← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 300

Sashe 20

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya Mujaheed ya daburce ya rasa abin cewa, Abba yace "Ko in kai ta asibitin kawai" da sauri yace "Noo Abba, naga bani da kayan aiki a gida ne, sai dai in kai ta asibitin in duba ta a can" Abba yace "Toh hakan na da kyau" Magana yake amma gaba daya rabin attention dinsa na kan window din dakin Umma duk da baya hango komai, amma fatansa yanxu ace bata tashi bacci ba duk da yasan da wuya, Ya sunkuyar da kansa yace "Toh xan dauko makullin mota a ciki" Daddy ya mika masa nasa makullin motar yace "You use my car, duk yanda ake ciki you let me know" Mujaheed ya risina ya amsa makullin motar yace "Toh Abba" daddy yayi ma yayan nasa sallama ya wuce ba tare da ya kalli imaan da ta cika saura kiris ta fashe ba, bayan ya tafi Abba ya kalleta yace "Sannu Mamana" Ganin hawaye idonta yace "Baki son bin Muhammad din kenan?" Da sauri ta gyada masa kai hawayen na sakkowa idonta, yace "Kuma baki son daddyn naki ya huta koh, am sure kila xuwa anjima ko gobe xai koma bakin aiki, shi Mujaheed din ba yayanki bane?" Ta fashe da kuka tace "Abba ihu xai ta min a hanya fa" Abba yyi murmushi mai sauti sai dai bai ce komai ba, Mujaheed dai sai kallonta yake ta gefen ido, Back seat Abba ya bude mata yace "Shiga" a hankali ta shiga ta jinginar da kanta jikin motar, Abba na kallon Mujaheed yace "You take very good care of her, ko kallon banxa ban yarda kayi mata ba" Ya sauke idonsa yace "Toh Abba" Abba ya daga mata hannu ta mayar masa tana goge idonta, ya juya ya wuce ciki, Mujaheed ya gama warming motar yayi horn ana bude masa gate ya fita gidan, sai da suka hau saman titi yace "Saboda baki son xuwa schl shine kika fake da ciwon karya salon ki ba mutane wahala koh?" Jin bata ce komai ba ya kalleta ta madubin motar, murguda masa baki take, suna hada ido ta turo bakin kamar xata yi kuka sai dai bata ce komai ba, ya gyada kai yace "Xaki gwammace schl kika yi tafiyar ki yau" ta fashe da kuka tace "Dama dai Abba yace duk abinda ka min in gaya masa" Bai tanka ta ba har suka iso asibitin da yake aiki, yana gama parking ya bude motar ya fita ita ma ta fita, ya rufe motarsa ya dau hanyar entrance din shiga hospital din, a sauri ta bi bayansa, tsaye ta gansa reception suna gaisawa da nurses dake wajen da fara'a, Wata nurse tace "Doctor I heard an sake transferring dinka xuwa nan, kuma shiru ba mu ganka ba" Yace "Sure da yau xan yi resuming, but due to some reasons sai Wednesday in sha Allah" duk nurses din suka amsa masa da Allah ya kai mu, juyawa yyi yaga Imaan ta nemi kujera tayi xamanta, wata nurse tace "Dr sister dinka ce?" Yace "Sure bata da lafiya ne" daga haka ya wuce sama, duk sai da ya shiga office din doctors dake duty safiyar, Dr Mukhtar na ganinsa ya mike yace "Kaga mara kirki dama yau xaka yi resuming shine babu sanarwa" Mujaheed ya karasa yana murmushi suka gaisa yace "Sai Wednesday in sha Allah, na kawo sister na ne bata da lafiya" Mukhtar yace "Subhanallah Ummi ko Rahma?" Yace "None, cousin dita ce wannan" Dr Mukhtar ya koma ya xauna yace "Ohk tana ina" Yace "Tana reception" Dr Mukhtar ya buga waya downstairs ba a dau lkci ba wata nurse ta shigo office dinsa, gaida Mujaheed tayi da fara'a ya amsa yace "Ya aikin Zainab" tace "Alhmdllh Dr" Dr Mukhtar yace "Ki taho da patient dake reception" tace "Wanne they are almost 7 patients downstairs" Mujaheed yace "Imaan sunanta" tace "Ohk" daga haka ta fita, tare suka dawo da Imaan da ta wani yi laushi da kyar take jan kafar, Dr Mukhtar ya nuna mata kujeran dake kallon wanda Mujaheed ya xauna, ta xauna xata kwantar da kanta kan table Mujaheed ya mata wani kallo yace "Tashi" kamar xata yi kuka ta dago kanta, likitan yace "Sannu Imaan, ya kike jin jikinki, like ina ke maki ciwo?" A hankali tace "Jiya da daddare bayana ya dinga min ciwo har da kai na kuma ina jin sanyi, ban ma yi bacci ba" likitan yyi murmushi yace "Yau da safe fa" Ta kallesa murya can kasa tace "Kafafuwana suka fara min ciwo da na tashi, anjima kuma duk jikina ya fara min ciwo" Ya langwabar da kai yace "Ikon Allah, suna maki haka ne?" Kai ta gyada masa, yace "Toh kina shan wasu magunguna ne?" Kai ta gyada masa, yace "Kin san sunan su?" Ta gyada masa kai, yace "Can you write them down for me now?" Tace "Sure" farar takarda ya ajiye mata da pen, nan ta rubuta masa gaba daya drugs dinta har da na shafawa ta mika masa takardan ya amsa yana dubawa, bayan few seconds ya daga kai yana kallon Mujaheed dake kallonsa shi ma, kafin yace komai Mujaheed yace "Rubuta mata injections taje ayi mata" Likitan yyi yanda Mujaheed yace, Mujaheed ya amshi takardan yana kallon alluran da ya rubuta mata sannan ya mika ma Imaan da ta kife kanta da table yace "Karba kije nurses su maki alluran" ta dago da sauri tace "Yaya allura kuma, ni doctor na baya min allura magani kawai yake ban" ya jefa mata wani kallo yace "Sai ki jira ya dawo ya ci gaba da baki maganin, nan kam allura xa a maki, get up my friend" a d'an tsawace ya karasa maganan, Ta amsa lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya ta fita office din, a hankali Dr Mukhtar yace "Is she a sickled cell patient Mujaheed?" Mujaheed ya girgixa kai yace "Not at all, She is only carrying the trait, a carrier" da mamaki Likitan yace "But it's almost mimicking the disease" Mujaheed ya buda hannu yace "Mu ma haka muka gani" Dr Mukhtar yace "Subhanallah, this is kind of rare, Allah ya bata lafiya" Mujaheed yace "Ameen" Dr Mukhtar yace "Kasan alluran are strong, ta ci abinci kuwa?" Mujaheed ya mike da sauri yace "I don't know, bari in tambayeta, kafin in dawo plss kayi prescribing drugs in addition to hers" daga haka ya fita, injection room ya shiga bayan nurses din sun sanar masa suna ciki xa a mata alluran, tsaye take tana hawaye nurse din ma na tsaye rike da alluran sai kallonta take, tana ganin Mujaheed tace "Yauwa Dr ta ki fa" Mujaheed ya hade rai yace "Are you a baby? Waye kike son ba wahala, xan maida ki gida da ciwon ki ne idan baki yi respecting kan ki ba" ta fashe da kuka bata ce komai ba, Yace "Kin ci abinci?" Cikin rawar murya tace "Na sha shayi kadan amma yunwa nake ji" wani kallo ya dinga mata, can ya kalli nurse din yace "Nurse let me get her something to take plss" nurse din tace "Ba damuwa Dr" daga haka ya fita, nurse din ta nuna mata kujera ta xauna. Rike da malt Mujaheed ya dawo injection room din, ya bude sannan ya mika mata, Kadan ta sha xata ajiye yace "Wa za ki ajiye ma" ta hadiye na bakinta da kyar tace "Xan sha idan an gama min" nurse din tace "Aa ki kara kadan" da kyar Imaan ta kara malt din sannan nurse din tasa ta tashi, ta mike ta fashe da kuka tana kallon Mujaheed tace "Wllh tsoro nake ji xai min xafi" nurse din tace "Baxai maki ba kuwa" Mujaheed yace "Xan fa tafi in bar ki a asibitin nan kina bata min lkci" tace "Don Allah kai ka min plsss" yace "Baxan yi ba, kin tsaya ko inyi tafiyata" da kyar ta isa kusa da nurse din, ta kallesa ta mika masa hannu jikin rawar murya tace "Don Allah ka rike min hannu Yaya" bai san lkcn da yyi murmushi ba ya karasa inda suke, ta kama hannunsa ta runtse ido, nurse din tace "Me yasa baki sa under skirt ba?" Ta turo baki tace "Ni bana so" nurse din tayi murmushi, ta daga mata abayar jikinta, rungume Mujaheed tayi ta kwantar da kanta kirjinsa, cikin rawar murya tace "Wayyo Yaya don Allah kace ta min a hankali, kar ta min da xafi" Mujaheed ya amshi alluran hannun nurse din yayi mata, xaro ido tayi tana cewa "Yaya ta sa alluran? Don Allah tayi a hankali, tuni ya amshi dayan alluran yyi mata shi ma, sae da ya cire syringe din ta sakar masu ihu duk tunaninta lkcn xa ayi alluran, ya turata daga jikinsa, ta dinga xaro ido, nurse din tayi dariya tace "Toh ba gashi har an gama ba" Imaan ta zaro ido tace "Da gaske? To ban ji sanda aka cire ba" Mujaheed dai ko kallonta bai yi ba yyi disposing syringe din ya nufi kofa, nurse din tace "Ki fa danna wajen sosai idan kun koma gida" Imaan ta gyada mata kai tana goge idonta har sannan tana mamakin wai har an mata allura don bata ji zafin da take ta jira ba, ta dau sauran malt dinta ta fita, xaunawa tayi reception ganin bata gansa ba, bayan kusan minti goma sai gashi ya sakko, yana kallonta ya nufi kofa, da kyar ta mike tace "Yaya na fara jin jiri" yace "Toh ko in bar ki a nan" da sauri ta girgixa masa kai ta isa gunsa, saura kadan ta fadi gun fita, ya kalleta sau daya yyi gaba, back seat ta shiga ta kwanta tana maida numfashi, ya shiga motar ya tada suka bar asibitin, wani pharmacy ya tsaya xai fita tace "Yaya wllh idona juya min yake" nan ma dai bai tanka ta ba, drugs dinta da sabbin da Dr Mukhtar yyi prescribing ya siya mata sae lucozade boost babba biyu, duk ya ajiye bayan motar, har suka isa gida yyi parking a parking lot din daddy bacci Imaan take, daga cikin motar ya dinga lekan apartment dinsu gabansa na faduwa, ya juya ya kalleta, sannan ya fito daga motar, ya bude back seat yace "kee" bude ido tayi da
Chapter 20 · 0% Book details