← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 300

Sashe 23

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hatta islamiyya Imaan bata iya taje ba ranan banda bacci babu abinda take, xuwa lkcn jikin ya mata sauki sai dai rashin kwari, Daddy dake parlor a study area dinsa ya kalli Ammi dake parlon ita ma yace "It's almost six madam baxa ki tada Imaan ba?" Ta kallesa tace "Kafin magrib xan tasheta" yace "Amma jikin ba xafi koh?" Tace "Ehh ba xafi but she's weak" yace "Allah ya bata lafiya" a hankali Ammi tace "Ameen" bayan wani lkci ta kallesa tace "Am really disturbed with Imaans health ailment... She have suffered a lot but always claiming strong, and...." Sai kuma tayi shiru, a hankali ta ci gaba "I don't want to loose her" Daddy na kallonta yace "Allah plans best, ke dai ki ci gaba da yi mata addu'a a ko da yaushe wataran sai labari, Allah xai yaye mata" Ammi tace "In sha Allah" Bayan magrib Ammi na kitchen taji muryar inna a parlor, fitowa tayi ta gaida ta da ladabi tace "Sannu da xuwa inna" inna tace "Ina mijin naki?" Ammi tace "Ya fita masallaci" Inna tace "Daxu Imaan ta xo duk tayi wani fayau fayau da ita, jikin ne ya matsa mata koh?" Ammi tace "Ehh wllh, amma taji sauki ma yanxu, tana daki xata yi sllh" Inna tayi kasa da murya tace "Yanxu 'yar nan idan shi mijin nan naki boko ya gama cutarsa ya ratsa sa ta ko ina ke baxa ki maida hankali ki tashi tsaye kiyi ta kanki da 'yar ki ba? Fisabillilah meye laifin maganin gargajiya Aisha, komai sai ace sai asibiti ga na gargajiya kasadan?" Ammi tace "Gaskiya ne inna" Inna tace "Wllh malamin a bayan tsauni yake" Ammi ta d'an bude ido tana kallonta, tace "Ga aikinsa kamar yankar wuka, duk xata fitsare jaraban ta dawo kamar mutane, amma ni tsoron magana nake Bukar da Ahmadu ba kirki ne da su ba sai su karee min rashin mutunci suce boka ne alhalin ba boka bane kawai Allah ne yyi xamansa a bayan tsauni, ta rasulu ta sha xuwa can kuma ana kwana daya da rabi a hanya kafin a kai, tunda kika ji haka ai kinsan akwai kamshin nasara, tafiyar kwana daya har da rabi ai kuwa akwai nasara....." Shigowar Daddy ya sa tayi shiru, daddy ya gaida ta da ladabi ta amsa masa sama sama tana kallon Ammi tace "Kina ji 'yar nan bari in koma na bar kofa bude kada yaran gidan nan su min aika aika ga dambun nama ta can daki, dama Mujaheed sai xarya yake min tun safe, ko shi ya isa ya kwashe, yanxu dai yaushe mijin naki xai koma?" Ammi tace "Xuwa gobe in sha Allah" Ammi tace "Toh idan ya tafi ki taho sashina ki same ni mu karasa maganar a can don sirri ne" daga haka ta nufi kofa daddy na mata sai anjima ko tanka sa bata yi ba. Bangarensu Mujaheed inna ta nufa tana cewa "Ita kuma Amina bara inje inji ko lafiya ban ganta yau ba" Mujaheed ne xaune parlor sai Yusuf, Hajiya na dinning tana jera abinci Rahma na taya ta, gaba daya Mujaheed bai yarda sun hadu ranan ba sai yanxu da ta riskesa a parlor ta fito kitchen, Inna na kallon Yusuf tace "Kai ina uwar ka, lafiyarta yau bata xo gaisheni ba" Yusuf yace "Yanxu da daddaren nan xaki kamo hanyan xuwa nan inna" Hajiya ta karaso parlon tayi kasa da kai tana daga tsaye tace "An yini lafiya Inna" Inna tace "Rukayya idan Hadiza ce xa ki gaida ta a tsaye sandandan haka?" Juyawa Umma tayi ta koma ta ci gaba da abinda take ba tare da ta bata amsa ba, inna ta kara da cewa "Sannan kiyi min rai ki rufa min asiri ki daina gaisheni kwata kwata a gidan nan idan kin gan ni, don Allah bana bukata, wnn ae kanki kike munafurta, kuma Allah ya tsine ma gaisuwar" Wani kallo Mujaheed ke ma inna fuskarsa daure, inna tayi kwafa tace "Mu xuba dai, xamu ga mai kwashewa, ae kema ga naki d'an ya isa aure ba don ya tsaya shashanci ba xaki ji ko da dadi ko babu" mikewa Mujaheed yyi yace "Ke dai ba dai alkhairi ya kawo ki nan ba sai fitina da complaint, haba don Allah, gaba daya ba a ta6a maki dai dai...." Inna ta bude baki tace "Ni kake xagi Mujaheed?" A fusace yace "Mu bar sa a hakan" daga haka ya wuce ta kamar xai tashi sama, Yusuf ya bi sa da wani kallo, tuni Umma ta shige kitchen ranta fari fat duk da haushinsa da take ji, Yusuf ya mike yace "Yi hakuri muje in raka ki" Inna ta fara matsar kwalla tace "Isuhu kaga abinda Mujaheed ya min ko? Da ina kusa da shi babu mai hanasa make ni.... Ina mahaifin ku yake" Yusuf yace "Ke dai mu je, Abba bai dawo ba" Da kyar Yusuf ya lallabata suka fita parlon tace "Wllh in har Mujaheed zae ci gaba da xaman gidan nan sai dai ni in tafi" Yusuf ya danne dariyarsa suna isa part din su Imaan ta bude kofa, daddy dake xaune yana duba laptop ya mike ganinta tace "Bukar babu abinda Mujaheed ya mance bai gaya min ba yanxun nan daga nayi ma uwarsa gyara, sai ku xaba ko ni ko shi a gidan nan" daga haka ta rufe kofar. Yusuf dai tuni yyi gaba, suna isa part dinta ta rushe da kuka tace "Sai yanxu abun ke min ciwo isuhu, kai kaga wahalar da nayi da Mujaheed kare baxae ci ba wllh" Yusuf yace "Sai kiyi hakuri, Mujaheed din ki ne fa" a fusace tace "Mujaheed dinsu dai, bari dai mahaifin ku ya dawo xai gaya min ko shi ke koya masa ya min rashin arxiki" kiran Isha da ake yasa Yusuf ya bar part din inna, tare Daddy ya je gun Inna da Imaan bayan isha, Inna ta fito daga daki ta shimfida tabarma ta xauna tace "Wllh Bukar daga nace ma Rukayya ta daina gaisheni a gidan nan don na munafurci ne, shi kenan Mujaheed ya hayayyako min yana huci..." Daddy yace "Kiyi hakuri Inna, ina fita xan je in samesa yanxu" a fusace tace "Oh oh babu xancen samunsa, kawai ni ba na son ganinsa gidan ne ko kuma ni in tafi ai dama ya isa aure sai yyi ya koma gidansa baxan xauna tare da shi wataran ya mareni ba, wai ku me yasa baku san ciwon uwar ku ba, uwarsa fa na yi ma fada shine ya min rashin arxiki haka, kai ko ga ka xaune sandandan gabana kana bani hakuri, ya fi karfin ka ne mujaheed din ko kuma uwarsa ta fi naka ne, Ahmadu dai bai ba yaron tarbiyar da ya ratsa jikinsa ba wllh" Daddy ya mike yace "Xan dawo anjima inna" daga haka ya nufi kofa tace "Yauwa, ka titsiye sa sai ya gaya maka ko ni sa'arsa ce kafin ya bar gidan" shi dai bai ce mata komai ba har ya fita, Inna tayi kwafa tace "Xai san ya ta6a uwar su yau" Imaan dai na kwance kan kujera tana kallonta, Inna tace "Ni na ma fara tsoronsa tunda abinda ya zama kenan yanxu" Imaan tace "Toh ke me ya kai ki bangarensu" inna tace "Ya za ki ce min haka 'yar nan, ni da gidan d'a na kuma kice me ya kai ni?" Imaan dai bata ce komai ba, Inna tayi kwafa tace "Ke kin ga wahalar da nayi da Mujaheed?" Imaan tayi dariya tace "Ae ke dama kullum sai kice kin yi wahala da kowa" Inna tace "Kee na Mujaheed k'are baxai ci ba, ni nasan me nake cewa, ina fa tsaye bakin kofar dakin haihuwa daga safe har dare sannan aka haifesa, sai kin ga wahalar da ya ba uwar d'an banxan, ai ko aka haifosa lafcece ya kusa biyun wani jaririn, duk ya cika asibiti da kuka nyaaa ke kina gani kinsan sadauki aka haifo, gashi jajir da shi fari hulll, gashin kansa kuwa ga bak'i ga cika yanda kika san d'an balarabe, ke ki bari kawai, nan dai muka koma gida na wanke sa tass, baki ga uwarsa ba lkcn yar siririya kamar xata karye ba yanxu da ta ci kudin d'a na iya ci ba ta koma kamar buhun masara, kullum zanyi wanka da sassafe daga gidana in tafi gidan Ahmadu yi ma fitsararren yaron nan wanka, don babu abinda uwar ta iya wai tsoron jaririn ma take don bala'i, a haka har yayi wata uku ya koma yanda kika san bredi wato ya xama wani lukeke, ga kyau tsantsa, ba sai uwar tayi ta cika masa nono yayi ta tumbudi ba duk k'arni??" Imaan ta fashe da dariya har da kyakyatawa tace "Shi yayan?" Inna tace "Wllh shi, to ni ko ina xan iya kazanta da k'arni, oh oh nan na taka mata burki, ga uwar kazama dn har sannan tana tashen kuruciya ni fa ko abincin gidan bana iya ci da, ana haka har Mujaheed ya kai shekara biyu, ba sai naga ana neman hallaka yaron ba, ba shi da aiki sai kukan banxa, fitsari a tsaye kashi a tsaye, ga uban shan yogurt, to da yake ba yanda na raini ubansa ba kenan bakina a leko na daukesa, kin ji mafarin komawansa waje na kenan, kuma Mujaheed bai bar gu na ba sai da uban ya biya masa kudin karatun likita a kasashen turai bayan ya gama sakandari, to ace banyi wahala da d'an banxan yaron ba kuwa, tsakaninsa da iyayensa fa sai dai bayan kwana biyu yaje ya gaishesu ya dawo, ko k'uda bana yarda ya ta6a min shi balle shegun kishiyoyina da duk suka mace yanxu, Allah dai ya ji kansu amma shari'ar mu da su sai a lahira...." Imaan tace "Ni lokacin ma ba a haifeni ba koh?" Da mamaki Inna tace "Oh oh kaji wata magana kamar na ta6a66u, wa ke ta ke, ke da aka haifa jiya jiya, a hannuna fa kika fado, ai wannan labarin da nake baki a lkcn mu duk mun dauka uwar ki juya ce...." Imaan ta mike xaune ta hade rai tana kallon inna, inna ta gyara xama tace "An auro uwar Mujaheed da shekara uku fa
Chapter 23 · 0% Book details