← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 277 OF 300

Sashe 277

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ya rufe bakin, tsoro yasa numfashinta ya dinga daga nan kuma bata kuma sanin komai ba. Ray din rana da ya sauka kan fuskarta ya sa ta bude ido a hankali ta sauke kan Ac dake dakin, kalle kallen dakin ta shiga yi as if trying to recall something, dai dai nan aka bude kofar dakin suka yi ido hudu da Mujaheed lkci daya ya sauke idonsa kasa ya kullo kofar, ta mike xaune da kyar, ta dafe kanta tace "Yaya Ina jin xaxxabi, my head is aching" Ya iso kusa da ita ya xauna gefenta still ya ki kallonta yace "Kiyi sllh sai kiyi breakfast in baki magani" ta xaro ido ta kalli agogo taga karfe takwas ya kusa a hankali tace "Sllh kuma Yaya, me yasa baka tasheni da asuba ba..." Komawa tayi ta kwanta saman pillow tace "and my body is weak, xaxxabi nake ji" Ya mike ya shiga bathroom ta bi sa da kallo kanta na sara mata, kara kallon agogo tayi ta mike xaune tana son tashi amma taji kamar idan ta tashi xata fadi ga ciwo da bayanta ke mata, fitowa yayi bathroom din yace "Ga warm water a kettle kije kiyi alwala" Yana fadin haka ya iso gabanta ya kama hannunta trying not to look at her in the eyes, sosai yaji jikinta yyi dumi, Imaan dai sai kallonsa take, Lkci daya ta xame hannunta ta fasa ihu tana komawa baya tana kallonsa, rikota yyi cikin sanyin murya yace "Stay still Imaan" girgixa masa kai ta dinga yi jikinta na bari tace "Wayyo Allah na, don Allah ka sakeni yaya...." ya saketa yace "Toh alwala xa ki yi ai" ta rufe fuskarta da pillow tana kuka sosai tana kiran inna, juyawa yyi ya fita dakin ya kulle mata kofar. Ba karamin wahala imaan ta ba Mujaheed ba ranan, though yasan dole xata daga masa hankali amma bai yi tunanin xai kai haka ba, sai a lkcn yasan raki yafi yawa a ciwon da take yi a gida, bai ta6a ganin mai raki irin Imaan ba, duk ta sa shi ma ya dinga jin kamar xaxxabi sai rufesa, duk abinda yasan xai mata ta samu relieve na ciwon baya da take ta ce masa yyi.. amma Imaan taki bari ya huta da rakinta, damuwarsa abincin da ta ki ci tun safe, gashi duk ta ishesa da kuka ita ya maida ta gida, a haka dai ya yini yana fama kamar Nanny har washegari, nan ma kuma ta daura daga inda ta tsaya jiya, though da Xaxxabi sosai ta tashi ranan, sure yasan she is in pain but ko kadan bata da juriya, karfe sha biyu ya fita pharmacy ya siyo ruwan drip da xai kara mata, bayan ya saka mata ruwan shine ta samu tayi ta bacci har kusan yamma. Yana xaune parlor ya jinginar da kansa da kujera har bacci ya soma daukansa a haka aka danna bell, bude ido yyi ya mike ya isa kofar ya bude, Maimoon ce tsaye da basket da ke dauke da abinci tana murmushi tace "Ina yini Yaya?" Ya shafa kansa yace "Lafiya lau, how are you?" Tace "I am fine, Inna ce tace in kawo ma Imaan abinci amma fa wai ban da kai, tace bata baka ba ko ka ci" tana magana tana dariya, ya d'an yi murmushi yace "Toh shiga ki ajiye mata" Yana fadin haka ya bata hanya ta shiga parlor ta ajiye abincin tace "Tana Ina?" Yace "She's sleeping upstairs" tace "Inna ta ban sako in gaya mata fa" yace "Bacci take yi..." Maimoon na murmushi tace "Toh shkkn sai da safe" yace "Jira in dauko maki transport" tace "A'a driver ne ya kawo ni" yace "Toh ki gaida Aunty and everyone" tace "In sha Allah" daga haka ta fita parlon ya kulle kofa, Yana son xuwa sama amma yana tsoron tashin hankalin Imaan, ya fi minti sha biyar xaune daga karshe ya mike ya wuce sama, a hankali ya bude kofar dakin, ya ganta xaune ta jingina da gado hawaye na sakkowa idonta... Ya sauke idonsa ya kulle kofar ya karasa kusa da ita, ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, har ransa ya dinga jin tausayinta, cikin sanyin murya yace "I am sorry Imaan, na fa ce ki yi hakuru..." Ta fashe da kuka tace "Ni bana so, kuma wllh sai na fada ka da Inna" murmushi yyi ya dago kanta ya jawota jikinsa tana kuka sosai, yace "Toh na ji ki gaya ma Inna in har xa ki hakura" ita dai bata ce komai tana shessheka.
Chapter 277 · 0% Book details