Sashe 103
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
hakan, Inna tace "Toh ai hakan yafi ma, kinga babu ta yanda xai dinga cutarki kuma, wahalan da yayi a kanki a baya Allah ya saka masa, idan kuma biyansa yake son ayi sai ya fada min nawa ne bai gagareni in daga daya daga gidajena na gado in siyar in biyasa ba, kuma ba karamin aikin Bulasawa bane ya siya min wani ma a kasashen turai in xuba yan haya" Murmushi imaan tayi ta mike ta dauko mata dankunnen da Sadeeq ya bata, inna na budewa tace "Wannan ai gwal ce, a ina kika samo Imaan?" Imaan tace "Shi ya bani" Inna ta xaro ido tace "Mujaheed din???" Imaan ta hade rai tace "Sadeeq dai" Inna ta saki wani kabbara tace "Kinga abinda nake nufi ko, to a xamanin nan wa xai ma naka haka?? Wllh ki rike yaron nan da kyau kai ko su Maimoon kada ki yarda su san abinda kike ciki balle wancan mutumin Mujaheed, 'ya yan Ahmadu ba wani tsoron Allah garesu isasshe ba, duk yan bakin ciki ne, ki bar wannan gu na in ajiye maki, ana nuna ma su Ahmadu dama cewa xa su yi a mayar tunda ba hankali ya ishe su ba, shi ma mutumin nan Mujaheed yanxun nan xaki ga ya shigo wai gaisheni bai san ni damuna yake ba, maxa dauka ki wuce da shi ciki kada...." Bata rufe baki ba aka bude kofa, Abba ya shigo da sallama Mujaheed na biye da shi, Inna ta boye dankunnen a karkashin carpet, a hankali Imaan tace "Ina kwana Abba" Abba yace "Lafiya Imaan, naji baki da lafiya, ya jikin naki?" Kallonta Mujaheed yyi da sauri, tace "Naji sauki Abba" Abba yace "Toh Allah ya sauwake" tace "Ameen" kallon inna tayi tace "Inna zan je dauko kayana" inna tace "Toh yi maxa" tashi tayi ta nufi kofa ta fita, Mujaheed ya fara danna waya ya kai kunne sai kuma ya mike ya fita yana cewa hello, Imaan na shiga parlon ta nufi dakinta don har Daddy ya fita ganin bata ga motarsa a parking space ba, tana dauko kayanta ta ji an bude kofa, ta juya da sauri tana kallon kofar dakinta, can dai ta nufi kofar ta murda, Mujaheed ta gani tsaye kusa da kofar dakin nata, Xata gudu ya fixgota waje fuska daure yace "Ni dodonki ne kike gudu na?" Kuka ta fara yi a rikice taki yarda su hada ido tace "Ban son hka ni ka sake ni yaya" kallonta ya dinga yi kafin yace "Meyasa kike gudu idan kin gan ni" sosai xuciyarta ke bugawa tace "Ba komai, ni ka sake ni plss" ya sauke idonsa daga kallonta, can yace "What's wrong with you?" Da kyar tace "Ni na ji sauki" saketa yyi ya juya ya fita, ta durkushe wajen har sannan xuciyar ta bai daina bugawa ba. Da yammacin ranan Imaan na durkushe bakin tap din inna tana alwala kamar ance ta daga kai taga Sadeeq yana tahowa, da sauri ta rufe gashinta ta xaro ido, murmushi yyi, yana isowa inda take murya can kasa yace "Good evening dear, sae ynxu xa ki yi la'asar?" Bata iya tace masa komai ba ya tsaya bakin kofa yyi sallama cikin cool voice dinsa, Inna ta fito daki tana amsa sallaman, shiga yayi tace "Au, sannu da xuwa Bukar ashe kai ne" ya xauna yana murmushi yace "Ina yini kaka?" Tace "Lafiya lau Bukari, ya aiki?" Yace "Alhmdllh mun gode Allah" tace "Toh ya xafi xafi, ko da yake ma akwai Ac ko ina yanxu" Yayi dariya yace "Haka ne kaka" Tace "Toh madallah, bari in kawo maka ruwa da lemo" bata jira cewarsa ba ta debo masa su a fridge ta ajiye, tace "Toh nayi tuwo na ajiye maka ina bacci wannan mutumi Mujaheed ya shigo ya cinye"