Sashe 17
Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya zura wayar a aljihu, sannan kai tsaye ya fito daga wajen ya nufi hanyar da zata zagaya dashi baya zuwa Sangaren masu aikin gidan, bangaren dashi kansa gida ne guda mai ™atuwar haraba da kuma shuke-shuke, ba zai iya tuna rana ta karshe da ya taka kafarsa zuwa wajen ba, kawai dai ya san kafin su kai ga tarewa a gidan da suka zo gabaWaya tare da mahaifinsu da kuma sauran ´anuwansa maza, sun zagaya koina har nan kuwa.
"Good morning sir... Good morning."
Wasu ´an aikin guda biyu dake shanya tarin kayan wankin yara suka tsugunna suna gaishe shi, ya gyaWa kansa alamun amsawa sannan ya tsaya yana kallonsu, ya rasa ma me zai ce musu saboda ko sunan yarinyar bai sani ba, ya san dai ya taba ji Mamah ta taSa kiranta a gabansa, watakila fiye da sau Waya ma amma baya jin zai iya tunawa.
"You want something sir?" ( Kana bukatar wani abu ne yallabai?)
Daya daga cikin ma'aikatan ta faWa, sai dai kafin ya buWe bakinsa yayi magana idonsa ya hango masa ita, ta karyo kwana ta shigo wajen, hannunta dauke da wani katon farin nokiti da ta ciko kayan miya a ciki, ko daga nesa ya san bokitin yayi mata nauyi daga yadda yake kokarin rinjayarta ta gefe guda.
Sai kawai ya juya ya nufi wajenta, kuma har ya taho bata lura dashi ba sai da ya iso daidai gabanta tukunna, da farko idanunta basu shaida shi sosai ba, watakila ko bata taba zaton ganinsa a lokacin kuma a wajen bane, amma a lokaci guda sai idanun nata suka haska da tsananin mamaki da kuma fargaba.
Yana ganin yadda ta saki bokitin da sauri zuwa kasa kafin itama ta bishi kasan ta durkushe kan gwiwoyinta sannan tace.
"Ina kwana... Barka da safiya."
Duka kalar gaisuwar guda biyu shi kaWai, kuma har ya buWe baki zaiyi magana sai idonsa ya kai kan wasu mata daga ginin dake gabansu sun le™o ta window suna hangensu, wani tunani ya gifta a cikin ransa don haka sai kawai ya maida kalaman da yayi niyyar faWa yace.
"Me kuka dafa a bangren Mamah?"
Tambayar ta shiga kan Zainb da tsananin mamakin da ya fi na farko, don ta tabbata ba abinda ya kawo shi kenan ba, ya za'ayi ya bato bangaren ya taho tun daga can har zuwa nan don ya tambayeta kawai abinda aka dafa? Mutumin da idan hr ba fita zai yi ba kowa ya haddace cewar baya tashi sai rana ta mi™a, amma ™arfe nawa yanzu? Tara da mintuna...
Ta yaya ne ma yake mata magana muryarsa a ™asa, ta zata ai idan har ba tare da mahaifiyatsa yake ba baya iya magana babu hantara. Sai tayi saurin hadiye abu a bakinta sannan tace.
"Ba'a gama abincin duka ba, an dai yi wasu."
Ya gyada kansa.
"Ki debo wanda aka gama ki kawo min."
Da haka bai kara cewa komai ba yayi gaba. Zainab tabi bayansa da kallo gabanta na faduwa kafin ta mike a hankali.
Kuma minti goma bayan hakan, ta kwankwasa kofar Wakin nasa Wauke da farantin kayan abincin, kallon da sauran manyan ´an aikin gidan suka dinga binta dashi bayan ta gaya musu inda zata kai abincin.
"Shigo."
Muryarsa ta fada daga ciki, kuma karo na farko ta murda hannun kofar ta shiga, dakin kamar yadda ta zata ne, ™ato mai cike da hadaddun kayan kamar na sauran ´anuwansa mata, sai dai har gwara nasu ma yafi kyale-kyale akan wannan da komai tsilla-tsilla ne. Yana zaune daga gaban gadon dakin a tsakiya, ya dora hannayensa kowanne akan cinyoyinsa yana kallonta, kuma da yatsu biyu kawai yayi mata alamar cewar ta karaso.
Ta taho Win, amma muryarsa ta tsaida ta.
"Koma ki rufe kofar."
Gabanta ya sake faduwa, amma babu yadda ta yi ta koma Win ta rufe ta a hankali sannan ta sake juyowa, tana ta tahowa bai ce ta tsaya ba, kallonta yake yi ta sani amma ita idanunta na kan farantin.
Sai da ta karaso nesa dashi kadan sannan ta tsugunna ta ajiye farantin a saitin gabansa, kuma kafin ta mike kamar yadda daga shi har ita suka san shine abu na gaba ya sake magana.
"Zauna."
Ta hadiye wani kullutun abu a makogwaronta sannan ta gyara tsugunnon nata a hankali alamun ta zauna Win, tambayarsa ta gaba ta kada ´a´an hanjinta a lokaci guda.
"Daga ina kike?"
Sai ta dago ta kalle shi.
"Nace daga ina aka kawo ki?"
Ya sake maimaitawa, ya sake maimaitawa yana fadada tambayar da ta riga ta fahimta din kuma ta san ina take dosa.
"Sunan garinmu Yakura, a kusa da Kaduna yake." Muryarta tana rawa.
Ya gyada kansa.
"Waye ya kawo ki nan?"
"Abokin babana ne."
"Ina baban naki?"
A hankali tace.
"Ya rasu."
"Ina babarki?"
Sai da ya lura ta hadiye wani abu sannan tace.
"Tana nan, matarsa ce ita yanzu."
Kalaman suka daki kirjinsa da wani abu da bai san meye ba, amma dai ya san nazarinta yake yi, nazarin shekarunta da ya kasa ™iyasinsu.
"Ita me yasa bata hana shi kawo ki ba?"
Sai ta sake dagowa ta kalle shi, idanunta na nuna wani abu da ya kasa tantancewa, idan ma tunani take cewa muryarsa ta fito da damuwa ne, zai goge mata hakan yanzun nan.
"Bashi da kirki, Naani baza ta iya hana shi ba."
Kalmar Naanin da ta fada ya fahimce itace mahaifiyarta don haka kai tsaye ya sake tambaya
"Yaya sunanki?"
Wannan karon da mamakin da yafi nasa ta kalle shi, bai san sunanta ba? Bai san sunanta ba yake tambayar labarinta?
"Sunana Zainab."
Sai ya sake gyaWa kansa yana kallonta.
"Zainab, I know you heard us...."
Maganar tasa ta katse tuna cewar a banza zai yi bayanin ko ta cigaba.
"Na san kin ji mu ranar nan, kinji duk abinda muka fada ni da wanda yazo...."
Ta riga ta sani dama, tasan zancen da zai yi mata kenan, ta san ta shiga uku, ta san karshen rayuwarta a gidan nan tazo tun daga wannan lokacin, Allah ya sani tana jin daWin zaman gidan nan fiye da sauran gidaje biyu da tayi aiki dasu a baya saboda yadda mahaifiyarsa ke kyautata mata, amma tun daga ranar da ta ci karo dashi har ta zuba masa miya a kaya, tun daga ranar hannayenta suka fara lissafin kwanakin barinta gidan, sai gashi ta samu talalar wasu watannin kafin shekanjiya ta tabbatar mata cewar wa'adin kwanakin nata yazo karshe.
Don haka taji yadda iska ta wuce cikin busashshen makogwaronta kafin ta tattaro dukkan karfinta ta daga kanta sau daya.
Jawad ya gyaWa nasa kansa shima.
"Good. Shi yasa na kira ki nan."
Ya fadi hakan sannan ya gyara zamansa.
"Ba zaki so in zama abokin babanki na biyu ba Zainab balle kuma har in fi shi, don ina rabbatar miki zan iya kuntata rayuwarki fiye da yadda bakya tunani idan har kika zabi yin wasa dani.
Abinda kika ji sirrina ne, kuma duk da babu yardata ya iso gare ki, na baki amanarsa a yanzu, kuma in so ki barshi a cikin ranki, ki barshi kamar yadda yake a tsakanin mu yanzu, idan har shiga kunne na biyu musamman kunnen mahaifiyata Zainab..."
Yayi shiru yana cije lebbensa kafin ya fadi abinda yasa ta zare idanunta a lokaci guda ta dago tana kallonsa, hannayenta dama ilahirin jikinta gabaWaya suka shiga kakkarwa yayin da idanunta ke haskawa da tsoron da bsta lissafa dashi ba a duk wani lissafinta na ukubar rayuwar da take tunanin fuskanta!
****
*Kano.*
*No. 58 Mafara Street, NNDC SharaWa Quaters.*
*˜arfe Goma na safe.*
A cikin dakin, cikin uwar dakin Hajiya Kilishi ta dubi kawarta Hajiya Salamatu wadda isowarta kenan a wannan safiyar bayan fitar Mama Rabi wadda ta shirya musu abun motsa baki fal a wani katon faranti.
"Kinyi min nisa da yawa Salamatu, china tayi min nisa tunda ni ba harkar social media din nan nake yi ba. Na kulla abubuwan da yawa wanda babu tayawarki a ciki balle har mu kai wa tufkar ™arshe mai daukar ido."
Hajiya Salamatun ta cire dankwalinta ta ajiye shi a gefe, mikakken gashin kanta da yasha gyara ya shiga nuna maikonsa cikin hasken dakin kafin tace.
"Ni iyaka ta dake ai shawara Kilishi, wasu ma ba Wauka kike ba idan na fada, to don me zaki yi kewata? Yanzu kawai ki gaya min me ya faru? Me ya faru daga inda na barki."
Hajiya Kilishi ta juya idanunta tana murmushi sannan ta kalli aminyar tata dake zaune daga bakin gadon dakin tace.
"Abubuwa da yawa Salamatu, don haka mu kyale ™ananan ma a gefe, mu fuskanci manyan.
Na riga na gama da yarinyar nan, ta san komai kuma ta yarda da komai..."
"Haka cikin sauki?"
Salamatun ta kasa daure namakin da yasa ta katse ta wajen tambaya.
Sai kawai ta Wauki kofi guda akan farantin, ta tsiyaya lemo a ciki ta mikowa Hajiya Salamatu kafin ta bata amsa.
"Ba cikin sauki bane, nayi abinda ba zata iya bijire min bane kamar yadda ta fada da bankinta. Kin sani Salamatu, kin san yadda bana wasa da dukkan abinda nasa a gaba, kuma kin san yadda nake bawa abinda nake so muhimmanci."
Hajiya Salamatu ta kurSi lemon sannan tace.
"Na sani Kilishi, ba sai kinyi wannan bayanin ba, na yarda kin samu yarinyar bayan ita kuma sai me?"
Tayi wani sassanyan murmushi tana kallonta.
"Sai burin da na Wanawa tarko, burin cike kan wadannan kudaden."
"An samu?"
Ta tambaya bayan ta ajiye kofin lemon.
"Kwarai, an samu Salamatu, wani ciniki suka yi na makudan kudaden da har suka fi gejin da nake nema ma."
"Kince min ya gano waccan hanyar taku ta hacking account din kamfanin da akayi aka tura musu da alert din bogi. To wannan karon me kika yi?"
Kai tsaye Kilishin tace.
"Kwantar dashi nayi kamar yadda na saba kuma zaki yi mamaki ta hanyar yarinyar nan hakan ta faru."
Wannan karon da mamaki Hajiya Salamatun ta kalle ta kafin ta kyalkyale da dariya.
"Irinki basu da yawa a kowanne ™arni Kilishi, shi yasa nake gayawa duk mai takura min akan rayuwa cewa ya kyale ni kawai, da nayi niyya zan rayu a duniyar nan kamar a aljanna ne saboda ke." (Waiyazubillah.)