← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 87

Sashe 83

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Komai mu™addari ne daga ubangiji ya yarda!  lokacin da ya amince da aurenta, yayi ne saboda Jamal, saboda ya san alakarsa da ita a lokacin da yaga sunanta har ma da adireshin ta, sai gashi daga baya ya fahimci cewa wannan sunan na wata Aminan ce daban da itama take a wannan unguwar ta gadon kaya, wata Amina ce daban da suka yi makaranta tare a wajen sauran takardunsa na wajen Hajiya Maimuna da bai san dasu ba sai a lokacin da Amina ta haddasa kusancinsu...

Allah ya sani bai san tarin alkhairin da zai lissafa  da ya samu ta dalilinta ba tun daga lokacin da ta shigo cikin rayuwarsa zuwa yanzu, kamar tana tafiya ne da wani haske a kafafunta dama hannayenta ta yadda duk inda ta taka ko kuma abinda ta taSa sai ta haskaka shi.

Ita kaWai, ita kaWai ce abinda idan ya tuna cewar ta hanyar Kilishi ya samu, zuciyarsa ke yin sanyi da tarin rangwamen da yake jin cewa zai iya kyale ta da iya hukuncin da take fuskanta anan duniya, amma tabbas ne cewa tsakaninsu da ita wani hukuncin sai a lahira, don ko da giftawar sakan guda baya so ko da fuskarta ne ta gifta a tunaninsa balle kuma wani abu nata.

Adadin yadda zuciyarsa ta so ta shine adadin tsanar da yayi mata a yanzu, tsanar dake tafiya tare da albarkacin Aminar da ta zama inuwarsa a yanzu, don abinda ya sani shine ba don ita din da yake kallo a gabansa ba, ko zai sake yi sau dubu yana kasawa, ba zai fasa ba zai yi ta kokarin da zai aika ta ne har lahirar da danuwansa ya tafi don ta riga shi zuwa da sakon da yake son ya isa ga danuwansa.

Amma saboda Amina, saboda ita da kuma sauran tarin yanuwa da iyayensa da yake ganin kokarin da suke yi akansa wajen ganin daidaituwar lafiyarsa...

Shi yasa a dole yake ta kokarin kai zuciyarsa nesa yana tuna tarin maganganun da kowa ke yi masa wajen ganin yayi hakurin da komai ya daidaita rayuwarsa, sai dai a duk ciki babu abinda yafi rikewa irin kalaman Ishaq da ya gaya masa cewa babu yadda suka iya da Kilishi, babu abinda zasu yi msta da zsiyo daidai da adadin cutar da tayi musu a duniyar nan, dole ne su hakura su kyale ta da iya abinda da Allah ya kadarta a rayuwarta kawai,fon wata shari'ar sai a lahira!

"Tabbas wata shari'ar sai a lahira...!"

Bakin sa ya maimaita hakan a yanzu yana kallon Aminan dake dariya a cikin wayar tare da Hamida...

Shine bai fahimta ba tun asali, Kilishi bata daga cikin mutanen da suka cancanta a rayuwarsa!... Bata cikin su ko kadan.

Sai kawai ya zaro Waya wayarsa ya shiga kiran mutumin da yake son ya hada shi da agency din da zai sayi kujerar makka guda biyu na Amma da kuma Baba (iyayen Amina).

Fatansa a kodayaushe shine ya faranta ran wannan ´ar yarinyar fiye da yadda take gyara tasa rayuwar!

*Alhmdlilah.*
*˜arshe.*

***

*Fara Wuta...*

_Ba'a kodayaushe ne Ubangiji ke rama cutar da makiyanmu ke yi mana daidai gwargwado da abinda suka zalunce mu a dashi ba, hakki yana da nauyi kuma yana bibiyar dukkan mai Waukarsa, sai dai dukkan wata wahala da kuma azabar da mai zalunci ke fuskanta game da wani hakki da ya Wauka a duniyar nan baya ™arasawa ko kaso guda a cikin Wari idan za'a kimanta sauran hukuncin da zai je ya tarar a gaban ubangijinmu... Don gaskiya ne abinda masu iya magana ke faWa cewa WATA SHARI'AR SAI A LAHIRA!_

_Ina fatan Allah ya bamu gamawa da kuma wucewa lafiya a duniyar nan ba tare da mun koma gare shi da hakkin kowa ba, sannan ina fatan kuma ba zaku dauki hakkina ba wajen tura labarin nan ga wasu a matsayin kyauta... Don bana fatan wata shari'ar ta hada mu daku a gaban ubangijin da kowannenmu zai koma gare shi._

_Godiya mai tarin yawa ga dukkan hakuri da kuma jinkirinku har zuwa gabar da muka kammala Farar wuta, nayi laifuka masu tari yawa na sani, amma dama da wuya ne kowacce tafiya ta kasance dari bisa dari wajen samun daidaito... Ina fatan dukkan wadanda na Satawa rai zasu gafarce ni su yi min afuwa irin wadda zasu so ayi mudu idan sune a matsayina..._

_Nagode ga dukkan masoya rubutuna, nagode da hakurinku nagode da lokacinku, Nagode da kaunarku, idan har zanyi wani rubutu a gaba ina fata ba zai karaso gare ku ba sai a cikakken sa insha Allah._

_Ina fatan Allah ya faranta rayuwarku fiye da yadda zan kimanta... Allah ya bamu ikon amfani da ´an darussan dake cikin labarin nan... Jazakallah khairan._
Chapter 83 · 0% Book details