← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 210 OF 300

Sashe 210

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*Imaan isn't for free* it's 300 via

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788

Bayan azahar mai make up da aka yi hiring ta xo tayi ma Imaan very light make up da ya fito da ainahin kyanta na 'yar fillo, ta saka wani lace mai tsadan gaske da Daddy yyi mata da head din da xata saka, ko tsinke ba a taba ba a lefenta dama, gaba daya kayan da xata yi fitan biki Daddy ne yyi mata su, tayi kyau har ta gaji barin ita da dama bata make up, kowa sai kallonta yake cike da sha'awa, Aunties din Sadeeq da Step mum dinsa duk sun xo gun mother's day din, Mariya da frnds dinsu na islamiyya da boko duk sun xo suma, da Ammi da Aunty ankon lace suka yi, ko kai ka gansu sai sun burge ka, karfe uku da wani abu Umma ta dawo gidan ita ma ta shirya cikin tsadadden lace ta shigo cikin jama'ah ana ta gaisawa, sosai hakan ya ba Aunty mamaki sai dai bata ce komai ba, bayan kusan awa daya sai ga Safeenah ta xo gidan cikin shiga ta alfarma da sisters dinta biyu, can kuma sai ga wasu daga kawayen Umma, gida ya cika da frnds din Aunty da Ammi masu ji da kansu cikin ankonsu na mothers day da Aunty ta fitar, irin rawan da Safeenah tayi sai abun ya baka mamaki, don xagewa tayi ba kadan ba kamar dai bikin masoyiyarta, sosai hakan ya ba Imaan mamaki, ita dai tana xaune ana ta abubuwa a wajen, duk Ammi na lura da imaan throughout the program bata da walwala kana gani kasan tana da damuwa, biyar da wani abu Ammi ta samu ta kebe da ita a backyard din apartment dinsu tana kallonta tace "Imaan ba nace ki kwantar da hankalin ki ba, or do you have any problem da baki son fada min ne" Imaan ta girgixa mata kai cikin sanyin murya tace "Ba komai Ammi...." Sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara taruwa idonta, Ammi tayi tunanin kila duk fargaban da ko wace amarya ke yi da xulumin barin gida ne ke damun yar tata, hakan yasa ta jawota kusa da ita ta shiga kwantar mata da hankali cikin taushin murya, Imaan dai sai gyada mata kai take hawaye na sakko mata, Ammi ta rungumeta tace "Bana son wannan kukan Imaan, today is ur happy day, ki saki ranki pls" a hankali imaan tace "Na daina" Ammi tace "Good ki shiga ciki ki xauna, karfe nawa yace xa ku tafi dinner din?" ta girgixa kai tace "Ban dai sani ba kila bayan Magrib" Ammi ta bude mata kofar kitchen tace "Go in and get some rest before then, or are you feeling pain anywhere?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a" Ammi tace "Toh shiga ciki ki xauna" shiga kitchen din tayi sai kuma ta juyo a hankali tace "Ammi Daddy na fa?" Ammi tace "Ya dawo two days ago ai, don kina part din Inna ne" Imaan tace "Toh" daga haka ta wuce dakinta, wayarta da ta sa a jaka ta fiddo tana dubawa taga text na Sadeeq, sosai gabanta ya fadi ta bude message din tana kallon content dinsa, "I am sorry to let u know that... tonight dinner isn't going to hold anymore due to some reasons, ki sanar ma mutanen gida, thanks" ta karanta message din ya fi sau biyar sannan ta ajiye wayar a sanyaye, lkci daya ta ji wani hawaye me xafi na xubo mata, xaunawa tayi gefen gado ta cire head tie dake kanta, Maimoon ta kira a waya daga karshe ta sanar mata babu dinner din ta gaya ma su Ammi don a sanar ma mutane da xa su tsaya sbda dinnern, Maimoon tace "What?? Sbda me??" A hankali Imaan tace "Ke dai ki gaya masu kawai ni ina daki yanxu" daga haka ta katse kiran, Aunty ce ta shigo dakin tana kallonta tace "Imaan shi Sadeeq din yace maki babu dinner kuma?" Imaan ta kalleta trying her best to look alright tace "Ehh daxu yyi min text Aunty, he said he is sorry for the inconvenience" Aunty tayi shiru tana kallonta can tace "Toh shkkn Allah ya so babu wanda ya tafi can din ma" daga haka ta fita dakin, kowa a gidan yayi mamakin me yasa aka ce an yi canceling dina, ciki har da Umma dake tsakar gida tace "Ahhh gaskiya mu dai ba a kyauta mana ba, mu da muka sa ran mu yi yanda muka ga dama yau abu namu maganin akwabe mu, ni fa har na hango an dire ma kowa full chicken a table da lemon masu kudi, gaskiya an shiga alhakin mutane da yawa..." Safeenah tace "Ikon Allah, to bari mu san inda dare ya mana dama dinner din nake xaman jira a tafi, ni ban ma taba jin inda aka fasa dinner ba sai a bikin gidan nan" Ammi dai ko kallonsu bata yi ba tana sallaman wasu frnds dinta da gifts da aka raba na mothers day, Mama Hadiza tace "Toh ai gwara hakan, Allah na tuba meye abun birgewa a dinner, albarka ake so a aure dama ba tsiya ba, dinner sai kace fadan Allah, ai ni wllh ya burgeni da yace bbu dinner kowa sai ya ci kajin a gidansa...." Umma dai bata kalli inda take ba ta shiga sallaman neighbors dinsu da xa su tafi, Mama Hadiza ce ta tafi sanar ma Inna babu Dinner don suna can ana shiri da ta Rasulu da taxo da yamma, Inna ta gwalo ido tana kallon Mama Hadiza tace "Subhanallahi shi Bulasawan wiwi ya sha da xai ce an fasa shagalin?" Mama Hadiza dai bata ce mata komai ba ta fita, Inna ta kalli Ta Rasulu da har ta fiddo kayan da xata saka da mayafi tace "Yau naga gantalallen mutumi ta Rasulu, wai ki ji ba casu" Bayan isha Imaan na xaune can karshen gado tana ta bin frnds dinsu da Mariya dake ta hira a dakin da kallo, ko kadan bata san abinda suke cewa ba don gaba daya she is absentminded, Maryam dai na xaune one side tana danna wayarta amma gaba daya mood dinta wasn't good, Maimoon ce ta shigo dakin ta nufo Imaan ta mika mata wayar hannunta, Imaan ta amsa a hankali tace "Waye?" Maimoon tace "Ya M.A" Imaan ta kai wayar kunne tayi sallama, cikin sanyin murya Mujaheed ya amsa mata daga daya bangaren, tace "Ina yini Yaya?" yace "Lafiya, can you pls come out now?" Tace "Kana Ina?" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Ki sameni bayan apartment dinmu" tace "Toh" daga haka ya katse wayar, ta mika ma Maimoon wayarta ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta har kasa ta saka, Maryam na kallonta tace "Where are you going to?" Imaan tace "Yaya ke kirana" daga haka ta fita bayan tace ma su Mariya tana xuwa, ta kitchen dinsu ta fita, ta dinga tafiya kamar mai tausayin kasa har ta kai Bangarensu Maimoon, tsaye ta gansa yana facing bango har ta iso kusa da shi bai juyo ba, a hankali tace "Ga ni Yaya" juyowa yyi yana kallonta, lkci daya ya sauke idonsa, ya fi minti biyu bai iya yace komai ba, sai kuma cikin sanyin murya yace "Sure I was suppose to ask you what u want for ur wedding but I didn't Imaan, but I don't know if you will appreciate this little that I have for you..." Imaan dai sai kallonsa take, wani round box mai kyau dake hannunsa ya bude yana kallonta ya fiddo bracelet sai kyalli yake kana gani kasan na menene ya kamo hannunta a hankali ya saka mata a wrist cikin sanyin murya yace "Am hoping you will love it lil sis" lkci daya hawaye ya kawo idonta ta fada jikinsa tana shessheka tace "Nagode Yayana" rungumeta yyi cikin breaking voice yace "I am... wishing u all d very best in ur marriage lil sis, Allah ya ba ku xaman lfya, but.. but i want to let you know this Imaan....." Sai kuma ya kasa ci gaba ya runtse ido, saketa yyi ya janyeta jikinsa ya juya xai bar wajen tace "You want to let me know what Yaya?" Bai juyo ba sbda bai son taga hawayen idonsa yace "I want to let you know that, kiyi ma mijin ki biyayya, be the best wife you can..." Daga haka ya wuce ta bi sa da kallo tana goge hawayen idonta tace "Toh nagode Yaya" a hankali ta juya ta koma apartment dinsu hawayen da take ta gogewa ya ki tsaya mata. Kamar Daren jiya wannan Daren ma Imaan bata yi baccin kirki ba, sai kallonsu Mariya da Maimoon da Maryam dake ta baccinsu take, daga karshe ta tashi ta dauro alwala ta dinga sllh har sai da taji bacci ya xo mata, nan kan darduman ta kwanta nn da nan kuma bacci yyi awon gaba da ita. Da asuba Ammi ta shigo ganinta kwance kasa ta tada ta tana kallonta tace "A kasa kuma Imaan maimakon ki tafi dakina?" Imaan ta mike xaune tana murxa ido tace "Sllh nayi ne daxu" Ammi tayi shiru tana kallonta, can tace "Toh ku tashi ku yi sllh lkci yyi" daga haka ta fita dakin, Da safe gida ya xamo ba masaka tsinke duk inda ka bi jama'ah ne, tun asuban fari dama ake ta girki a gidan don Aunty tace da kansu xa su yi abinci ba sai an wani kira masu yi ba, Umma ma dai na cikinsu, da ita aka dinga yin komai tun asuban, Ba karamin tilasta Imaan Ammi tayi ba ta sha shayin da ta hado mata sannan mai make up tayi mata make up kamar jira, yau ma dai wani ubansun lace din ta saka da ya fi na jiya, Maryam kam cewa tayi kanta na ciwo don ma kada a tilasta ta saka kaya, da ta tuna yanda suka yi da Sadeeq jiya sai ranta yyi mugun baci, in kuma ta tuna abinda Imaan ta gaya mata wai ba ruwanta sai tayi wani murmushi tana tausayin Yar uwar tata, Maimoon da Mariya suka cakare cikin ankonsu na ranan aka dinga hotuna. Karfe sha daya Yusuf ya fito dakinsa xuwa parlon Abba ta dalilin kiransa da yyi a waya, gaisawa yyi da mutanen dake parlon nasu don tun safe yake daki da few frnds dinsa, da sallama ya shiga parlon Abbansa yana kallonsa ya xauna yace "Gani Abba...." Abba xai yi magana Daddy ya shigo parlon da sallama, Yusuf ya gaishesa, Daddy ya amsa gaisuwarsa sannan ya xauna yana kallon Abba yace "Ina hanya ka kirani Barrister..." Abba ya kalli Yusuf yace "Kaje waje ku shigo tare da Sadeeq, ya kira yana waje...." Yusuf yace "Sadeeq Bulasawa?" Abba yace "Ehh" mikewa Yusuf yyi ya fita, Daddy ya kalli agogo sannan ya kalli Abba yace "Why is he here?"
Chapter 210 · 0% Book details