← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 234 OF 300

Sashe 234

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

can" fita suka yi parlon gaba daya, Abba na kallon Inna ganin yanda ta rikice yace "Bari a dubota can bangaren su, amma ina xata je dama Inna" Inna ta bi bayansu Maimoon da sauri, tana tsaye bakin kofa sai xaxxare ido take tana jiran fitowarsu, Maimoon ce ta fara fitowa tace "Bata nan fa Inna" Wani salati Inna ta rafka da karfi sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, bata ciki fa ku ka ce???" Su Abba da Aunty duk suka fito tsakar gida Mama Hadiza ma ta fito bayan Maryam ta je sama ta gaya mata abinda ke faruwa, Daddy dai na tsaye balcony dinsa yana kallon mahaifiyar tasa, Inna ta tsaya dai dai tsakar compound din ta daura hannu a kai ta dinga rusa kuka tana cewa "Na shiga uku Allah ka dubeni kada Bukar ya kullace ni har gobe kiyama, Ina imaan xata shiga da tsakar daren nan jama'ah, wllh wanke bandaki nake na fito naga babu ita sai kwanon farfesunta, na shiga uku jama'a ku taimakeni kada a dinga cewa a parlona Imaan ta 6ata...." Mama Hadiza ta nufe ta da sauri tace "Haba Inna meye haka kuma, ce maki aka yi Imaan din 6ata tayi? Haba don Allah" Cikin kuka Inna tace "Idan ba 6ata tayi ba to Ina take Hadiza?? Kafff gidan nan an duba bbu ita babu alamarta fa, Wllh da ba a bangarena take ba bbu abinda xai dameni sai dai a daure Ahmadu tunda shi yyi mata auren dole, yanxu kuwa ai ni xa a daure tunda kowa yasan a bangarena take, da wani bakin xan ma 'yan sandan bayani idan an tafi dani?? Kuma duk aka tashi magana dama cewa xa ayi parlon Inna ta 6ata, to ina dalili a sa ni a bakin duniya Hadiza???? Don Allah ku min rai a nemo ta kada in shiga uku, wannan ba karamin magana bane wllh" Ta kuma rushewa da kuka har da durkusawa kasa tana salati, Abba dai ya kasa cewa komai haka ma Daddy da ya makale a Balcony dinsa, Inna ta kara mikewa tana kuka sosai ta nufi gate tana cewa "Duk Ahmadu ne ya jaza mana fitinar nan gaskiya idan wani abu ya sami jikata xan rufe ido in mance ni na haifeka Ahmadu" Umma da shigowarta gidan kenan daga gidan Hajiya Saude ta makale parking space tana wurwurga ido jin wai ba a ga Imaan ba, Inna na kallon mai gadi a waje ta fixgosa tace "Ilu kaga fitar Imaan?" yace "A'a ban gani ba Baaba..." Inna ta wani xaro ido ta turasa kawai ta fice gate din ta saka kai gaba sai babban titi tana salati tana rusa kuka, Mama Hadiza ce ta bi ta tana kiranta amma Inaaa... Karfe goma saura Mujaheed ya mike daga xaunen da yyi gefen gado tun shigowarsu yana kallon football a tv na bango dake manne a dakin hotel din, Imaan dai har lkcn tana durkushe inda take tun daxu, banda axaban ciwo babu abinda kanta da duk joints dinta suke mata amma ko xama ta ki yi, ga kuma bacci dake fixgarta, ta dai gaji da kuka da rokonsa da take tayi tsit ta xuba ma saurautar Allah ido, satan kallonta Mujaheed yyi ganin idonta a lumshe bacci ya dauketa a yanda take, ya dau remote ya kashe tvn ya mike a hankali ya nufeta, dukawa yyi ya dagota ta farka a rikice xata fasa masa ihu ya rufe bakinta a jikinsa, jikinta ya dau rawa tana kokarin kwace kanta bai ajiyeta ba sai saman gado, xata mike ya hade rai, calmly yace "Lie still..." Kai kawai take gyada masa a tsorace, ya dinga kallonta ko kiftawa babu, kamo hannunsa tayi tana girgixa masa kai pleadingly tace "Don Allah Yaya ka maida ni gida kila ana ta nemana wllh" Ya xame hannunsa still looking at her yace "Kila don kina ganin ki a kadunan yasa kike tunanin xan maida ki gida, Allah ya kai mu gobe da safe, I will eraze that thought off ur mind" Ta dinga kallonsa xuciyarta na bugawa, mikewa yyi ya nufi switch din dakin ya kashe wutan, ta mike xaune da sauri gabanta na faduwa tana kallonsa cikin duhu, a hankali tace "Yaya..." D'an Murmushi yyi ya nufi kan gadon, tuni ta sauka ta tsaya tana kallonsa cikin duhun xuciyarta na bugawa....
Chapter 234 · 0% Book details