← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 87

Sashe 2

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(Daga karshe ina son mu mika jinjina komai ga hazikin shugabanmu, Mr. Ma'aruf Mansoor Bakori, don ba don shi ba, ba zamu ™araso wannan gaSar a yau ba.)

A lokacin ne kowa ya juyo yana kallonsa yayin da sautin wani tafin ya sake karadewa, hatta Faruk sai da ya tsaya da aikin da yake yi shima ya shiga tafin tare da kifta masa ido.

Sai kawai ya mike tsaye yana sunkuyar da kansa alamun godiya, kuma a wannan lokacin ne kalamansa tare da na Jamal suka haska a cikin kansa.

_Idan kuma ni na mutu kai ka rayu fa?_

_Sai in ajiye dukkan burin rayuwata a gefe in karbi matsayinka, inyi irin rayuwarka ta yadda kowa zai ga cewa Ma'aruf ne ya mutu ba Jamal ba!_

This is you Yaya! (Kaine wannan Yaya!)

A hankali ya furta abinda yake fada a duk lokacin da ya zama sanadin samar da wata nasara a Kamfanin.

***

"Ka san ™o™arin da muka yi da mutanen RTL Win nan shine babban abinda ya sake Wago da percentage dinmu."

Faruk ya faWa bayan kammala meeting Win suna zaune a cikin office dinsa. Faruk Win ne zaune akan kujerar Ma'aruf Win yana neman abu a cikin desktop din kan teburin yayin da Ma'aruf din ke zaune daga tsakiyar office din inda aka zagaya da wasu cushion chairs guda hudu da kuma tebur a tsakiyarsu, waya ce kare a kunnensa kuma da lama dukkan abinda yake saurare daga cikin wayar mai muhimmanci ne.

Kuma jin shirun da yayi bai amsa ba yasa Faruk matso da kujerarsa zuwa karshem teburin yana barin inda screen din ™atuwar desktop din da ta kare fuskarsa. Kuma yanayin fuskarsa kadai ya gani ya san tare da wa yake wayar.

"Ka tabbata sunan da ya gaya maka kenan?"

Ma'aruf din ya tambaya fuskarsa babu wannan annurin da ya cika ta a ´an mintuna kadan da suka wuce wajen meeting din nan.

Aka sake wani bayanin a cikin wayar da yasa shi cije leSSensa sannan yace.

"Ku cigaba da rike shi kawai, zuwa gobe zamu yi waya."

Daga wannan maganar, Faruk ya riga ya san wa yake nufi ya kuma san ina zancen ya dosa, don shi yayi nasarar gano address din accountat din wadannan kamfanin da a baya suka gano cewar ta daliilinsu kamfanin Bakori yayi wannan asarar da aka kasa gano tushenta, wanda daga baya suka gano cewa kamfanin ne suka cuce su da alert din kudin karya bayan an gama yarjejeniyar komai, suka gabatar da shaidun biyan kuWin ba tare da kuWin ya shigo ba.

Don haka sanin cewa basu da hujjar zasu tunkare su kai tsaye yasa suka shiga neman accountant Win mutanen wanda yake kan aiki a lokacin da abin ya faru Mr. Ishmael Grahm, kuma da kyar ya iya gano address Winsa a jiya bayan tafiyar Ma'aruf din Jigawa, kums a jiyan tun ya a can ya kira shi ya shaida masa hakan kuma bai jira komai ba ya nemi ´ansandan da ya sani suka hada shi dana garin Delta inda suka gano mutumin anan yake suka je suka kama shi duk a jiyan, don haka a yanzu ya tabbata dasu yake wayar suna shaida masa wani bayanin.

Ma'aruf ya sauke wayar daidai lokacin da Faruk Win ya taso ya taho zuwa kujerar dake gabansa ya zauna.

"Me ya faru?" Ya tambaya yana kallon yanayin fuskar Ma'aruf din.

"Me muke dashi akan wannan Mr. Okafor din?"

Faruk ya girgiza kansa.

"Babu komai, har yanzu mutanen dana saka basu gama gano inda yake ba."

Sai kawai ya cillar da wayarsa akan tueburin dake tsakiyarsu kafin yace.

"Dole ne mu nemo mutumin nan Faruk, don duk amsar da muke nema tana wajensa, har yanzu na kasa gane yadda tsohon nan shi kadai ya shiga rayuwata da yawa haka."

"Me ya faru?"

Faruk Win ya sake tambaya yanayin kan fuskarsa na jira bai tafi ba. Kuma sai da Ma'aruf Win ya zura hannunsa a cikin gashin kansa sannan yace.

"Wahalar banza muka yi tayi Faruk, wannan dai Mr. Okafor din shi ya san komai, bai kamata ma mu cigaba da binciken ba bayan tafiyarsa, da ace mun dage wajen nemansa da watakila tuni mun gama da case din nan. Yanzu shi wannan mr. Ishmael din yayi musu bayani cewar Mr. Okaforn ne ya shirya musu komai a kamfanin, shi ya hada su da wani computer hacker daya turo mana da alert din kudin nan ba tare da kudin sun shigo a gaske ba, mu kuma a lokacin muka dauki kayan muka basu ba tare da anyi confirming ba, sai daga baya aka nemi kudin aka rasa shi yasa akayi wannan babbar faduwar.

Kuma har yanzu bamu da hujjar da zamu kai su kamfanin kotu tunda a baki ya shaida mana komai. Dole ne mu nemo shi Mr. Okaforn ya hada mu da wanda yayi musu aikin ko baza'a same shi ba a sami wata takarda da zata tabbatar mana da abinda suka yi wadda zasu tsorata su dawo mana da kudinmu ko kuma alkali yayi amfani da ita idan mun kaisu kotu a karbar mana ta hanyar shari'a."

Faruk ya haWe girarsa biyu waje guda yana nazarin kowacce kalma da Ma'aruf Win ke fada cike da zurfin bincike irin wanda ™wa™walwar sa ta saba akan abubuwa, kuma sai da ya gama fahimtar komai sannan yace.

"Idan haka ne B, idan wannan mutumin shi e a bayan komai me yasa yazo da kansa da a farko ya same ni yace zai shaida min abubuwan da muke nema? Idan har shine ™usar aiwatar da komai me yasa zai bayyana kansa da wuri har yayi kokarin fallasa sirrinsu kai tsaye?"

"Ni kaina abinda nake tunani kenan."

Ma'aruf ya fada yana lashe leSSensa na ™asa da yaji yana neman bushewa.

"Watakila a ranar da naje wajensa, da ban ga Hamida a gidan ba, da ace na zauna na saurare shi munyi magana watakila da tuni mun kawo ™arshen wannan maganar, da tuni mun gama da case Win nan komai yazo hannunmu."

"Dole akwai abinda yake a ™asa B, don ni yanzu jikina ma ya fara bani ba mu kadai muke neman wannan mutumin ba."

"Nima tunanin da nake yi kenan, don dole ne sai mun yi da gaske..."

Ya Wanyi shiru sai kuma ya Wago ya kalle shi da sauri.

"Ka san me za'ayi? Ka nemo mana appointment da Yakubu kawai. Kar ya wuce yau zuwa gobe."

Faruq ya zare idanunsa.

"What?? B Yakubu? Yakubu dai Yakubun SS? Ka san kudin da mutumin nan yake karSa kuwa yanzu?"

"Na sani, da kudina zan biya shi Faruk bada na kamfani ba, 'Cox a yanzu ban ga wata hanya da zamu iya neman mutumin nan cikin sauki ba tunda har su Salihu suka kasa, dole irin Yakubun zamu nema tunda dama shi irin aikinsa kenan, ko ni da kai muka tafi ba lallai muyi abinda shi zai yi ba."

Faruk ya gyaWa kansa a hankali alamun ya fahimta daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga can kan teburin, don haka ya miki yaje ya Wauka, kuma ganin number data fito a jiki yasa shi fadin.

"Excuse me." Sannan ya nufi kofa ya fita.

Kuma hakan ya tunawa da Ma'aruf missed call din Ishaq da ya gani a wayarsa shima har guda biyu, don haka ya jawo wayar ya shiga kokarin kiransa.

"Kana ina Kano ko Jigawa?"

Itace tambayar da Ishaq din ya fara yi bayan ya dauki wayar, kuma a lokaci guda kalmar Jigawan ta gifta masa da fuskar Amina, wani abu ya fada a zuciyarsa yana tuna masa da cewar rayuwarsa akwai canji a yanzu, a ™alla duk bayan wannan hargitsin yana da wani waje da zai samu nutsuwa.

A dazu lokacin da suna hanya, lokacin da ya sata ta kwafar masa wasu lambobi daga cikin wayarsa zuwa daya wayar, yana tukin yana kallonta, yana kallon yadda ta nutsu sosai tana aikin da ya saka tan,  kuma a wannan lokacin ne ™wa™walwarsa ta fahimtar masa cewa irin abinda yake ji a zuciyarsa duk lokacin da yahe asibitin sa na MMB-6 haka yake ji idan yana tare da ita, wani irin buWewa zuciyarsa take yi yana jin yana manta kowa dama komai sai iya abinda zai iya kawai.

Kuma ya san dalili, saboda ya fahimci duk abinda yace kawai shi take yi, duk abinda ya gaya mata shi zata yi ba irin Rulayya bace ita, Rukayya tana da ra'ayi tana da choices da expectations masu tarin yawa, shi yasa ko a lokacin aurensu da ya sa rai cewa zai samu nutsuwa a tare da ita, sai abubuwa suka canja, suka yi juyin waina don ita kullum cikin tuna masa da abubuwan da ya bari a rayuwarsa ta baya yake yi, abubuwan da yake a Ma'aruf Win da ta sanshi dasu wanda baya yi yanzu, shi yasa shi da ita basu taba daidaitawa ba, don yana son barin baya ne ita kuma tana jawo shi.

Amma Amina da a yanzu bata san waye shi a baya ba, bata san komai game dashi ba, bata da tunanin komai balle har tasa ran cewa zaiyi abu baiyi ba sai yake jin hankalinsa na kwanciya duk sanda yake tare da ita, zuciyarsa tana kara amsawa da abinda ya fara ji akanta tunda daga ranar farko da ya ganta.

"Mun dawo Wazu."

Ya amsawa Ishaq din dake jiran amsarsa a cikin wayar.

"Honeymoon din har ya kare?"

Ba shiri ya zare idonsa.

"Ni na gaya maka abinda ya kaimu kenan?"

"Sai ka gaya min? Wane sabon labari ne wai baka son tu™in dare, inaga har Kaduna munje ni da kai bayan isha."

Sai kawai ya koma da baya ya kishingiWa da kujerar da yake kai yana guntun murmushi, ya cusa yatsunsa Waya cikin gashin kansa.

"To ka gama aibata ni sai ka gaya min dalilin da yasa naga missed call Winka har guda biyu."

Daga cikin wayar Ishaq yayi magana da wani don alama tafiya yake yi kafin yace.

"B kana sane jibi ne zaman shari'ar nan?"

"Yes, na sake duba takardar, na sani."

"Kuma har yanzu kana nan akan bakan ka ba zaka nemo kowacce irin shaida ba?"

"Eh." Ya tabbatar yana gyada kansa.
Chapter 2 · 0% Book details