← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 87

Sashe 48

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryarta ta fito da sautin da taji da ace dare ne zata iya tayar da hasken taurari su haska masa fuskarta sosai don ya fahimce ta, ta fadi hakan sannan ta janye kanta a hankali zuwa baya tana kallon fuskar tasa, kallonta yake yi kawai babu alamun zai ce wani abun amma duk da haka tana iya jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar tata.

Komai fushin da zaiyi da ita, bata jin zai karasa har cikin zuciyarsa, ita mai rangwame ce akanta ta sani, sai kawai tasa tafin hannunta duka biyu ta rike kowanne gefen fuskar tasa.

"Ba fushi nake yi ba, me yasa kike bani hakuri?"

Ya yanke shawarar fada muryarsa na fitowa da wani irin amo da bai yi nata dadi ba, amon da yasa babu dalili a lokaci guda taji hawaye ya cika idanunta, bai fahimce ta ba har yanzu, bai fahimci dukkan bayanin da tayi masa ba, bata taSa tunanin kuma zai kasa fahimtar tata irin haka ba.

Zuciyarta ta matse da tunanin irin fassarar da yayi mata tun kafin ma ta sani, tana jin wani abu na narkewa a cikin jikinta kamar ™arfen da ake ™onawa a cikin wuta, wannan ya™inta ne ta daWe da gayawa kanta hakan, babu wanda ya san wannan manufar tata a duniya bayan shi, ko Amma bata furtawa ba, shi kaWai Win ne ta san ya zama dole ya sani kuma shi kaWai take tunanin zai fahimce ta su rufawa junansu wannan asirin duk da bai san komai ba, amma idan har yana yi mata wani tunani na daban nasarar me taci kenan?

Sai kawai ta girgiza kanta tana cigaba da kallonsa.

"Da zan iya zan tattaro komai a duniyar nan Sugar, zan tattaro du gabaWaya in jera a gabanka don su zama shaida cewar ba zan taSa yin wani abu da na san zai bata ranka ba, so nake kawai ka fahimce ni, ba zaka gane yanzu ba na sani, kuma lokacin da zaka gane Win ma na tabata ba sai na sake yi maka bayani ba.

Ro™on ka kawai nake yanzu ka bani haWin kanka, bayan shi bana son komai Ma'aruf, kaine inuwata kuma kaine tallafi na, bani da wani mai kare ni a duniyar nan da ya wuce kai, bani da wani da zan dogara dashi a duniyar nan bayan ubangiji da ya wuce kai, kuma ba zan taSa daina godewa Allah ba da ya kawo min kai cikin rayuwata a lokacin da ban tsara ba kuma ban taba tunani ba, I will always love you in a way that I will never hurt you..."

A yanzu bata jin wannan kwallar data taru a cikin idonta, wani abu take gani a idanunsa take kuma ji a jikinta kamar kwarin gwiwar da ya sata ™arasa maganarta.

"Zamu haifi babyn nan cikin kwanciyar hankali insha Allah Sugar, babu abinda zai faru, ka cire tunanin komai a ranka dan Allah ka yarda dani, kamar yadda kake yarda da Faruq Win nan."

Sai kawai ya girgiza mata kansa a lokaci guda sannan yace.

"Kar ki taSa haWa kanki dashi Babydoll, matsayinki da nasa daban ne a cikin zuciyata, there's no way ma da kuka zo kusa."

Ya fadi hakan yana matso da ita jikinsa, kusa dashi sosai ta yadda take jin ™arar bugun zuciyarsu ya haWe waje guda akan zare guda, sanyi da zafi, mai nauyi da mara shi da kuma siririn da ya yake haWewa cikin dan'uwansa.

"Na yarda dake Noor, na yarda I'm just curious ne, abubuwa be suke neman haWe min haWe min waje Waya matsalar office da kuma..."

Ya faWa hannunsa na kokarin lalubo zip din rigarta a hankali, wani abu da yake son wasa dashi a kodayaushe. Sai kawai ta girgiza mata kanta a hankali.

"Babu ruwan gidan nan da office my Ranger Handsome, ka bani damar da zan sa idan ka dawo wajenmu kaji kamar wata duniya daban ka shigo, kamar mun koma Mars ne mun bar musu duniyarsu da hayaniyarsu."

A lokaci guda murmushi ya suSuce a fuskarsa yana kallonta.

"Really BabyDoll? Kamar me kenan?"
Ya tambaya yana Waga mata gira Waya, sai ta cije lebbenta na ™asa alamun tunani kafin tace.

"Zamu zama iyaye nan da watanni masu zuwa..."

"Alhmdulilah." Ya katse ta yana gyaWa kansa.

Bata tsaya ba ta cigaba.

"... Kuma yau muka sani, yau aka gaya mana... So let's celebrate!"

Ya ™ara gyaWa kansa murmushinsa na ™ara yawa, yayin da a cikin kanta take godewa Allah ganin yana dawowa yanayinsa na Ma'aruf Win ta.

"We should BabyDoll, me kike so muyi yanzu? I think ina da two hours kafin in fita."

Ya fada yana Wora goshinsa akan nata, hancinsa na taSa saman nata.

Ta sake cije leSSenta tana kallonsa sannan ta girgiza kai, duka fuskarsu ta girgiza a tare.

"Yanzu lokaci yayi kaWan, kayi breakfast ka fita, celebration Win zai fi daWi da daddare."

A lokaci guda hannunsa ya tsaya da taSa zip din rigarta da yake yi, ya janye fuskarsa daga tata yana kallonta sosai, da idanunsa da take jin kamar yana sace ruhinta daga jikinta, har a lokacin da murmurshi a fuskarsa yace.

"Tabbas zai fi daWi sosai Babydoll..."

Ta gyada kanta itama.

"Zan nemo restaurant hadadde wanda suke da fitulu sosai 'cox we are going to take pictures na tarihi wanda zasu zauna har tsawon shekar...."

Bata ™arasa ba lokacin da Ma'aruf ya kyalkyale da dariya yana Wora kansa a gefen kafadarta ta dama.

"Menene? Me ya faru?"

Ta tambaya tana murmushin da bata san na meye ba yayin da hannunta ke kokarin  Wago da fuskarsa. Tana jin yadda jikinta ke girgizawa da dariyar da yake yi.

"Na kasa ganewa, wai menene?"

Ta ™ara faWa sanda tayi nasarar dago da kan nasa, ya kalle ta sosai yana girgiza kansa kafin yace.

"Babydoll da kika ce celebration kuma kika ce da daddare, abinda nake hangowa daban..."

Bata san lokacin da ta ture shi ba tana kiran sunan sa, sunansa gabaWaya.

"Ma'aruf Mansour Bakori..... ka dinga tunani irin na mutane a cikin kanka dan Allah."

Ta fada tana ™o™arin mi™ewa, bata je koina ba kuwa ya jawo ta suka koma kan gadon gabaWaya.

"Zo ki koya min irin yadda ake yi tunanin mutanen..."

Abinda ya faWa bayan hakan ya saka ta kyalkyala dariya tana cusa kanta a cikin wuyansa, abinda ya cigaba da faWa kuma ya sata faWin.

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un... Ma'aruf!"

Dukkaninsu suka kyalkyale da dariya, kuma abinda dukkaninsu basu sani ba shine, za'a Wauki wata tazara mai tsawo kafin sake faruwar irin wannan ranar a rayuwarsu!

****

*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*

Ta san dakin, amma idanunta suna kallonsa ne kamar bata taSa ganin sa ba, idan ma akace ta ™irga bata san sau nawa zata kirga adadin data share kuma ta gyara shi ba, shi kaWai ne a ™asa bayan falon, kuma tasha tambayar kanta dalilin da yasa aka hada shi har da komai da komai alhali mai wajen baya amfani dashi ko kaWan.

Bayan haka kuma zuciyarta tasha hasko mata yadda zata ji daWin kwanciya akan gadon da yake dakin, don kalar labulayen cikinsa da kuma zanin gadon Wakin da suke suke dukka kalar yalo, suna faranta zuciyarta haka kawai, tana jin kalar na shiga idanunta da tasirin da take jin kamar tana samun ´ancinta ne a ciki, kamar zata samu wani fiffike da zai mi™ar da ita sama ta tsaya da kafafunta irin yadda take fata a kullum.

Amma yau da take tsaye a cikin dakin rike da ledar kayan dake hannunta bata jin dukkan waWannan abubuwan, bata jin komai, zuciyarta fayau take kamar fuskarta.

_"Zainab zaki aure ni?"_

Sune kalaman dake maimaitawa kawai a cikin kanta, amonsu take ji yana ratsa ko'ina na tunaninta, tana ji kamar sha™uwar data kwace mata a lokacin zata sake dawowa, don sha™uwa kawai ta dinga yi yayin da idanunta ke ™ara zarewa akansa, kuma bai sake cewa komai ba sai kawai ya kai hannunsa ya shafa kansa sannan ya juya ya bar wajen.

Bai sake cewa da ita komai ba har suka gama dukkan abinda za'ayi a asibitin ya karSo mata magani, binsa kawai take yi tana so ta tsayar da sha™uwar da ta kasa tafiya, ya barta a mota ya shiga wani waje da ta kula cewa magunguna ake sayarwa, kuma bayan ya dawo ne ya shigo motar ya miko mata robar ruwa har a lokacin bai sake cewa da ita komai ba.

Tana tuna yadda ta shanye ruwan gabadaya kasancewar ba wani girma ne dashi ba amma har a lokacin shakuwar bata tafi ba, sai kawai taga ya sake miko mata wata robar daga cikin ledar maganin, a lokacin har sun fita daga cikin asibitin sun hau titi. Kuma ga wani mamakinta ba gida suka taho a lokacin  kamar yadda ta zata ba, idan zata tuna ma taga sanda suka wuce hanyar gidan suka tafi kai tsaye har wajen aikin sa.

Wajen da ya ™ara rikita ta, ya kara sawa ta raina kanta ta san cewa ita ba komai bace a duniyar nan, tun daga waje ginin wajen ya daki zuciyarta har suka shiga ciki, don bai bata wani zabi ba yace ta biyo shi, suka tafi har office din wata mata da taji yana kira da Aunty Mary, dattijuwa ce amma kuma arniya, ta saka kayan da basu matse kayion jikinta ba sannan tayi kitson ™arin gashi.

Tana da tsananin fara'a da kuma kirki, anan yace ta zauna zai je ya dawo, kuma bayan ya tafi haka tayi ta mata magana duk da ta fahimci ba ganewa take sosai ba, don idan ma zata gane Win, taraddadin dake cikin zuciyarta na tunanin Hajiya Mardiyya da nemanta da za'ayi ba zai barta ba, a haka ta zauna cikin tunani da tsoro har sanda wani ma'aikacin wajen ya shigo rike da leda mai dauke da abinci da kuma magungunan da aka siyo.

_"Hajiya ga shi yace ki ci abincin kuma ki sha magungunan."_

Tana tuna fuskar mutumin da ya kira ta da Hajiyar, zata iya rantsewa zai kai sa'an mijin mahaifiyarta da ta baro a gida, amma kamar bai ga kankantar ta ba ko kuma dogon hijabin data zura wanWanda basa shaida wani abu na Hajiyar da ya kira ta.
Chapter 48 · 0% Book details