← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 300

Sashe 8

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Imaan ce xaune kitchen sai faman xuba surutu take ma Ammi dake girkin dinner a kitchen, yar skirt ne jikinta sai ves da yake ranan alhamis ne babu islamiyya, Ammi dake ta saurarenta ta tabe baki daga karshe tace "Aikin kenan sai dai ki cika mutum da surutu ba taimakon fari balle na bak'i" shiru Imaan tayi tana kallon Ammi, Ammi ta kalleta ganin yanda mood dinta ya canxa tayi murmushi tace "Toh ci gaba ina jin ki" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, Ammi ta karasa kusa da ita tace "I was joking sweetheart, tafi ciki let me fry some onion and pepper" mikewa Imaan tayi a hankali xata wuce Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, Ammi ta jingina da cabinet din kitchen din ta sauke ajiyar xuciya, can ta nufi kofa ta fita don bata son tayi bacci coz shine next abinda xata yi in har ta shiga daki, dakinta Ammi ta shiga ta sameta har ta kwanta, Ammi tace "Baxa kiyi bacci ba yanxu yamma yayi, je dakina xa ki ga leda da atamfa a ciki kan dressing chair ki kai ma su Anty kice ankon bikin Halima" Imaan ta mike xaune tace "Ammi to na mu fa" Ammi tace "Sai ki kirata ki tambayeta ban san ko an fidda naku ba" Imaan tace "Toh, Anty kawai xan nuna ma?" Ammi tace "Ehh sai ki ce mata ta nuna ma Hajiya, na dai fita ai" daga haka Ammi ta fita dakin, imaan ta sa hijab har kasa kan kayana jikinta ta fita ta dau ledan ankon a dakin Ammi, tun da ta shiga parlonsu Anty take yamutse fuska ta dalilin yaji dake tashi sosai daga kitchen, lkci daya ta rike numfashinta, har xata juya ta fita sai ta nufi stairs da gudu don ta shiga dakin Anty, tsarkewa tayi sbda rike numfashin da tayi ga kuma gudun da take, lkci daya ta fara tari sosai breathing dinta na sama, dai dai corridor ta fadi tana kokarin jan numfashi, Maimoon ta fito dakin Anty ganinta ta durkusa gabanta da sauri tace "Subhanallahi me ya faru Imaan" sound din faduwarta yasa Mujaheed ya fito daga bedroom din sa, ganinta a kasa ya kalli kofar Ummarsa kafin ya karasa da sauri ya dagata yana kallon Maimoon da ta rikice yace "Tafi ki karbo inhaler dinta da sauri" da gudu ta sauka xuwa part din su Imaan, Mujaheed ya bude kofar dakin Anty ya shigar da ita ya xaunar da ita kasa ya jinginar da ita da gado ya cire Hijab din jikinta, dai dai nan Anty ta fito daga bandaki, a rude tace "Subhanallahi, Asthman ne, garin Yaya? Ko in amso inhaler dinta" yace "Maimoon taje amsowa" sosai imaan xata baka tausayi saboda ynda take struggling da numfashinta, Mujaheed ya mike ya fita don bin bayan Maimoon suka kusa cin karo bakin kofa, fixge inhaler din yyi ya juya ya koma dakin ya durkusa gabanta ya kai mata baki, dafe hannunsa tayi tana inhaling, Anty dai na tsaye sai kallonta take cike da tausayinta, bayan wani lkci numfashin nata ya fara fita a hankali yana kokarin dawowa normal, Anty ta xauna gefen gado tayi tagumi tana kallonta, Ummi da Rahma na tsaye bakin kofar suna kallonta su ma, Har sannan Mujaheed na duke gabanta idonsa a kanta, muryar Umma suka ji tana cewa "Lafiya me ya faru ku ka tsaya cirko cirko bakin kofa?" Rahma tace "Asthma ne ya tashi wai" Umma ta leko dakin ganin Mujaheed ta wani xaro ido tace "Me Mujaheed yake a nan?" Mikewa yyi da sauri, ta wani hade rai tace "Tambayar ka nake, me ka shigo yi, ko kayi kama da likitan ta ne?" Ya girgixa kai yace "No na xo wucewa ne...." Dakatar da shi tayi tana masa wani shegen kallo tace "Sai ka tsaya aikin da ba lada koh? To ka shiga hankalin ka, Ka guji bacin raina, basu da number likitan ta ne ko kuma neman suna kake?" Shiru yyi bai ce komai ba, Cikin tsawa tace "Xo ka fita malam bana son shishshigi da kwala kai a faranti, kanwar uwar ka ko ta ubanka?" Bai ce komai ba ya kalli Imaan da Anty ke kokarin kwantarwa kan gado ya juya ya nufi kofa xai fita, Anty ta tabe baki tace "Ciwo dai bai wuce kan kowa ba, ita ma ba ita ta doro ma kanta ba....." Umma ta katse ta da sauri tace "Allah yayi mana tsari da irin wannan ciwo nata, ya tsari jikokinmu da tatta6a kunne, a rayuwar nan ta ynxu wa enda ba sickler ba ma ya suka kare, ae irinsu ne ke tsiyata namiji a sintirin asibiti...." Tsaye Mujaheed yyi bakin kofa yana kallon Umma, Anty ta wani hade rai tace "Kinga ki daina kiranta da sickler ita din ba sickler bace, Allah kuma yyi mata tsari da shi" Umma ta wani tabe baki hade da dariya tace "Kwa dinga boye ma wanda ku ka raina ma wayo, Allah dai ya ba kowa lafiya...." A hankali Mujaheed yace "Umma ba fa sickler bace, she is just a carrier...." Umma ta maka masa wani kallo tace "Meye maraban dambe da fada? And did you have any problem with her being a sickler or not da har kake karyata ni Mujaheed?" Bude kofar yayi ya fita dakin bai ce komai ba, ta ja tsaki ta fice ita ma. Anty ta girgixa kai ta zauna kusa da Imaan da ta lumshe ido numfashinta na sauka a hankali tana mata sannu, sai da ta ga alamar tayi bacci sannan ta mike ta fita, Imaan bata dau lkci tana bacci ba ta tashi ta dalilin ciwo da kirjinta ke mata, ta dinga juye juye kan gadon hawaye na xuba idonta, bude kofar dakin aka yi Mujaheed ya shigo, ya karasa kan gadon yana kallonta, daure fuska yyi yace "Me ya faru kuma?" Kirjinta ta nuna masa ta fashe da kuka, yace "Toh kukan ne xai sa ya daina ciwo, tashi xaune" mikewa tayi ta xauna da kyar, sai ga Anty ta shigo dakin, da sauri ta isa gadon tace "Me kuma ya faru Imaan, are you feeling pain anywhere?" Ta gyada kai tana nuna kirjinta, Anty ta dau Hijab ta nufi kofa tana cewa "Bari in je in kwaso magungunanta dai" Xaunawa Mujaheed yyi gefen gadon, ta koma xata kwanta yace "Kar ki kwanta" ta jingina da gadon tana goge idonta, ba a dau lkci ba Anty ta dawo da ledan maganin gaba daya, Mujaheed ya amsa yana duba maganin ya cire mata wanda xata sha, still yyi jin an bude dakin Umma, sai kuma ya ji muryarta tana tambayar inda yake, tashi yyi da sauri ya tafi bayan kofa ya tsaya, Anty ta tabe baki ta balli maganin ta dau table water ta mika ma Imaan, bude dakin aka yi Umma ta kare ma dakin kallo kafin ta tabe baki ta kulle, Shi dai yana tsaye bayan kofar, Anty ta sa Imaan ta kwanta bayan ta sha maganin sannan ta kallesa tace "Don Allah ka fita min a daki malam, tunda aikin xumuncin ma ba so ake kayi ba, kai ma kuma tsoron yi kake, yau ko da ace baka san Imaan ba a matsayin ka na likita ka ganta a wannan hali ai baxa ka ki taimaka mata ba balle tana yar uwarka halak malak, Allah dai ya shiryi mahaifiyar ka" shi dai bai ce komai ba, bayan karin mintuna uku ya bude dakin ya fita. Anty na xaune kan darduma bayan ta idar da magrib Imaan ta tashi daga baccin da ya kara dauketa, Anty tace "Sannu ya jikin Imaan" a hankali tace "Na ji sauki" Anty tace "Toh shiga bayi kiyi alwala ki xo kiyi sllh" ba musu ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito Anty ta mike kan darduman ta fita, Imaan ta sa Hijab dinta ta hau kai ta tada sllh, tana ta xaune kan darduman bayan ta idar sai ga Anty ta shigo da plate din abinci dakin. Imaan na gama ci ta mike rike da plate din tace "Anty sae da safe" Anty tace "Au baxa ki kwana nan ba" murmushi tayi ta make kafada ta nufi kofa, Anty tace "Toh baki fada min ko na meye atamfar ba" Ta juyo da sauri tace "Lahh, Ammi ce tace in kawo maku ankon bikin Anty Halima" Anty tace "Ashe abu ya xo dai, toh ki ce mata xan shigo gobe" Imaan tace "Toh" Anty tace "Allah ya sauwake Imaan" murmushi tayi a hankali tace "Ameen" daga haka ta fita, tun da ta sakko downstairs umma ke mata kallon tsana tana tabe baki, Imaan dai bata ko kalleta ba ta nufi kitchen rike da plate din, Rahma ce kitchen din ta gama wanke wanke, sai Mujaheed dake tsaye yana xuba ruwan Lipton daga teapot a cikin mug, Imaan xata ajiye plate din, Rahma tace "Kinga plate mai datti a wajen ne malama" turo baki tayi ta dau morning fresh ta bude xata wanke plate din, Rahma tace "Ya M.A in debar maka abincin ne xan fita?" Ya harareta yace "Abincin da ku ka cika yaji ko wanda ba yaji?" Yar dariya tayi tace "Ya Mujaheed yajin fa ba yawa" tsaki yyi yace "Ance maki ban yi tasting abincin bne ku dinga cika ma mutane ya ji a abinci kamar mayyu" Tace "Toh in maka cous cous?" Yace "I will take tea" Imaan ta gama wanke plate din ta juya ta fita kitchen din. Kallonta Ammi ta dinga yi bayan ta shigo tace "Ya jikin Imaan" tayi murmushi tace "Na ji sauki Ammi" daga haka ta nufi dakinta Ammi ta bi ta da kallo. Karfe sha daya saura Ammi ta shiga dakin Imaan, ganin tayi bacci ta tasheta tana mika mata wayar hannunta tace "Me ya sa kika kashe wayar ki" Imaan na murxa ido tace "Kila mutuwa yyi ba charge" Ammi tace "Toh idan kin gama ki maido min wayata daki" Imaan tace "Toh" sannan ta kai wayar kunne tace "Daddy ina yini" Daga daya bangaren ya amsa yace "Why is ur phone switched off" ta langwabar da kai tace "Daddy ban sa a charge ba tun jiya" yace "Toh kiyi kokari ki sa ya jikin?" Tace
Chapter 8 · 0% Book details