi ba, a yau Jamal zai bar duniyar nan, ai ta gaya masa... ta gaya masa lokacin da ya juya mata baya zai tafi.
_"Na so zan yi dukkan shirina in bar cikinku ba tare da na taba wani ahalin Baffa ba, nayi maka katanga mai yawa Jamal, na daWe ina kange ka daga sharrina, amma ka rufe idonka ka tsallako ka iso... Ina jiye maka takaicin barin duniya da ™uruciyarka, ina taya ka alhinin barin duniyar nan a lokacin da ya kamata ka fara cin ganiyarka, don daga yanzu ni da kai, mutane ne da baza su taSa iya rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba."_
Ta sake wani murmushin tana cije leSSenta, zata so ace zai tuna wadannan maganganun nata a lokacin yake bin ruhinsa da kallo zuwa sama. Awwalu ya karaso wajenta a lokacin da nasa murmushin shima, fuskarsa na Wauke da yanayin da ko bai furta ba ta san me zaice.
_"Me na gaya miki? Mutanen nan zasu iya aikin ki."_
Sai kawai ta juya ta kalli motar tasu a lokacin da Jama'a suka fara taruwa suna ™o™arin zagayeta.