Sashe 150
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna fitowa compound Inna ta kalli Imaan tace "Toh ko dai in je inyi ma Ahmadu magana ya sa direba ya kai mu?" Imaan dai bata ce komai ba, Inna tayi tsaki tace "Ayi ta maki magana kina ma mutane shiru idan ma baccin ne bai isheki ba idan munje gidan Mujaheed din ba sai a baki daki daya ki kwanta kiyi ta yi ba, ai can ma gida ne" Daga haka ta nufi part din Abba imaan na biye da ita, Aunty ce parlor tana goge goge da su Maimoon, Aunty ta xauna ta gaida Inna, su Maimoon ma suka gaisheta, Inna ta amsa tace "Gidan shiru ba wannan mata Rukayya koh" Ita dai Aunty bata ce komai ba, Inna tace "Toh Ahmadu nake nema ya kira wannan mutumi me jan mota ya kai mu gidan Mujaheed, tun asuba na gama shiryawa Imaan ta bata min lkci" Aunty tace "Toh xauna Inna ki jira driver din an aike sa yanxu" Inna ta xauna tace "So dai ake in makara kawai, Banda haka ni fa tun Asuba nayi wanka na" Imaan ta xauna a parlon bayan ta gaida Aunty tana kallon series din da akeyi, ba a dau lkci ba driver ya dawo, Aunty na kallon Inna dake xuba gyangyadi tace "Toh ya dawo fa inna..." Inna ta bude ido da sauri ta mike tace "Toh tashi mu je imaan, shi Ahmadun baya nan ne?" Aunty tace "Bacci yake" Inna tace "Ni dai ba wajena suka gaji baccin safe kamar rubabbu ba gaskiya" daga haka ta fita imaan na biye da ita, a waje suka tadda driver da mota, imaan ta bude ma Inna motar ta shiga tana amsa gaisuwar driver din sannan imaan ma ta shiga, sai da suka hau saman titi Inna na kallon Imaan tace "Toh kin gaya masa anguwar ne" Drivern na murmushi yace "Ae na san gidan kaka" Inna ta washe baki tace "Ashe har ku kunje kun sa ma gidan albarka ku ma" Shi dai bai ce komai ba yana murmushi, tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso gidan Mujaheed, Inna na kallon driver da yayi parking a waje tace "Kai ya haka ka danna han a bude maka gate ka shiga mana, gidan jikana ne fa" Horn driver yyi mai gadi ya fito yana kallonsa, can ya karaso gun motar yace "Daga ina?" Rike baki Inna tayi da mamaki tana kallonsa tace "Naga abinda ya isheni, kai gidan jikana ne fa kake tambayar daga ina? Na shiga uku wai ni yake tambaya daga Ina, ko in sauko in bude get din da kai na ne" Mai gadin yyi kasa da kai yace "Yi hakuri Baaba" daga haka ya tafi da sauri ya bude gate din, Inna ta ja tsaki tace "Mutane dai ba tsoron Allah... wai daga Ina, ke ki ji fa gantalalle amma ba laifinsa bane na Mujaheed ne da bai sanar masa kakarsa na da rai ba" Ita dai Imaan bata ce komai ba driver ne ke bata hakuri, yana gama parking imaan ta bude motar ta fito, Inna na kallon driver din tace "Toh yi wucewar ka yaro, mu da gida kuma sai bayan isha in sha Allah" Yace "Toh baaba ku dawo lafiya" Inna ta nufi entrance din shiga gidan tana washe baki, Imaan dai na biye da ita, Bubbuga kofa Inna ta shiga yi da karfi tana cewa "Salama alaikum" Imaan tace "Kai inna kiyi a hankali mana..." Matsawa Inna tayi ta bude baki tana kallonta, Imaan ta turo baki ta danna bell tace "Kawai kiyi ta bubbuga ma mutane kofa da karfi" Inna xata yi magana aka bude kofar, Inna ta washe baki tana kallonsa tace "Mujaheed...." Kallonsu kawai yake yana tsaye bakin kofar sanye da jallabiya, Inna ta rike haba tace "Ashe da gaske ba ku tashi ba kenan" rabawa tayi ta gefensa kamar yar yarinya ta shige parlon, Imaan ta juya tana murmushi, can dai ta juyo a hankali, kallonta taga yana yi, ta sunkuyar da kai tace "Ina kwana Yaya" Muryar Inna suka ji a parlor tace "Ina amaryar??" Mujaheed ya juya ya koma parlon, Imaan ta bi bayansa, Xaunawa yyi yana kallon Inna yace "Ina kwana?" ta washe baki tace "Lafiya lau Mujaheed, tun asuba da na tashi nayi wanka wllh, Banda imaan da ta bata min lkci da tun gari bai gama wayewa ba xa ku gan ni" shafa kansa yyi bai dai ce komai ba, Inna na kallon pillow da aka ajiye kan lallausan sabon rug din parlon tace "Cewa nayi ina amaryar" Mujaheed yace "Tana sama...." Yana fadin haka ya tashi ya wuce sama, Inna ta kara kallon pillow dake parlor murya can kasa tace "Toh waye kuma ya kwana a parlor ni patuu" Imaan tayi murmushi tace "Toh ke ina ruwan ki" Inna tace "Atohhh, ba ruwana kuwa" Cire Hijab Inna tayi ta linke tana kallon parlon tana murmushi tace "Sabon gida ba dai sha'awa ba" Mikewa tayi ta nufi wani kofa ta bude tana lekan ciki ta karasa ta ajiye hijab din nata a ciki ta fito ta rufe tace "Dakinsu Hansai ne, shi ma sun xuba lafiyayyun kaya a ciki wllh masu tsada...." tabe baki tayi ta tafi ta bude kofar kitchen tana lekan ciki ta xaro ido tace "Waiii.... Ai kitchen din ma ba masaka tsinke da kayan kitchen na xamani, Ashe dai ba gwalagwalan karya aka dinga yawo da shi ranan casu ba" Imaan dai ta hade rai sai kallonta take... Mujaheed na haurawa sama ya bude dakin da Safeenah ke ciki, bacci ya sameta tana yi, ya shiga ya kulle kofar ya karasa kan gadon ya d'an bugi gadon yana kallonta, sai da ya buga gadon da karfi for d second time sannan ta bude ido ta mike xaune tana kallonsa da wani expression, yace "Kin ma yi sllhn kuwa?" D'an tsaki tayi tace "Haba don Allah sai ka wani buga gado ka tsorata ni kamar xaka tada kato??" Daga head har toes yake kallonta, ta tabe baki ta kalli agogo tace "Sllh dai dole inyi ko karfe nawa ne" da mamaki yake kallonta yace "A gidan ku haka kike kai wa har karfe tara baki yi sllh ba Safeenah?" A fusace tace "Toh gajiyan bikin fa? Plss Mujaheed that's not how to treat a new bride you are not romantic, haba don Allah sai kace mun ta6a rayuwa gida daya...." Wani kallo kawai Mujaheed yake mata, strictly yace "Look Safeenah I won't tolerate this, gidana ba na kafurai bane, tun asuba na shigo na tashe ki kiyi sllh shine har yanxu baki yi ba, is this ur home training?" Yar dariya tayi tana kallonsa daga sama har kasa tace "Kai ko kunya baka ji ba don Allah??" tana kwaikwayonsa tace "Wai wani tun asuba na shigo na tashe ki.. ban taba jin labarin ango irin ka ba sai yau da nake gani a xahiri a gidana, wai ka shigo min da asuba, ain't you ashame of ur self plss" murguda baki tayi ta sauka daga saman gadon da yar figigiyar rigar baccinta ta nufi bathroom, ya bi da kallo kafin ta shiga bayin yace "Ki sameni downstairs yanxu idan kin yi sllhn" daga haka ya juya ya fice daga dakin, Tv ya tarar Inna na kokarin kunnawa tana cewa "Toh sai me idan Baki kunna min ba kamar yau na saba hada kayan kallo kuma... Gidan Mujaheed kuma baxa ki saki jiki kiyi yanda kike so, ban da shi wa gare ki da xa ki je gidansa ki sake jiki dama, ni dai ba ruwana, ki dinga abu domin Allah Banda munafurci" Imaan dai sai kallonta take fuska daure, Inna na ganin Mujaheed ta mike tace "Wai ka ji daga nace ta hada min kayan kallo shine xata ce min daga xuwa gidan mutane, su waye kuma mutane, Mujaheed din koko Amaryar da bata fito gaisheni ba har yanxu, ni dai ba ruwana, idan ma xa ki cire Hijabin nan na jikinki ki linke ki ajiye ki tsayar da ranki waje daya ki saki jiki kamar kina gidan Bukar to gwara ki cire don da kyar ma ba kwana xamu yi a nan ba gaskiya, ga dai dakuna na kirga har hudu ranan" Mujaheed ya karasa ya kunna mata tv din yace "Xata sakko yanxu ta gaishe ki ai" Inna ta koma kan kujera ta xauna ta tsuke fuska tana kallon Tv, Xaunawa Mujaheed yayi kan kujera ya kalli Imaan ta gefen ido, Sai turo baki take, Mujaheed ya kalli Inna yace "Amma kuma sai ki yi irin wannan sammako Inna" Inna ta kallesa da sauri tace "Ni dai Ahmadu ne yace in taho da sassafe, bayan jiya ya shigo da daddare mun yi magana" Imaan ta xaro ido tana kallon Inna, Murmushi Mujaheed yyi yana gyada kai, Jin taku a stairs ya juya, Safeenah ce ke sakkowa sanye da doguwar riga damamme, Still tayi tana kallonsu, Inna ta kankance ido tana kallonta da kyau ita ma, Safeenah ta hade rai ta karasa sakkowa ta shigo cikin parlon, Mujaheed ya kalleta yace "Meet my grandma and my lil sis Imaan...." Inna na washe baki tace "Sannu Amarya, da fatan dai an tashi lafiya" dauke kai Safeenah tayi ta tabe baki murya can ciki tace "Ina kwana" Inna tace "Lafiya lau, sai dai ko sunanki ban sani ba" Mujaheed yace "Safeenah" Inna tace "Toh madalla, to safeenah Mujaheed dai gashi nan a gabana aka haifesa, kuma ni nayi wahala da shi tun yana tsummarsa, ke wahalar da nayi da shi wllh kare baxai ci ba, Tabb banda nakudarsa me Rukayya tayi???" Hade rai Mujaheed yyi yana kallonta, Safeenah tace "Toh maa sha Allah, ina d'an yi abu ne a sama Hajiya...." Xaro ido Inna tayi kafin tace komai Mujaheed yace "Mind you, Inna is what we call her..." Safeenah ta d'an tabe baki tace "Toh xan je in yi abinda ke gabana a sama Inna" Inna tace "Ba xancen kije kiyi abinda ke gaban ki ba Yar nan, ko karyawa fa ba mu yi ba, Imaan ma ina jin ko wanka bata yi ba don da naje ma bacci na tarar tana yi...." Imaan na kallon Inna tace "Ni bance maki ban yi wanka ba inna" wani matsiyacin kallon Safeenah ta jefa mata