← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 87

Sashe 19

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma'aruf ya rufe idanunsa, ya dafe goshinsa da hannu daya yana rarraba ´an yatsunsa akan goshin. Abubuwan dake yawo a cikin kansa basu da iyaka, motsin kowannensu kawai yake ji yana ihu tare da ´anuwansa, yana jin kamar tafiya suke yi akan fatar kan nasa suna zagayawa da karfin da yafi na kadawar iska a cikin sakanni.

Me yasa ne sai su? Me yasa ko waye su ya zaba yana bibiyarsu? Me yasa ko sau daya bai taba tunanin ya barsu su huta ba? Kamar dukkan fafutuka da kuma ayyukan da suke yi na da sauki a wajensa, kamar a rana Waya kawai suke kammala komai ta yadda gake diban dukiyarsu hankalinsa a kwance, yana jin cewa zuciyarsa ba zata tafi da nauyin wahalarsu da ma guminsu ba.

"Na gaya maka B, na gaya maka ka bari sai ka dawo office tukunna ma tattauna, but you still insist. Gashi nan yanzu naji alama you're changing, bana so na jawo maka wata matsalar kaima ka sani. So mayi magana kawai anjima."

Da haka wayar ta katse kuma Ma'aruf bai sauke ta daga kunnensa ba, ya cigaba da rike ta kawai idanunsa a rufe yayin da kwakwalwarsa ke juyawa da son tantance dukkan wata kalma da ta fito daga bakin Faruq din.

Bashi da wanda zai zarga, babu wannan mutumin a cikin lissafinsa, amma ya san a yanzu zargin kamar dole ne, don ta haka ne kawai za'a iya  samun hanyar da zasu fara tunanin kawo ™arshen wannan al'amarin.

Anyi haka ba sau dayaba, ba sau biyu ba... An daWe ana irin wannan abin a kamfanin tun kafin ya kai ga karbar wannan mu™amin, anyi a farkon fara aikinsa ma, watannin daBaffa da Baba Usman suka dora dukkan wani fatansu akansa na cewar abubuwa zasu canja da zuwansa, amma babu abinda ya canja Win banda adadin kudin da suka ninku wajen bata ma fiye da baya.

_Ina so ka sani Ma'aruf ba kowa zaka dinga yarda dashi a duniyar ba, wani lokacin mutanen dake kusa da kai suna iya zamewa abinda makiyanka, ba a kowacce fuska mai murmushi ake samun so ba, ba a kowanne ido mai kyalli ™auna take ba._

Kalaman Jamal sula haska akansa tun bayan wani lokaci, a shekarun baya ya kan tuna su fiye da cikin masaki, amma da wucewar lokaci da kuma hargitsin rayuwa ya manta lokaci na ™arshe da ya tuna su sai yanzu da suka dawo kansa a lokaci guda, yana iya tuna cewa a wancan lokacin Jamal ya gayamasa cewa bai san dalilin da yasa ya fada masa hakan ba, kawai tunani yake cewar zai iya amfanarsa a gaba...

'Gaban' tana da ma'ana da yawa, zata iya zama shekarun baya da suka wuce, zata iya zama shekaru masu zuwa a gaba, zata iya zama kuma yanzu, yanzun da yake jin kamar maganar tana Woruwa ne akan halin da yake ciki.

Ya ajiye wayar a hankali daga gefen kujerar sannan ya mike a zuwa hanyar kitchen inda ya baro Amina ya taho amsa wayar, ya san ma ta gama aikin nata a yanzu, don tun kafin ya fito ta kusa karasawa.

So yake yayi distracting kansa, so yake ya juyar da tunaninsa a yanzu gabaWaya daga kan wannan al'amarin, ya samu wani abu da zai Wauke hankalinsa ya manta da abinda ya gama ji, don bai san me zai faru ba idan ya cigaba da kasancewa cikin hakan a yanzu, abinda ya sani kawai shine koma waye a bayan wannan al'amarin zaiyi dana sanin da wani mahaluki bai taba irinsa ba duk ranar da yazo hannunsa.

Don haka yayi kokarin maida tunaninsa kan Aminar a yanzu, yana kuma tunawa kansa da dukkan abinda ya faru jiya, jiyan da a cikinta kadai ya kara yarda cewa da gaske ™aunar yarinyar nan, zuciyarsa ta manta da dalilin da yasa ya aure ta don baya ko saka ranar fara wannan binciken, tunda ya taushi kansa da cewar sai ya saba da ita tukunna shikenan ya ajiye hakan a gefe.

Baya iya wani tunani sai na yadda kusan komai nata ke burge shi, halaiyarta, saukin kanta da kuma kunyarta wadda bata hana ta abinda take so, ya kara fahimtar hakan a jiya sosai, a jiyan da yaso abubuwa su fi haka a tsakaninsu, amma baya jin dadi, baya jin kwarin jikinsa kuma baya son yin komai a wannan yanayin, don bai yarda da kansa ba, bai san ta yaya ma komai zai kasance ba.

Ya karasa cikin kitchen din idanunsa na nuna masa cewa babu kowa a ciki, sai kayan girkinta da ta gama ta jera komai tsaf akan table. Karfe sha daya ne na safiya a lokacin, basu dade da tashi ba, don ita kanta ya kula ta gaji jiyan, kwanan asibitin nan da suka yi ba wani mai dadi bane, shi yasa ya sake rike ta a jikinsa bayan sunyi sallar asuba, tana ta gaya masa cewa zata tashi da wuri amma ya ture bayaninta ya kashe bakinta.

A haka wani baccin yayi awon gaba dasu su duka biyun wanda basu tashi ba sai ™arfe goma saura, shi ya fara tashi ma, kuma yana yin motsi ta farka, shikenan sai baccin ya kare.

Kofar kitchen din ta baya da take a buWe ta shaida masa cewa fita tayi wajen, don haka ya nufi wajen kuma tun kafin ya ™arasa ya hango ta, ta wanke wasu ´an kananan dusters na kitchen Win tana shanya su a jikin igiyar da bai san lokacin da ta Waura ta ba.

Wannan rigar ce a jikinta, wannan rigar da bata rufe kafafunta ba, da safen nan bayan tayi wanka ya roke ta da Allah da ta saka don zuciyarsa ta gaji da hasashen kafafun nata da yake jin kamar ya shekara bai gansu ba, kuma da kyar ta yarda ta maida kayan da ta dauko ta saka din tana fadin ita ta bacci ce, abinda yasa shi tunanin zai siyo wanda ba na baccin ba kenan.

Amina ta shanya tawul na gaba a hannunta yayin da take jin zuciyarta tayi wani irin wasai a yau, farin cikinta na karuwa da kowanne wucewar lokaci idan ranta ya tuna abinda ya faru jiya, kokarin da  tayi wajen hada al'ummar gidan nan kaf a gaban Ma'aruf bayan tashinsa, ciki har kuwa da mahaifiyarsa da sai dagabaya ma zuciyarta ta bata shawarar hakan, wani abu da ta san babu wanda bai ji dadinsa ba, don ko su Shukra kafin su tafi suna ta fadin zasu tambayi Ma'aruf ya barta tazo inda suke suma, yayin da Salma ke fadin cewa zata zo su saka labule, tayi ta binsu da murmushi kawai tana amsawa har suka tafi, Shahida ma matar Faruqa a jiyan kadai ta sake da ita har sunyi exchanging numbers, musamaman da Wan ™aramin Wanta Aabid yaki kowa duk a tarin jama'ar nan ta jiya sai ita da kuma Inna Danejo... Har Innan na ta tsokanarsa cewa jinin tsofaffi ne dashi don wai tana da kishiya data rasu mai suna Amina.

Sannan ga Ma'aruf ma, yadda ya dinga yi mata jiya kadai ya isa ya shaida mata irin nasa jin dadin, don har godiyar yayi ta radawa a kunnenta, godiyar ma da daga baya ta kasa tantance gabadaya ta mecece. Yanzu babban abinda ya rage shine ta roke shi ya barta taje gidansu kafin Hajiya Kilishi ta sake Wago da wani abun ko kuma ita ta cigaba da nata takun.

Don Allah ya sani tana kewar ´anuwanta fiye da yadda zata iya misaltawa, shi yasa ko a jiyan da suka yi waya da Fati da kuma Maryam a wayar Fatin, bata ko sake yi musu zancen zuwansu ba, don ta yiwa kanta alkawarin da kanta zata zo sai dai su biyo ta daga baya.

A wanan lokacin ne kuma Ma'aruf ya karaso ta bayanta, ta san shine don a lokaci guda ya  hanayensa zuro ta gefen cikinta duka biyun ya rungumota ta baya, fuskarsa ta sauka akan kafadarta guda Waya yayin da Wumin fatarsa da kuma na hannayensa suka ratsa jikinta a take... Zazzabi ne kuma ya kama shi?

Babu shiri ta juyo da sauri tana kallonsa, sai yayi mata wani guntun murmushi sannan yasa yatsansa Waya yana taSa gashinta da ya fito ta gaba kamar yana karkaWe mata wani abun, a lokaci guda taji zuciyarta kamar ta fashe a kirjinta, dumin hannayensa ya shiga ratsa fatar goshinta yayin da numfashinta ya fara rawa a kirjinta, ta zata ta fara sabawa... Sai kawai ta buWe baki tace.

"Zazzabi kake... yi?"

Ya girgiza kansa a hankali.

"Lafiya ta kalau, na gaya miki na warke tun jiya, ko baki yarda ba?"

Ta girgiza kanta itama.

"Jikin ka da zafi har yanzu."

Sai kawai ya jawo duka hannayenta biyu dake Wauke da kowanne dusters Win nan jikakku, ya kara su duka biyun akan kumatunsa sannan yace.

"Kina jin zafin har yanzu?"

Tayi wani guntun murmushi sannan ta girgiza kanta.

Ya cije lebbensa kaWan.

"Na so kince A'a, don ina da wasu hanyoyin da zan nuna miki cewa lafiyata kalau BabyDoll."

"Me yasa kake kirana haka nr?"

Yace.

"Saboda kina min kana dasu, wadanannan siraran ´antsanan da nake gani su Sahla suna wasa dasu da."

"Zanyi kiba kwanan nan, kar ka damu."

"Da gaske?"

Ya tambaya ysna kara matso da fuskarsa kusa da tata.

"... Me zai saki kiyi kibar?"

Tana murmushi har yanzu ta Wauke hannyenta daga fuskars ta dan ture shi baya ta kafadunsa sannan tace.

"Idan nayi zaka gani."

Yayi baya ya dawo sannan ya girgiza kansa.

"Ki gaya min idan akwai gudunmawata kinga sai na fara shiryawa tun yanzu."

Yadda yake maganar ya sata yin dariya kafin tayi kokarin juyawa a hankali don karasa shanyar na hannunta, amma ya dawo da ita.

"Seriously idan kiba kike so na san ta yadda zamu samo ta, kawai ki gaya min."

Ganin da gaske yake yasa ta kara ture shi tana dariya.

"Nan fa waje ne, beside rana tana tayi ma bamu yi breakfast..."

Muryarta ta katse sanda ya dora goshinta a saman nata, idanunta suka shiga haskawa da mamaki da kuma tsoro tace.

"Wani zai iya shigowa fa..."

Ya girgiza kansa, motsin na tafiya da nata kan.
Chapter 19 · 0% Book details