← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 87

Sashe 68

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abu ya wuce a makogwaronsa da bai san meye ba, yayin da yake jin tasirin kowacce kalma da ya furta da kuma yanayin tare da tashin hankalin dake zagaye dasu na haddasa wani abu a ™irjinsa da bai san meye ba, kuma a lokacin ne ya juyo ya kslle ta, har yanzu bashi take kallo ba, kanta a juye ysketana kallon waje, idanunta auna tafiya zuwa wani nisan da bashi da karshe, idanunta da har yanzu basa nuna masa kamanin Mamin da ya sani, baya ganinta a tare da matar dake gabansa kwata-kwata.

Har yanzu a gaban bishiyar motar take, bishiyar da ta shiga cikin wani Sari na rayuwarsa, Sarin da ya riga ya zama tambarin da a kodayaushe a kowanne waiwaye shi zai fara kalla a rayuwarsa.

˜arfe shida na safiya, ´an mintuna kaWan bayan sallar asubahi lokacin da suka ™araso wajen, yana tafiya ne da karfin gudun da tun daga nesa wani magidanci dake tahowa akan keke daga hanyar shiga kauyensu ya hango ta, hasken fitilun gaba ya fara gani kafin kurar dake bin ta a baya ta cika idanunsa.

Ba shiri ya dawo da idanunsa kan gonakin dake gaba, gonaki kusan biyar dake dauke da sabbin shukoki da suka fara fitowa, kuma kafin ya gama lissafin abinda ke shirin faruwa, motar ta karaso ta zarce ta cikinsu da tsananin gudun da tayoyinta har dagawa suke saboda tudun kunya-kunya dake gurin, tana wucewa tayoyinta na murje shukokin da matukin cikinta baya ko ganinsu balle yaji alamunsu daga ciki.

Hannunsa akan sitiyarin suke kawai yana danne shi wajen kara nausawa ciki, dogwayen bishiyun da idanunsa ke gani kadai yake iya kaucewa bayan haka baya ganin komai, baya jin komai sai tarin maganganun dake tarewa a cikin kansa suna sake dawowa.

Maganganun dake sa wa tun yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa, yana jin huci da kuma dumin wani abu na ratsa kirjinsa zuwa cikin idanunsa, har ya daina.... Ya zama baya jin komai... Baya jin komai sai sautin muryarta dake fitowa daga cikin wadannan CD's din a lokacin da yake tsugunne a gaban  computer Abdurrahim.

Yana tuna kowacce kalma da ta shiga kunnensa yana tuna su bi da bi saman kwakwalwarsa na tsara masa su daki-daki a yadda al'amarin ya faru a yadda komai ya kasance... Sannan bayan haka daga can ™arshen kansa muryar Awwalu ce ke amsawa, dukkan bayanan da zai iya tunawa yaji lokacin da yake shaidawa su Baffa tarin abubuwan da suka daWe suna binne su a cikinsa.

Ya sani cewa zuwan Awwalun da kansa a wannan lokacin da kuma abubuwan da yake fada abu ne mai mutukar mamaki duba da tsawon lokacin da suka shafe suna nemansa, amma mamakin sautin muryar Mamin da kuma tarin abubuwan da dake fitowa daga muryar tata ya shallake dukkan wani abu a cikin kansa bayan hakan duk da cewar bayanan Awwalun wani abu ne da ya ™ara basu dukkan tabbacin da zasu nema, don Allah ya sani zai iya ™aryatawa.

A wannan lokacin zai ce ba haka bane, zai ce dukkan abinda yaji karya ne... Zai yarda da dukkan wata hujja da zata gaya masa cewa impersonation Win Maminsa aka yi, Mamin da ya sani mai ™aunarsu ce, zuciyarta a buWe take ga kowa, ba zata taba ko iya hada hanya da wanda zai cuce su ba balle ta saka hannu, balle kuma ace itace ja gaba wajen faruwar munanan abubuwa da yawa a rayuwarsu....

Sai dai me? Bai ma yi wannan fatan ba, baiyi ma yi wannan tunanin ba aka tafi har zuwa gaSar da komai ya tabbata, komai ya tabbata ta sigar da basu da wata kafa ko kuma hujjar ™alubalantar abinda suka ji.

Kuma ba ga shi kaWai ba, ya sani dukkansu a yanzu dalili zasu so sani, dalilin da yasa tayi hakan, ta aikata tarin abubuwan da baya jin ko akan fatar bakinsa zai iya furta su, dalilin da yasa ta shigo rayuwarsu tun farko ma, dalilin da yasa basu taba ganin komai ba sai tarin murmushi da kuma dimbin kaunar dake nunawa akan fuskarta mai kaifi, kaifin da take amfani dashi tana huda zuciyoyinsu a tarun lokutan da ko sau daya wsni a cikinsu bai taSa waigawa yaga  makamin da hannayenta ke rike dasu ba.

Wani? Akwai wanin da ya dace ne bayan shi? Akwai wanin da ya kamata ace a cikin Winbin shekarun da ya rayu tare da ita ace ko sau Waya idanunsa ko kuma tunaninsa basu taSa haska masa wani abu da ya kamata ya Worawa ayar tambaya akanta ba?

Hannunsa Waya ya shiga cikin gashin kansa a lokacin da Wayan ke kara danne kan sitiyarin suna ™ara nausawa cikin dajin, a cikin hannunsa ya shake likitan da aks ce ya jagoranci ´ar karamar tiyatar da akace anyi mata an tabbatar da makantar idanunta, kuna ba'aje koina ba a cikin hannun nasa likitan ya gaya masa cewa ita ta nemi da yayi mata hakan ya fadawa kowa cewa ta makance bayan tayi masa alkawarin tarin wasu kuWaWen da ba zai iya ™in tayin ba.

Kuma daga idanunsa kaWai ya san ta sani, ta san ya san komai, tun kafin ma ya faWa shi yasa bata ce komai ba har yanzu, har suka ™araso wajen da bai manta hanyar ba, don ba zai taSa manta ta ba, yazo fiye da sau goma kuma a zuwan farko ne kaWai yayi bilinbituwar da ta Wauke shi awanni kafin ya iya gane ba wajen, bayan haka baya jin ko a mafarkinsa ya taSa kauce hanya.

A lokacin da suka ™araso, idanunsa sun  tsaya akan bishiyar da kuma gudun da motar ke yi a cikin hannunsa, yaji wani abu na yawo a cikin kansa kamar wancan lokacin, shekaru goma da suka wuce, lokacin da hannayensa dama duk wani abu mai tsini a cikin kansa suka kasa tsayar da motar dake nufar bishiyar da yake kallo a yanzu, da sanda suka tafi suka dake ta, suka dake ta a yanayin ba zai taSa fita daga kansa ba...

Sai kawai ya danna birkin motar a yanzu da ™arfi, da ™arfin da ya fitar da sauti mai ™ara daga waje, ™arar ta karaWe cikin dajin zuwa nisan da ba zai iya kintata ba, kuma duk da karfin birkin, motar bata tsaya ba sai da taje dab da bishiyar, dab da ita sosai ta yadda bai fi tazarar taku biyu kawai ba a abinda ya rage

Tayoyin na tsayawa ya buWe ™ofar ya fito, ya fito ya buWe ta baya idanunsa na kaiwa kan Hajiya Kilishin da har yanzu bata kallonsa, kanta na juye daga gefe tana hangen wani wajen daban, da tafiyar da suke yi da ma karfin birkin da ya faru a yanzu babu daya da ya canja ta daga mazauninta, idonsa ya tsaya akan fuskarta, awanni kadan da suka wuce, awanni da basu fi kirgen yatsunsa ba, duniyarsa a tsaye take game da rashin lafiyarta, yana jin komai ya birkice masa yana jin rayuwar ba daidai take tafiya ba tun kafin ma ya san sakamakon abinda ya same ta.

Amma a yanzu gashi tsaye a gabanta sai dai a yanzu bashi Win bane, ba Ma'aruf Win da yake a jiya bane, ba Ma'aruf Win da yake a shekarun baya bane... Baya jin kansa a matsayin kowa da kuma komai, jin sa yake a wani sabon mutum daban, sabon mutum Win da babu komai a zuciyarsa illa tarin abubuwan da yaji ya kuma sani daga daren jiya.

A karo na farko, yaji wani abu kamar kwalla na shirin ziyartar idanunsa, sai kawai ya juya ya koma mazaunin direban ya juya ya buWe booth Win baya na motar... idanunsa suka tsaya akan rediyon motar yayin da yake jin zuciyarsa na girgizawa tamkar yadda yatsun hannayensa ke yi, sai kawai ya danna ya play buttun a jiki kuma a take sautin dake fitowa ya karaWe kowacce speaker dake cikin motar.

_"Ka yi masa magana kawai Awwalu, na yarda zan bashi hakan, babu abinda ba zan bayar ba saboda wannan aikin... Ya kamata ka sani tun da har na kashe Jamal babu abinda ba zan iya ba akan cikar burina..."_

Tashin hankalin da ya daki tsakiyar kan Hajiya Kilishi a lokacin ba abu ne da zata iya misaltawa ba, tun daga lokacin da ta farka a daren jiya, lokacin da ta gama jin hirar dukkanin abinda ya same ta, ta daWe kwance a wajen tana tsara hanyar mafitar da zuciyarta ke sa™a mata, ta da yadda zata wanke kanta a idon kowa ta kuma fita daga ™ullin ´ansandan nan... Kuma tsarin nata ta tafi daidai a cikin kanta, ta ™irga komai ta fitar da dukkan hanyoyinta kamar yadda ta saba, hatta kuWin da zata kashe ta lissafa da kuma yadda bayan hakan tsarinta zai cigaba da tafiya daga inda ta tsaya.

Ta sami wani likita da ta farar-Waya ya amince da bu™atar ta jin makudan kuWin da a take tayi masa alkawari. Tana tuna murmushin da tayi bayan fitarsa, murmushin jin dadi da kuma jinjina wa kanta na yadda a kodayaushe mafita ke zywar mata, sai dai me? Ashe bata sani ba wannan murmushin shine na karshe da zata yi a wannan karnin watakila har ma da me zuwa a gaba... Don wadannan lokutan na jiya ta sani cewa har abada su zata lissafa a matsayin lokuta na ™arshe da suke daidai a rayuwarta.

Tana iya tuna maganganun da suka yi da Baffa kafin nan, sun shigo wajenta shi da Baba Usman, kuma dukkan maganganun da zasu kwantar da hankalinta su suka zanta, suna tabbatar mata da halin da kowa a can gida yake game da ciwonta da kuma cewar ta kwantar da hankalinta abubuwa zasu daidaita, wasu maganganu da suka ™ara saita hankalinta waje guda bayan tabbatarwar da tayi cewa abubuwa suna nan a yadda ta san su har a lokacin.
Chapter 68 · 0% Book details