← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 300

Sashe 9

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Naji sauki, daddy ina missing dinka yaushe xaka dawo?" Yace "Weekend in sha Allah" ta wara ido cike da jin ddi tace "Plss daddy ka dawo week end din kar ka daga, wllh ina son in ganka" kamar xata yi kuka ta kare, yyi murmushi yace "Sure dear, plss ki daina wasa da shan drugs din ki kinji" tace "Ina sha Allah daddy, har yanxu Dr ma bai xo ba" yace "Ehh mun yi waya daxu yace bai dawo ba" Imaan tace "Toh" yace "Sleep tight dear, banda kunna Ac" yar dariya tayi tace "Toh daddy byeee" katse wayar tayi ta mike ta kai ma Ammi daki sannan ta dawo dakinta ta shige duvet. Yau Friday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka tana kokarin saka kayanta taji k'aurin abincin da Ammi ta bar mata a kitchen kan gas don tana shigowa gidan Ammi ta fita kasuwa yin cefane, da gudu ta fita daure da towel don kashe gas din don dama sae da Ammi tayi mata kashedi kan cewar kada ta yarda abincin ta ya kone, muryar inna ta ji a balcony tana cewa "Aa kawai ni dai naga kwana biyu bata shigo bane shine nace in xo in duba ko jikin ne, tunda haka Allah yyi ta mai laulayi, ni jiya ma ko abinci basu kawo min ba wllh, in ma ba ta da lafiya ita Aishar baxata iya takowa ta kawo min abincin ba tunda ba uwarta Habiba bace, abu dai gashi ba tsari da ni fitinanniyar tsohuwa ce ba Bukar xan kira ince matarsa ta bar ni da yunwa ba?" muryar Yusuf imaan taji yana dariya yace "Toh ae an kai maki daga gidanmu naga" da sauri Imaan ta shige daki ta dau Hijab dinta ta fito ta shige kitchen ta kashe gas din sannan ta bude kofar kitchen din ta fice tana murguda baki ta sa Hijab dinta da iyakarsa gwiwa, ko takalmi bbu kafarta ta dinga tafiya har ta zagayo front din gidan, Mujaheed ne xaune kan farin kujera yana waya, ta turo baki ta wuce sa da sauri, ko minti biyar ba ayi da wucewarta ba shi ma ya ji muryar inna tana tahowa, mikewa yyi da sauri tun kan ya bar wajen ta gansa, da karfi ta kwalo masa kira tana murmushi, ya ki juyowa har ya sha corner, Yusuf sai danne dariyarsa yake, Inna ta bude baki tace "Wato ni Mujaheed xai walakanta ina kiransa ya min banxa kai shaida ne ko Isuhu" tana magana tana kunce ha6ar xanin xata goge kwalla, Yusuf ya kasa daurewa ya fara dariya yace "Ke fa kika ce kar ya sake xuwa bangaren ki..." A fusace tace "To shi mahaukaci ne bai san bacin rai ba" Karo Mujaheed ya kusa yi da Imaan dake kokarin lekowa taga ko inna ta taho bangaren, ya hade rai yace "Baki gani ne?" Tana shafa Inda ya bugeta tace "Ko ba inna bace, ta wani biyoni gidanmu anjima tace ina mata rashin kunya" tafiyarsa yyi ya bar ta wajen tsaye, ta turo baki ta bi bayansa, jin tafiyarta a bayansa ya tsaya ya juyo yace "Wai me yasa kike bi na ne" Tace "Ni ba bin ka nake ba tafiyata kawai nake" Tsayawa yyi ya daure fuska yace "To yi tafiyar ki, bana son ganin ki kusa da ni" ba ta ce komai ba ta fara tafiya kamar mai counting steps dinta, yana ta tsaye yana jiran tayi nisa ganin ynda take tafiyar ya girgixa kai ya wuce ta cikin lokaci kankani, sai a sannan ta kara saurinta har ta jera da shi, d'an murmushi yyi bai dai ce komai ba bai kuma kalleta ba, sai da suka kusa entrance din kitchen din part dinsu tace "Yaya ka mance promise da ka taba min 2 years back koh?" Kallonta yayi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Na me?" Ta wara manyan idanuwanta tace "Idan nayi saukan al-quran, gashi mun kusa in few months time" tabe baki yyi xai bude kofar kitchen din yace "I can't recall...." Ta xaro ido ta rikosa da sauri tace "Wllh nasan baka mance ba" Buge hannunta yyi yana mata wani kallo yace "Keee" Ta turo baki tana kallonsa, yace "Sakeni kar in mare ki" sake sa tayi ya bude kofar kitchen din ya shiga ya kulle, tana ta tsaye wajen bayan few minutes ta murguda baki ta wuce, ta kitchen dinsu ta bi ta kulle kofar sannan ta wuce dakinta ta sa kayanta. Yau tunda Imaan ta tashi take ta murna, gaba daya farin cikin ta ya kasa boyuwa, Kitchen ta shiga tace "Ammi da yaushe daddy xai iso?" Bude baki Ammi tayi tace "Kina kallon agogo kuwa Imaan?" Imaan tace "Ammi wai yau ma da daddyna xai dawo sai naje islamiyya?" Ammi ta mata wani mugun kallo tace "Uwar me xa ki xauna ki min ko yace maki da safe xai taso, common kin 6ace min a nan kin je kin shirya ko sai na 6ata maki rai" a hankali Imaan ta juya a sanyaye ta koma bedroom dinta ta fiddo uniform dinta ta shiga sa wa, sai da Ammi tayi mata jan ido ta amince da yin breakfast da ta hada mata, tana xaune dinning tana shan shayin da kyar Maimoon ta shigo parlon sanye da uniform, Ammi dake goge goge a parlorn tace "Maimoon ku yi wucewar ku kar ta bata maku lkci ko da kafa ne sai ta je" dariya kawai Maimoon tayi ta fita, Imaan ta mike don kanta ganin takwas ya wuce ta dau jakarta ta fita tana matsar kwalla ko ta kan kudin makarantar bata bi, Ammi dai ko kallonta bata yi ba, Tsaye taga Mujaheed jikin motar banda masifa babu abinda yake ma kannin nasa, duk kallonsa kawai suke babu wanda yace komai, "Don samun waje nan nan da islamiyyar ma sai an kai ku a mota ku ga yan gayu ko, to wllh ni ba driver din kowa bane a cikin ku da xa a dinga cewa in ajiye ku a makaranta, Yusuf da ya ga xai iya sai yyi, I won't tolerate that shittt" A hankali Ummi tace "Amma ya Mujaheed kawai don kana nan ne yasa xaka kai mu ai ba kai ke kai mu ba dama, kuma Abba yace kila Monday xa mu samu sabon driver...." wani kallo ya dinga mata fuska daure, ta sunkuyar da kanta, Imaan da isowanta kenan ta bude motar xata shiga ya dakatar da ita yace "Kee, do I look like drivern gidanku da xaki ajiye ni for the past 15 mins a nan, to ke daga yanxu ma xa ki fara naki trekking din" yana fadin haka ya nuna mata makeken gate din gidan yace "Bi can ki kama hanyar makarantar" ta wani gwalo ido tana kallonsa, lkci daya ta juya kamar xata yi kuka xata koma part dinsu tace "Ni dai ban ta6a tafiya da kafa ba...." Wani tsawa yyi mata yace "Wllh ki ka yarda na takowa har Inda kike sai na sa ki kuka" tsayawa tayi tana hawaye don bata mance last abinda ya mata ba, ya nuna mata gate on a serious note yace "Bi can" Gate din ta nufa tana kuka ya jira ya ga fitar ta sannan ya shiga motar ya bar gidan har ya wuce ta. Tsaye tayi bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab tana kuka, ta kusa minti sha biyar tsaye a haka taji cikin cool voice ance "Are you okay" xame hannunta tayi a hankali daga fuskarta tana lekan ko waye ta cikin hijab dinta, wani dogon matashi ne da baxai wuce thirty two ba, yana sanye cikin kananun kaya idonsa sanye da bakar spec, dogo ne shi din sosai, sannan shi ba baki ba kuma baxa a sa shi a jerin farare ba, kuka ya kara taho mata ta dinga rerawa, yace "Subhanallah, wani abu ya faru da ke ne? Talk to me plss" Cikin rawar murya tace "Yaya ne ya ce baxan shiga mota ba trekking xanyi kuma islamiyyar mu da nisa wllh" kallonta ya dinga yi da mamaki, ta sake lekosa ta cikin Hijab suka hada ido ta yi saurin rufe fuskar tana shessheka, ya d'an yi murmushi yace "Kin masa laifi kenan" girgixa masa kai tayi, yace "Toh mu je in ajiye ki ga ride dina can, while going inside the filling station na gan ki tsaye bayan nayi refilling tank na fito I still saw u the way you were so I decided to check if you are alright" shiru tayi bata ce komai ba yace "Mu je to" tace "A'a" yace "Ohk in samar maki adai daita?" Kai ta gyada masa, ya tsayar da adai daitan ta shiga ya basa kudin, a hankali tace "Nagode" ya mata murmushi kawai mai adai daitan ya ja suka bar wajen, Yusuf ne ya dauko su daga islamiyyar bayan sun tashi karfe sha biyu, tun a mota ya dinga tambayar Imaan me ya faru ganin yanda take yamutse fuska, da kyar tace "Kafana ke min ciwo" yace "Toh sannu, idan muka isa gida sai ki shafa maganin" a hankali tace "Toh" suna isa gidan da kyar ta fito motar, Yusuf ya kama hannunta ya rakata har sashin nasu sannan ya bude mata kofa ta shiga ciki, wanka kawai tayi ta saka doguwar riga Ammi ta shafa mata methylated lotion din da take shafawa a kafafuwanta sannan ta sa ta kwanta nan da nan kuma bacci ya dauketa, dab da la'asar Ammi ta tasheta, Ammi bata mata xancen islamiyya ba Imaan ta wara ido ganin irin girke girken da Ammi tayi tace "Ammi is all this for daddy?" Ammi tace "No it's for Imaan" murmushi Imaan tayi ta rungumeta ta baya tace "Thanks sweet mum" Ammi tace "Ki tafi kiyi sllh ko baki ga lokacin hr ya gota ba" da sauri ta koma daki, tana idar wa ta fito, Ammi tace "Daddy ya kira yana gate, ki fita ki shigo masa da kaya" da sauri Imaan ta nufi kofa Ammi na kiranta ta xo ta sa hajib don rigar jikinta karamin hannun garesa amma tuni ta fice, dai dai nan mai gadi ya bude gate sai ga motar Daddynta, da gudu ta nufi parking space ta tsaya cike da murna, Mujaheed dake kokarin
Chapter 9 · 0% Book details