← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 87

Sashe 45

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi ajiyar zuciya a hankali tana sake kallon text Win da ta tura wa Jawad, ita kanta ta sani a bayan wannan neman da take masa kuma akwai wani abu kamar damuwa, damuwar da bata san dalilinta ba, a baya ta danganta hakan ne da shirunsa kawai, amma idan har zata yiwa kanta adalci ta san akwai wani abu ksmar kewsrsa a can kasan ranta, kawai tana danne shi da tarin dalilin da take bawa kanta a kullum.

Sai kawai ta mike tsaye iskar dake shigowa daga winfon dakin na kada lallsusar rigar baccin da 'ke manne a jikinta, idonta ya ksi ksn siffarta acikin mudubin Wakin, waye zai taSa cewa tayi aure har da haihuwar ´a? Ai ko don kyawunta ta san ba zata taSa asara ba, shi kansa Ma'aruf Win bata son zubar da ajinta a wajensa ne shi yasa ba za ta tunkare shi ba.

Taso ganinsa lokacin shari'ar nan amma tunda har abubuwa sun canja, jiran nasa ne a yanzu, shi zai jira har zuwa lokacin da zai kasa lissafa asarar da yake yiwa kansa, tayi murmushi a hankali, siraran lebbenta suna talewa, da ta samu Ma'aruf ko meye a cikin tata zuciyar zai manta da Jawad shima.

Sai kawai ta kada kanta tana sake yin baya da gashinta sannan ta nufi bandakin dake cikin Wakin.

***

*Abuja.*

"Bata da lafiya kamar yaya?"

Jawad ya tambaya tsaye daga kofar Wakin, yana kallon wata yarinya mai suna Kristy dake tsaye tana gaya masa hakan.

"Eh Yallabai, baya da lafiya tun jiya bai fita ba, as a matter of fact ma snce ne yau zata tafi gida."

Yarinyar da ta fadi haka cikin gurbatacciyar hausarta jin ceqar tambayar da yayi matan da Hausa ne, ya cije lebbensa yana kallonta, wani tunanin ya gifta a cikin kanta na sakanni biyu, tun jiya bai ganta ba ance masa tana aiki sai wata banzar inyamurar aka aiko ta kawo masa abincin da bai ci ba don mukullin mitarsa ya dauka ya bar gidan kuma bai dawo ba sai dare, a yau ya farka ne babu tunanin komai akansa sai na son ganinta, to kuma ta yaya zai zo ace bata da lafiya? A cire ma maganar tafiyarta a gefe, wannan bai san dashi ba kuma babu ta yadda za'ayi ya faru.

Don haka bai jira komai ba sai kawai ya gyaWa kansa sannan yayi gaba zuwa hanyar dakin dake bayanta.

Ba shiri yarinyar ta juya ta bishi da kallo, idanunta na zarewa da tsananin mamakin ganin ya nufi hanyar kofar shiga dakunan wajen, idan aka cire lissafin cewa tunda take bata taba ganin wani dan gidan walau mace ko namiji ya shigo bangaren nasu na masu aiki ba... Babu ta yadda kuma za'ayi ace an samu wani da ya shiga har cikin dakunan nasu... Saboda haka da ita da sauran ´an aikin dake harkokinsu a harabar wajen, suka bi bayansa da kallo har sanda ya taka kafarsa zuwa ciki.

Wajen dogo ne yana Wauke da kofofin dakuna kusan biyar don haka yaja ya tsaya ba tare da ya san inda zai shiga ba, muatan dake wajen duk suka tsugunna a lokaci guda suna gaishe shi, idanunsu na nunawa da mamakin da ba sai sun furta.

"A ina Zainab take?"

Ya tambaya kai tsaye cikin harshen turanci don ya san babu wani karin bayani, du duka sun san wacece Zainab din tunda babu wata bayan ita, ta farko ce ta nuna kofar dakin dake gabansu tana fadin.

"She's inside here sir..." (Tana cikin nan ranka ya daWe.)

Zainab na kwance akan katifarta daga can karshen dakin, ta kudundune a cikin hijabin sallarta, jikinta yayi zafin da babu makawa ta san zazzaSi take yi, amma ko kaWan ta san wannan ba damuwarta bace, taraddadin dake cikin ranta daban ne, kalaman da Hajiya Mardiyya ta kira ta jiya ta gaya mata su ke ta yawo a cikin kanta...

"Babu wani abu kika yi min ba Zainab, Allah ya sani naji dadin zama dake da kuma aikin ki. Tafiya zanyi zuwa wata kasar kuma zan debe tsawon watanni shi yasa nake ganin ya dace ki koma gida, tunda babu wanda zaki zauna kina yiwa aiki, kuma babu amfanin zamanki cikin kabilun nan, gobe zan saka direba ya mayar dake har garinku, ga kaya nan cikin wancan akwatin duk naki ne, ga kuma kudi nan isassau zan bawa Hajiya Mairo da ta kawo ki ta kaiwa iyayenki, nace ta roke su ayi miki aure Zainab, kar su sake tura ki wani wajen gwara ki tafi dakin mijinki ke ma ki samu kwanciyar hankali...."

Tana tuna kowacce kalma da ta faWa har yanzu a cikin kanta, tana jin nauyinsu da kuma irin razanarwar da suke yiwa zuciyarta... Komawarta gida a yanzu kamar yana nufin zuwa karshen rayuwarta ne ta sani, babu ta yadda za'ayi mijin mahaifiyarta ya yarda cewa ba wani abu tayi aka dawo da ita ba, idan kuma har yaji wannan sa™on na cewar ayi mata aure ta tabbata za'ayi Waya ne cikin biyu, ko dai ya karSe kuWin ya sake tura ta wani wajen ko kuma yayi mata auren da wanda ranta ba zai taba so ba kuma a wajen da zata wahala.

Tana kwance tana hango fuskar mahaifiyarta, Allah ya sani bata san me ta fito nema ba, ta san ba wani yanci ta taho samu ba amma haka kurum zuciyarta na jin cewa kamar zata koma ne da wani abun da zata samawa mahaifiyar tata sauki, kamar zata koma da wani abu da zai cire su daga kangin wahalar da suka faWa tun bayan mutuwar mahaifinta... Sai gashi mafarkinta dama burin nata yana shirin bajewa a iska, ba zata koma da komai ba sai wannan jakar da Hajiya ta nuna mata, jakar da ta san ko meye a ciki bai kai ya canja rayuwarsu ba.

Daga yadda take kwancen tana jin hayaniyar sauran matan dake zirga zirga a waje, ita kaWai ce a cikin dakin, kuma tun jiyan ´an kadan ne a cikinsu suka kula da yanayinta kuma tunda suka tambaye ta tace musu bata da lafiya shikenan babu wanda ya kara bi ta kanta, amma gwara su sau dubu akan Waya Sangaren data baro, inda anan anfi samu wanda suka tsane ta kuma suke mata mugunta da gaske.

Ta rufe idanunta a hankali tana jin yadda yadda zuciyarta ke rawa a jikinta, taradaddin barin wajen ne kawai ke kamata, yana ™arawa akan halin da take ciki. A lokacin kuma taji muryoyinsu daga waje suna gaisuwa, kowa yana fadin barka da zuwa yallabai, don haka ta bude idanunta da sauri cike da mamakin da bsi je koina ba wanda idanunta ya sauka akan mutumin da ya shigo cikin dakin, zuciyarta ta buga a ™irjinta.

Jawad, Jawad ne tsaye daga bakin kofar taba sanye da wasu kaya bakake, irin kayan da yake sawa a kullum wanda ba manya ba, wadanda suke zama a jikinsa daidai, kansa har da hula wadda ta dace da kayan, sannan a hannunsa akwai mukullin motar kamar fita zaiyi, Allah ya sani tun a jiya ta manta da lissafinsa kwata-kwata, taraddadin da take ciki har shi ya haWa ya shanye baki daya.

Kafin tayi wani yunkuri ya karaso har inda take, kafafunsa da takalmi na bi ta kan katifun sauran ´an dakin da basa nan, yayin da gefen idonta ya Wauko mata yadda wasu  suka shiga lekowa ta kofar dan karamin dakin wani abu da ya haddasa rikicewarta a lokaci guda don ta san ta riga ta shiga uku kenan a wajen mutane da maganganu kala-kala, jikinta ya shiga rawa a karkashin hijabin yayin da idanunta suka zare a kansa, amma babu alamar ya kula da hakan ya tdugunna a daidai gabanta idanunsa na kare mata kallo.

"Me ya same ki?"

Shine abinda ya fara faWa kafin ™amshin turarensa ya zagaye ta, kuma duk da rikicewar da take ciki, sai da amon muryar tasa yasa taji wani abu kamar tayi kewarsa tsakanin jiya da yau din kawai, don haka gaisuwar da take da niyyar yi bata fito ba, sai kawai ta girgiza kanta tace.

"Babu komai zazzaSi kawai nake yi... Na, na warke ma, kawai ban fito bane yau shi yasa ban kawo maka abincin ba...."

Bayanin da ta fara cikin rawar murya ya katse a lokaci guda da Jawad yasa hannunsa akan wuyanta, sanyin fatarsa ya ratsa har cikin kanta, jikinta ya tsaya cak, numfashinta ya ™ame a cikin wuyanta, ya sake motsa hannun nasa yana ™ara zura yatsunsa cikin wuyanta...

"Wane magani kika sha?"

Muryarsa ta sake tambaya, tana kokarin dawo da ita cikin haiyacinta, sai kawai ta haWiye wani abu a makogwaron ta a hankali sannan ta girgiza masa kai, bai dauke hannun nasa ba ya cigaba da kallon ta da idanusa daue kara rikita ta sannan yace.

"Maamah ta san baki da lafiya?"

So take yi ta tashi amma ko yaya bata son yin motsin kar hijabin jikinta ya zame, rigar dake jikinta yar ™arama ce, irin ta bacci da ™anwarsa ta bata, da ita ta kwana sai da taji sanyi da asuba sannan ta jawo hijabin ta lulluSa, don haka sai ta sake girgiza kanta a hankali idanunta na kallon kasa.

Kamar ba zai Wauke hannun nasa ba sai kuma ya cire shi a hankali m, tana jin yadda yatsun nasa ke barin fatar ta.

"Taso mu tafi."

Ya fada yana mi™ewa kuma maimaikon ya juya sai ya tsaya akanta yana kallonta, kallon da yasa ba shiri ta mike tana kokarin riko hijabin nata kotawanne bangaren amma saboda yadda jikinta yake rawa kafarta ta take shi garin mikewa ba tare da ta sani ya kuwa tafi kasa gabadayansa.

Zuciyar Jawad ta buga a lokaci guda da idanunsa suka gane masa kayan jikin nata, sai kawai ya juya da sauri gabaWayansa yayin da ta koma ta zauna da sauri tana ™o™arin sake tattaro hijabin nata.

"Idan kin shirya ina waje."

Ya fadi hakan ba tare da ya sake juyowa ba sannan ya nufi hanyar fita, tana ji wadanda suka tsaye daga waje na yi masa a sauka lafiya, amma tsabar kunya, takaici da kuma rawar da jikinta yake yi ta kasa ko Wagowa.
Chapter 45 · 0% Book details