← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 87

Sashe 32

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shiga cikin falon inda mutane da yawa suke, suna ta gaishe shi ya amsa sama-sama don kaWan daga cikinsu kawai ya sani wanda sune manyan, wata yayar mahaifiyar tasa ta tsayar dashi suka yi magana akan aikin da take son ya samowa danta a wajen aikinsu kafin ya shige kai tsaye zuwa Wakin mahaifiyar tasa.

"Wallahi kinyi kyau, babu wadda ta isa tayi miki kallon raini a cikinsu, babu wadda zata yada miki maganar cewa ba kya fantamawa kamar su."

Abinda ya fara ji kenan yana fitowa daga bakin wata Aunty Nana kafin hoton mahaifiyar tasa ya shiga idonsa, ta saka wata doguwar riga ta lace da zai rantse da Allah babu wajen da yatsa Waya zai zauna ba tare da taSa tarin dutsunan dake ™yalli ba, sai wal™awa suke suna haske kota'ina.

Ba shiri ya haWe ransa a take sanda mutanen Wakin ke kiran sunansa da korafin tun safe suke nemansa.

"Naje aiki ne."

Shine amsar da yabi kowanne su dashi bayan gaisuwa.

"Mamah mukullin motata nake nema."

Ta tambaya kai tsaye sanda ya isa gabanta, sai tayi murmushin da ya nemi karya zuciyarsa a lokaci guda, murmushin da yasa ba shiri duk wannan haWe ran nasa yabi iska.

"Haba Babana, yanzu ba zaka ce nayi kyau ba...?"

Yasa yatsansa daya ya shafo kan hancinsa, sannan yace.

"Mamah kinyi kyau... Kinyi kyau sosai."

Sai kuma ya kara da.

"Sai dai na so don ra'ayinki kika yi wannam kwalliyar ba don wani ko kuma wasu ba."

Murmushin da take bai bar fuskarta ba tace.

"Ka kawo min mata ka gani wanda zanyi don kai bashi da iyaka Babana, har sai ka rufe idonka."

Murmushin da bai shirya ba ta sake saka shi kafin ya gyaWa kansa yace.

"Allah ya kaimu, key Win motar yana wajenki?"

Daidai lokacin da Zainab ta shigo dakin a lokacin, hannunta dauke da wani katon kwando, yana jin yadda sauran Aunties Win nasa na Wakin suka samu damar korafin jiran bikin nasa da suke yi suna faWin so yake yi su haWa shi da ™annensa su Khairat tukunna, amma hankalinsa baya kansu tun sanda ta shigo dakin, hannunta na Wauke da wani ™aton kwondo da ta ciko kayan da bai san na menene ba dasu, idonsa ya bita da kallo sanda taje har can ™arshen Wakin ta bude wardrobe tana saka kayan.

"Zainab anyi namu wankin?

Wata ta tambaya a cikin mutanen dakin, sai ta Waga kanta da sauri tana murmushi tace.

"Eh suna cikin dryer ban ™arasa dasu ba, amma yanzu zan kwaso."

Wata da ya san sunanta Aina'u tace.

"Kafin mu tafi ki kwaso min kayan da kika kai mota Wazu, na fasa barinsu anan."

Bata amsa ba wata tace.

"Zainab an karSo min sa™on kuwa?"

"Yanzu zan karbo Aunty, ban samu lokaci bane tun dazu."

Sai ta gyaWa kanta tace.

"Babu komai, ai kina kokari ma, tun safe kike tsaye."

Daga inda Hajiya Mardiyya ke ™o™arin lalubo mukullin motar Jawad Win tace.

"In dai Zainab ce ai ba daga nan ba,bata zama sam."

Duk maganganun da ake yi idanun Jawad na kan yarinyar, yana kallon yadda take saka kayan cikin wardrobe da sauri da kuma yadda hannayenta ke rawa, wani abu ya gifta cikin zuciyarsa da bai san menene ba.

Ta gama saka su tazo wucewa daidai lokacin da Hajiya Mardiyya ke miko masa mu™ullin motar, kuma bai ji me take cewa ba kawai ya karSa sannan yabi bayan ta, suka fita daga Wakin tare.

Kwandon da ta juye kayan ne a hannunta tana ta ratsawa ta cikin mutanen dake Wakin har waje, hannayensa duka cikin aljihun wandonsa yana bin bayanta har suka fita wajen, tayi kwana zuwa hanyar inda Wakunan kwanan su suke,kuma bai tsaida ita ba har suka fara shiga wajen suka bar hayaniyar mutanen nan a baya sannan ya kira sunanta.

"Zainab."

A lokaci guda ta tsaya cak kafin ta juyo da sauri, idanunta suka zare a lokaci guda da ganinsa, tasirin mamakin ganin nasa ya haska ™arara a fuskarta kafin ya lura cewa rawar da hannayenta ke yi sun ™aru. Sai kawai ya taho ya ™araso dab da ita ya tsaya. Hasken fitilun wajen ya nuna masa yadda fatar bakinta ta bushe sosai ksmar yadda ya hango.

"Kinci abinci?"

Ya tambaya kai tsaye yana kallon ta, bashi take kallo ba ta sunkuyar da kanta ™asa kawai, kuma jin tambayar yasa babu shiri ta shiga Waga kanta da sauri, Waga kan da a cikinsa ya fahimci cewa amsaawa kawai take don ta tsorata amma hakan ba gaskiya bane.

Sai ya ja tsakin da bai shirya masa ba, ™ararsa ta fito ™arara, sannan yana kallonta ya sake maimaita abinda ya fada.

"Ba wasa nake miki ba, nace kin ci abinci?"

Wucewar sakan daya ,biyu kamar ba zata amsa ba sai kuma ta girgiza kanta a hankali alamun A'a. Ya cije lebbensa yana gyada kai sannan yace.

"Biyo ni."

Ya fada ba tare da ya matsa ba, ta Wago ta kalle shi sannan ta girgiza kai har yanzu idanunta na nunawa da tsoro.

"Akwai aikin da zanyi da yawa, su Hajiya suna ta jira na, dan Allah ..."

Bata ™arasa ba saboda tasirin yadda idanunsa ke kallonta, kuma ganin ta dakatar da kanta da kanta yasa shi lumshe idanunsa a hankali sannan ya juya, har a lokacin hannayensa sanye cikin aljihunsa, ya juya ya fara tafiya.

Zainab ta kalli bayansa, yadda ™aramar rigar ta fito da fadin kafaWunsa, zuciyarta ta kara nauyi a ™irjinta, sai kawai ta haWiye wani abu a makogwaronta sannan ta bi bayan nasa itama.

Ta cikin mutanen nan suka wuce, tana tsayawa nesa dashi kadan duk sanda ya tsaya magana da wasu, kuma kusan sau biyar yana juyowa ya tabbatar idan tana bin nasa har suka ™arasa Sangarensa, ya buWe kofar da mukullin da ya zaro a aljihunsa sannan ya shiga ciki yana barinta a buWe.

Ta sake yin karfin halin danne zuciyarta kafin ta taka kafafunta ta karasa zuwa ciki, har yanzu tana ri™e da wannan kwandon, hannunta ya saki kofar bayan ta shiga cikiba tare da ta rufe ba, kuma har ta yi taku biyu a ciki taji muryarsa a cikin kanta.

"Koma ki rufe kofar."

Ta juya gefen da taji muryar, wajen kujerun falon dake gefe, yana kwance akan guda Waya three-sitter dake fuskantar Tv ya mike kafafun sa.

Sai ta juya a hankali ta koma, ta tura kofar a hankali har ta rufe, amma kuma sai ta kasa juyowa, ™afafunta suka tsaya a wajen, hancinta na sha™ar daddaWan kamshin air freshener da ta fesa da kanta yayin da hannayenta ke rawa ri™e da wannan kwandon.

"Ki ajiye wannan abin ki shigo ki ci abinci "

Ya faWa ba tare da ya bata damar shawara da zuciyarta ba, sai ta juyo ta sake kallonsa, shima ita yake kallo daga yadda yake kwancen.

"Wallahi akwai abinda zanyi da yawa, suna jirana kuma... kuma Hajiya zata min faWa, al™ur'an..."

"Me?" Ya katse ta a lokaci guda yana kallonta.

"Me kika ce?"

Ba tare da ta fahimci abinda yake nufi ta sake cewa.

"Alqur'an faWa zata yi min..." Rantsuwa ta sake fitowa daban da yanayin fuskarta, babubta yadda wani zai ce ma ita ta fada. Sai kawai ya girgiza kansa.

"Kar in sake ji kin fadi wannan rantsuwar. Bana so, kar ki sake faWa."

Ta hadiye yawu a makogwaronta sannnan ta gyada kanta a hankali alamun ta ji kuma ta fahimta, shima ya gyada nasa.

"Good, now enter."

Bata ji me ya faWa ba amma dai ta san yana nufin ta shigo ne, sai duk da haka ta kasa motsi daga wajen ta tsaya a tsorace kamar wani zaiyi motsi ta juya da gudu ta koma.

Kusan minti guda taba tsaye a haka kafin muryarsa ta sake ratsa kunnenta.

"Zaki yi dana sanin tsaiwa anan, idan na taso."

Sautin muryar tasa ya fito iri Waya dana kwanakin baya, ranar da ya gaya mata cewar idan ta sake ta bayyana wannan sirrin nasa da taji, ba ita zai taSa ba, mahaifiyarta da ta baro a ™auye zai sa a lahanta.

Don haka abinda bata gane ba yanzu shine meye manufarsa kuma yanzu akanta?

Wani yawun da bata shirya masa ya wuce a bakinta sanda ta tuno maganar mahaifiyarsa, maganar da tayi sanadin kawo ta cikin wannan ™ullin.

_"Ki saka min ido akansa sosai, shi yasa nake aika ki kuma nake saka ki gyaran Sangaren sa, duk wani abu da kika gani daban a dakinsa ki kawo min, ko waya yake yi ko kuma yana tare da abokansa ki tsaya ki saurara, dole yana ™ulla wani abu na sani Zainab, don haka idan banji komai daga gare ki ba, matakin da zan Wauka zai shafi har iyayenki!"_

Allah ya sani a yanzu bata san meye mafitar ta ba, ta san dai kawai ko waye zai fassara halin da take ciki da Gaba kura, baya sayaki.

***

"Ina jinka..."

Tattausar Muryar Ma'aruf ta faWa a cikin office Win, a cikin wayar da yake yi zaune akan teburinsa, hannunsa Waya na kan wata ™atuwar jotter da yake rubutu akai. Daga cikin wayar muryar Yakubu ta cigaba da cewa.

"Na sami former address Win sa da komai ance anan gidan ya zauna directly da suka taho daga Kano, amma kuma satinsu uku a gidan suka tashi.

Kuma na fahimci kamar wani abun ne yasa suka tashi don ance min cikin dare suka bar unguwar babu wanda ya sani sai mutumin da suke hayar gidan a hannunsa, to shima jiya munyi kusan 3 hours tare ya rantse min da ubangijinsu cewa bai san inda suka tafi ba, sai dai ya san mai taxi Win da ya Wauke su daga nan unguwar.

To da safen nan munje gidan mutumin amma kuma sai matarsa muka tarar ta, gaya mana cewa wai wasu mutane sun dauke shi haya zai kaisu wani ™auye a can hanyar Uyo, kuma wai kwana uku zasu yi sannan ya dawo dasu,to da har naui niyyar daukar mai mota naje can sai kuma banga tunda ba dadewa zaiyi ba ai zamu iya jiransa don kwana uku kawai, amma what do you suggest?"

Ma'aruf yayi shiru yana kallon abinda ya rubuta, idanunsa ya haska da nazarin da kwakwalarsa ke yi, sai kawai ya ajiye biron hsnnun nasa sannan ya shafo saman kan hancinsa.
Chapter 32 · 0% Book details