← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 87

Sashe 70

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su kusan biyar ne ´an uwanta suka zo a yanzu, harda guda biyu da suke a Abuja, tun a daren jiya da ta gaya masu suka yi booking jirgi a safiyar suka taho... Kuma a cikinsu babu wanda ya ™aryata hakan saboda sun zo ne sun iske tarin hijjojin da ita Salamatun da kuma yaron dake kiran kansa da Jawad suka tanadar ta kowanne bangare, musamman babban al'amarin da ya ™ara girgiza kowa na cewar Jawad Win ya tashi ne a gidan Alhaji Bashir wanda yake ™anin mahaifinsa.

Komai ya faru ne kamar almara, kamar mafarki ko kuma wani labari da ba zai zama gaskiya ba, shi yasa a cikin lokaci kadan zancen ke ta tawo kusufa-kusufa a cikin danginsu har ma da waje, wadanda ke zaune a garin Kanon ma har sun fara zuwa don ganewa idanunsu, don Salamatu kiran kowa take yi, kowa ya kira ta zata ce yazo gidan saboda murnar dake cike fala ranta.

Ko ta zancen ™awar tata Kilishin da kuma matakin da ya kamata su dauka akanta na irin wannan zaluncin da ta haifar bata yi, sai yayyensu maza uku da suka gama shawara tare da Nasir ne sannan  suka yanke shawarar Waukan yansanda a tafi har inda Kilishin take, don wanda yake Babba a cikinsu ya Wauki zafi da yawa ta yadda ya rantse da Allah babu abinda zai hana su zama akan shari'ar.

Wayar da Aunty Bilkin take tare da wata ™awarta dake can wajen aikinsu ta kare daidai lokacin da  Hajiya Salamatun ta bude kofar dakin ta shigo hannunta Wauke da wata katuwar leda fara.

"Aunty Bilki Yaya Nura zai wuce yanzu."

Ta fada tana kallonta a cikin mutanen dake dakin, da mamaki a fuskarta tace.

"A'a, tafiya kuma ba dauka zasu bari ko zuwa gobe idan komai ya natsa, naji suna zancen za'a je a taho da Kilishin."

Sunan Kilishin da ta ambata ya rage fara'a a fuskarta kafin tace.

"Shi kaWai zai tafi, su suna nan anjima zasu je tare da Nasir, yace shi yana da meeting din wani contaract da zaiyi a yau."

Ta gyada kanta tana kallon ledar hannunta sai tace.

"Kaya ne nasa aka kawo masa Aunty Bilki, daga Kaduna yake kuma ashe bai zo da kaya ba."

Ta fada tana fito da set Win kaya guda goma Winkakku da wani yaronta ya bata lambar irin wajajen Winkin nan na yanzu masu sunan 'Wardrobe' da suke da kaya dinkakku nasu kyau da zaka je ka siya.

Yadikan dukkaninsu plane masu tsananin kyau da kalolinsu mabanbanta, kowanne anyi masa Winki mai kyau irin sealed din nan da maza ke yayi.

"Zai daWe ne kafin ya koma?"

Aunty Bilkin ta tambaya, sai ta girgiza kanta.

"Babu inda zai koma Aunty Bilki, tare zamu je kuma tare zamu dawo na gaya masa ne dai kawai ya kira Bashir din ya gaya masa komai."

Ta faWa da dukkan ya™inin da zai iya fitowa daga cikin zuciyarta, sannan ta mayar da kayan cikin ledar da cewar zata same shi ta bashi, caraf  sai Amira ta mi™e ta karSa da niyyar kai masa, don haka sai ta samu waje a kusa da Aunty Bilkin ta zauna, tana gaya mata mutanen da suka kira ta a waya suna cewa ayi mata barka.

Sai dai sam ba fahimtar ta sosai take yi ba, ba komai take ganewa a cikin bayanin ba, zuciyarta zagaye kawai take yi taba komawa daren jiya, daren jiya da suka zauna tare da Jawad suka fayyace komai game da al'amarin, tarin bayanin da yayi nusu na yadda yaji labarin komai a cikin kankanin lokaci da ma dukkan abunda ya faru bayan nan,sai dai ba komai ne yafi tsaya mata a rai ba illa sunan Bashir da ya kira a matsayin mutumin da ya rayu a gidansa kuma yake masa kallon mahaifi tsawon shekarun nan.

Mukaminsa da ya ambata na matsayin minister shine abinda kai tsaye ya tabbatar mata da cewar Bashir din da ta sani a rayuwarta ne, kanin mijinta Ibrahim wanda yake kamar yayansa, don tun kafin mijinta yayi aure shi yake da mata uku, tana tare da Ibrahim din kuma ya kara ta uku mai suna Mardiyya, ta san shi ta san matansa sarai! Don sun yi shiri da matarsa ta biyu Yagana. Bayan abubuwa sun lalace a tsakaninsu ne sai itama ta juya mata baya kamar sauran duka danginsa.

Ibrahim yana son haihuwa, sun fara samun matsala ne tun daga lokacin da ta haifi dan da akace musu ya rasu, sannan sai abubuwa suka lalace a tsakaninsu bayan an tabbatar da matsalar da ta samu a mahaifarta, matsalolin da suka kai ga rabuwar aurensu tun a wancan lokacin, kuma cikin wani ikon Allah sai daga ita har shi babu wanda ya sake haihuwa a dukkan aurarrakin da suka yi bayan nan har zuwa lokacin da Allah ya karbi rayuwarsa.

Tana tuna lokacin da aka gaya mata rasuwarsa, shekaru kusan ashirin da wani abu a baya, tana tuna iya zafin hakan da taji tun a wancan lokacin, zafin da bai kai wanda take ji a kirjinta yanzu ba, wanda take ji idan ta tuna cewa Ibrahim ya rasu ne yana tare da Wansa ba tare da ya sani ba, don a bakun Jawad take ji cewa anan gidan Bashir Win akayi jinyarsa kafin ya rasu...

"Kukan me kike yi kuma Salamatu? Idan na murna ne ai ya isa haka, idan kuma wani tunanin ne a ranki ki kauda shi gefe dan Allah, ki godewa Allah da ya nuna hakan tun da ranki kafin ki bar duniyar, ki sa a ranki cewa ya so ki da rahama ne tunda har ya baki wannan damar... Ga ki da ranki da lafiyarki da dukiyarki har da kwarinki, ba sai a lokacin da ba lallai ki iya komai ba... Gidewa Allah zaki yi ki kara gode masa Salamatu, ba kullum ne al'amari irin wannan ke faruwa a duniyar ba."

Sai ta sa hannunta tayi saurin goge gawayen fuskarta sannan ta daga kai alamun ta yarda hakan ne... Sannan ta dago daidai lokacin da jikokin Aunty Bilkin yayan wata yarta Muniba da itama ta karaso a lokacin suka taho da gudu suka rungume su... Ta ri™e yarinyar a jikinta tana kallon Muniban data shigo rike da karamin dan ta a hannu yayin da sauran ´anmatan dakin suka juya suna yi mata magana, kowanne fuskarsa dauke da fara'a...

Sai kawai ta furta kalmar Alhmdlilah a fili tana kara godewa Ubangiji ya daya azurta ta da wannan damar a rayuwa.

*

Jawad yana tsaye daga cikin Wakin, daga jikin windon Wakin inda aka saki farar liner dake jikin labulayen ta yadda daga yadda yake a tsaye yana hango wasu motoci biyu da suka shigo gidan mutanen cikinsu na ™o™arin fitowa. Hannunsa Waya na kare da waya yayin da guda Waya ke rike da labulen yace.

"Wallahi mutane take ta kira Haro, daga safiya zuwa yanzu gidan ya kusa cika... They are making me feel uncomfortable, yanzu muka rabu da shi kanin nata Nasir, yana gaya min cewa idan yansandan sun iso tare zamu fita zuwa gidan ita Waya matar, tsakanin jiya da yau Haro na rasa ma lokacin da zan zauna inyi tunanin cikin kaina..."

Daga cikin wayar Haro yayi dariya kafin yace.

"Kace ka zama wata sabuwar amarya kawai, but I'm really happy for you man! Wallahi kayi sa'a ba kowa ne ke gane irin wannan abun game da rayuwarsa kuma ya samu mafita cikin kankanin lokaci ba... You solved everything out kafin ma mu sani, don ni sai jiya da daddare ne da muna waya da Bello na office dinku yake ce min wai ka dauki hutu a lokaci guda yana fata dai lafiya sannan na san cewar ashe baka gari ma."

Jawad ya saki labulen ya taho cikin dakin yana kare wa kayan cikinsa kallo, a tunanin Haro komai ya faru ne cikin sauki, a lokaci guda ba tare da wani bata lokaci ba, amma shi ya sani halin da ya shiga da kuma wuyar da ya sha a iya wannan Wan tsukin,  idan za'a rarraba ta a zuciyar wani zai Wauki watanni kafin ya iya kai ™arshensa.

Shi kadai ya san abinda yaji shi kuma shi kadai ya san abinda ya fuskanta a cikin zuciyarsa da ma jikinsa, sannan ga tasirin dukkan abinda ya faru jiya, na yadda ya samu abinda baiyi zato ba bayan sun bashi tabbacin da shi kansa ba zai iya musantawa ba. kusan hotuna goma Hajiya Kilishi ta dauko masa na mahaifin nasa da takira da sunan Ibrahim Shanawa, kuma tun a hoton farko yaga kamar ya san fuskar kamar ya gane shi duk da cewa suna ta zuzuta kammaninsa dashi.

Sai da ya fara yi mata bayanin inda ya taso sannan komai ya fito fili, wani ikon Allah da kuma wata sabuwar isharar ta fahimtar dashi cewa a tsawon rayuwar da yake tunanin ya shafe a hannun wasu mutane, ashe ba wasu bane, a cikin danginsa yake, a tsakiyarsu ma tunda tun kafin hawan Alhaji Bashir matsayin minista gidansa yake a matsayin centre guda ta family dinsu, kusan kowa yazo zai samu wajen zama babu takura, shi yasa a yanzu da yake matsayin ministan ´an aikin dake tafiyar da al'amarin gidan su kansu wajensu daban.

Bai kira kowa ba, bai kira su Hajiya Mardiyya ko kuma wani a gidan ba har yanzu, yafi son sai ya gama tara hankalinsa waje guda tukunna, yafi son sai ya saita iya abinda ke gabansa a yanzu, don ya sani gaggawa ba zata haifar masa da komai ba.

Ya ajiye wayar hannunsa a gefen gadon dakin sannan ya nufi ™ofar toilet ya buWe... wanka yake so yayi ya canja kayan jikinsa shi yasa yake ta jinkirtawa don ta gaya masa cewa zata sa a kawo masa wasu, hoton fuskar Zainab ya gifta a ransa a lokacin, ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha wanke masa toilet, ta haka ya fara gane ta, ta haka ya fara gane cewa an canja masa mai gyara masa daki kafin ma ya fahimci wacece ita.
Chapter 70 · 0% Book details