← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 87

Sashe 28

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban gane ba, kin ga yarinyar bayan tsawon kwanaki da Sacewarta, har a gaban alkali an baki ita kuma kice min kin dauke ta kin sake mayar da ita hannunsa? To meye hikimar Rukayya?

Na zata shi kike so, shi kike so ya dawo rayuwarki, kuma Allah ya mallaka miki ´ar da ta dalilinta zaki hillace shi ya dawo gareki, amma sai ki Wauke ta ki mika masa ita ke ki koma gefe?

Wane irin tunani ne wannan Rukyy? Wane jahilin ne yace miki..."

"Mahaifiyata ce."

Ksi tsaye Rukayyan ta katse kawarta mai suna Hanan dake wannan zancen ta cikin wayar.

"Kin san ni ba shashasha bace Hanan, tunda kika ga nayi hakan,kin san da dalili,kuma shi ya kamata ki fara tambaya ba ki shiga ™o™arin aibata ni ba."

Ba ganinta take yi ba, amma zata rantse Hanan Win ta taSe baki wani abu da yake al'adarta kafin tace.

"Ni ba aibata ki nake yi ba,amma koma meye shirin naku ina tabbatar miki wannan shirme ne,da kin tambaye ni tun farko da ba haka..."

"Ke na tambaya ai tun farko Hanan..." Ta katse ta muryarta na dagawa.

"Ke na tambaya tun kafin in gama iddar auren Ma'aruf, zuciyata tayi nadama tun a sannan, amma ke kika ce kar in bashi hakuri don in koma Hanan, kuma ke na tambaya kika bani shawarar auren Alhaji Ahmad, kuma ke na tambya lokacin da su Maamah suka hada ni da Jawad, ke kika nuna min cewa in biye masa muyi wannan rayuwar zan manta komai, amma na manta din Hanan? Sannan ke na tambaya kika hada ni da Mary ´ar aikin Hamida... Hanan ki gaya min a cikin tarin wannan shawarwarin naki wanne ne ya juye zuwa alkhairi? Wanne ne ya juye zuwa alkhairin da har yanzu nake mora?"

"Ban gane ba Rukayya, me kike nufi? Me kike nufi dani?"

Muryarta ta fito ne da harzukin dake keto wayar yana dukan kunnen Rukayya.

"Ina nufin ke ba ™awar arziki bace Hanan, na fahimci babu wani abu mai kyau da ya taba faruwa dani a tsawon zama na dake."

Kuma daga haka, bata jira komai ba ta katse wayar, ta rike ta a hannunta tana kallon adadin mintinan da suka Wauka a wayar.

Da dukkan maganganun da ta furta a wayar nan ta kwana a ™irjinta, dasu ta kwana suna yawo a zuciyarta, don a cikin tarin tunanin dake yawo a cikin kanta ta iya nemo wannan kawai ta jera shi daya bayan daya ta fitar da karshensa, kuma abinda bata gama sani ba shine bayan Hanan, mutane nawa ne kuma bata yi sa'ar kasancewa dasu ba a cikin rayuwarta.

Hannunta ya fita daga bangaren kira na wayar tata, ta shiga wajen sakonni, bayan na banki, sunan Jawad ne a kasa, sakon sa na karshe daya tura mata kafin su yi wannan haduwar.

_I madly love you Barbie, me yasa kike hukunta ni? Pick my call please..._

Haka kurum taji a ranta cewa shirunsa a yanzu yana da nasaba da wani abu, Jawad mai naci ne, mai wani irin rufaffen nacin da baya ji kuma baya gani idan har ya dora ransa akan wani abu, ta san wannan ba tun akanta ba, tun akan aikinsa don hakan shine babban abun da yasa cikin ´an shekaru kadan matsayinsa ya kere kowa a wajen, to ta yaya don kawai tayi masa wannan bayanin zai ha™ura komai ya cigaba da tafiya daidai?

Wayarta tayi kara tun kafin tunaninta ya kai karshe, Mahaifiyarta ce Hajiya Nafisa, ta Wauka daga haka tasa a speaker.

"Ki sauko kasa, muna magana ne akan wadda zata je gidan."

Wadda zata je gidan, ba sai Maamahn ta fasa ba, wadda zata je gidan tana nufin gidan Ma'aruf, yarinyar da zata je ta kwance asirin nan, asirin da kamar yadda suka tsara komai a yau ba sai gobe ba aikinsa zai fara, Ma'aruf zai tsani koma wacece yarinyar dake cikin gidan nan a matsayin matarsa, tsanar da a cikin kankanin lokaci zai rabu da ita, don ta riga ta san ko waye Ma'aruf, idan baya son abu baya son sa har cikin ransa kuma babu wanda ya isa a duniyar nan ya canja ra'ayinsa game da hakan hatta Baffa kuwa, shi yasa shi kansa Baffan baya saka baki akan al'amarin wani hukunci da ya yanke.

Sai kawai tayi wani murmushi mai fadi tana hango yadda rayuwa zata maida ita bigiren da ta yarda babu kamarsa duk duniyarta.

Ta yi mu'amala da maza da yawa tun kafin aurenta, amma babu wanda ya kamo kafar Ma'aruf a cikinsu shi yasa ta dage har ta aure shi a sannan, kuma bayan zuciya ta ruWe ta ta fito, har yanzu bata ga wanda ya kama kafarsa a komai ba... Jawad yana ji da kansa wajen iya kulawa da kuna tarairayar mace, amma ta tabbata zai zubar da dukkan makamansa idan da zata hasko masa kwana Waya kawai a rayuwar aurenta da Ma'aruf kafin abubuwa su canja a tsakaninsu.

Wayarta ta sake ™ara, Maamah ce, sai kawai ta sake wani murmushi mai fadi tasa hannunta duka biyu tana gyara dogon gashinta zuwa baya.

Bata san wane irin zama Ma'aruf ke yi da sabuwar matarsa ba, amma koma wane iri ne, yau zata zama rana ta ™arshe da hakan zai zo ™arshe.

***

"Meye wannan?"

Ma'aruf ya faWa a hankali yana laluben gefen fuskar Amina dake tsaye a gabansa, a jikin wardrobe Win dakinta ya same ta, tana kokarin samowa Hamida kayan da zata saka sakamakon bata nan jikinta da tayi da hodar ta fasa gabadaya kuma ta zube a jikinta, duk yadda ta kai ga kwashe kayan kwalliyar nan bai hana Sata kayan nata da take gudu ba.

Dawowarsa kensn daga cikin gida, don can ya fara shiga baysn ya dawo, bata ssn wajen wa yaje ba amma tana tunanin wajen Baffa ne don yau ma yans gida. Šazu bayan gama wayarta da Amma, Ssmirah tazo sun shiga sun gaishe shi, har da Hamida da taki zuwa wajensa ta makale a hannunta, wani sbu da ya taba zuciyarta a lokscin yayi mata dadin da kuma yabawa kanta na cewar yarinyar ta fara sabawa da ita.

Kuma sai da numfashinta ya katse a yanzu daya zura hannun nasa gefen fuskarta, tana jin yadda yatsun nasa suka ratsa kunnenta, sanyin jikinsu na bi ta kan fatar ta.

"Šan kunne ne, baka sanshi ba?"

Ta fada tana kallon cikin idanunsa hannunta rike da kayan da ta dauko, ya gyada kansa a hankali yana cije lebbensa kafin yace.

"Na sanshi, kawai bana son shi ne."

"Saboda me?"

"Saboda damuna zai dinga yi."

Sai da ta dan tsaya tana kallonsa kafin tace.

"Ta yaya zai dame ka?"

Bai ce komai ba ya fara kokrin zare shi a hankali, ya karkato da fuskarsa dab da tata yana kallon ta yadda zai cire kuma bata ce komai ba ta tsaya kawai jiran taga abinda zai yi, ya cire na bangaren dama, sannan ya karkato da kansa daya gefen ya cire na hagun shima, ya hada su a hannunsa sannan ya kamo nata daya a hankali, na hagun da bata rike kayan dasu ba, ya bude tafin hannun ya dora mata su a ciki.

"Please in dai saboda ni kike sawa ki daina, bana son su, takura min zasu yi 'Cox bayan kafafunki, I like this curve of your body best."

Numfashinta ya tsaya cak a ™irjinta yaki fita yaki shigactsawon wasu da™i™ai, dama kafafunta burge shi suke? Inalillahi! Ai bata taba tunani ba, ko lokacin da ta saka wannan yaluwar rigar sai da tayi ta ayyana yadda yake kallonsu a ranta amma bai ce komai ba, sai yau Allah ya budi bakinsa ya fada kenan.

Sai kawai ta rufe idanunta ta bude sannan tace.

"Insha Allah."

"Insha Allah me? Baki karasa ba..."

A hankali tana kallonsa tace.

"Me zan karasa?"

"Sunana..."

"Ma'aruf?"

Ya girgiza kansa.

"Wannan na kowa ne, though I like the way kike fadan 'R' din sunan, amma na fi so ki samo min wani daban, da ke kadai zaki dinga fada."

Ta danyi shiru tana cigaba da kallonsa, kwakwalarta na gaya mata cewa sun bar Hamida a can falo amma wani gefen na gaya mata cewa tunda kallo take yi vabu komai.

"Kamar me toh?"

Innocence din cikin muryarta ya fito tar, yayin da idanunta ke cigaba da kallon sa. Sai kawai yayi dariya yana zura hannunsa cikin gashinsa sannan ya girgiza kansa, kuma maimakon ya bata amsa sai kawai ya juyo da ita, tana fuskantar Wakin, ya tsaya daga bayanta sannan ya sunkuyo da fuskarsa cikin wuyanta, bakinsa daidai kunnenta ya rada a hankali yace.

"Call me the first thing you see..."

(Ki kira ni abu na farko da kika gani.)

Ta cije lebbenta tana murmushi, kuma a hankali idonta ya sauka akan robar sukarin da ta Wauko Wazu tayi amfani dashi a wani kayan gyaran fuska da akace mata sai an hada da sukarin.

"Sugar..."

Muryarta ta fito a hankali, sai yayi wani irin murmushi mai sauti a cikin wuyan nata yace.

"Yes! I know I'm that sweet Sunshine."

Sai kawai ta juya tana nata murmushin itama ta kalle shi, kuma a wannan lokacin ne kwakwalarta ta gaya mata cewa shine damarta na gaya masa sakon da take jin nauyinsa a cikin ™irjinta.

"Ina so ne in gaya maka wani abu."

Bakinta ya yanke shawarar fadar abinda ke zuciyarta kai tsaye tun kafin kwakwalarta ta canja tunani.

Sai ya gyada kansa yana kokarin rike ta a cikin hannunsa alamun yana saurarenta, ta haWiye wani abu a ma™ogwaronta a hankali tunaninta na ™ara gaya mata muhimmancin abinda zata fada.

"Ka yarda dani?"

A lokaci guda taga yanayin fuskar sa ya canja, ragowar murmushin na barin kan fuskar tasa, ya zama so serious Win da taji zata iya zagin kanta inda har da ba abu mai muhimmanci zata faWa ba. Ya ™ara gyada kansa sau daya yana kallonta kafin yace.

"With every cell of my body Doll, na yarda dake."

(Da kowanne kowanne abu dake jikina Doll, na yarda dake.)

Kalaman suka bata jwsrin gwiwar da a lokaci guda ta fara magana.
Chapter 28 · 0% Book details