Sashe 130
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ne mai sauki?" Dariya Daddy yayi yana kallon Mujaheed, Mujaheed ya kalli Inna ta gefen ido bai dai ce komai ba, Umma ta wani daure fuska tana hararan Inna ta gefen ido, Ta Rasulu tace "Toh kayi hakuri Mujaheed, abinda bayan bikin da sati daya kawai sai ka xo ka dauketa ka mayar da ita gidan naka gaba daya, ohh sa6o turken Wawa" Inna tace "Ae shine na ga, nayi kokarin fahimtar da shi hakan amma ya kasa kwantar da hankalinsa, sai in koma can gaba daya Imaan kuma ta dinga xuwa duk Juma'ah ta koma lahadi" Daddy dai sai murmushi yake, Imaan ta saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, dauke kai tayi da sauri, Inna tace "Toh ni dai ta Rasulu ga ki ga Bukar yau, sai ki masa bayanin mutumin nan na bayan tsauni a tsanake, tunda ni na kasa fahimtar da shi da Ahmadu suna ganin kamar ko boka ne, Ni ko me xai kai mu gun boka mu masu tsoron Allah" ta Rasulu tace "Wllh Bukar ku maida hankalin ku don sai anyi da gaske da 'yar nan taka Imaan, tana da makiya ne ba na wasa ba, sannan wannan ciwace ciwacen nata ma ance ba banxa ba da sa hannu, sai an tashi tsaye kyam kada a kai mu a baro, bangaren aure kuma ance xata auri wanda ke bala'in sonta, wasu xa su yi murna da auren wasu kuma bakin ciki da hassada baxai bari su yi ba, wasu kuma takaici baxai yarda su yi murna ba, sannan da matsalaloli iri iri a xaman auren, matsaloli masu girma ba dadin ji kuwa, ni dai ba fata nake ba amma gaskiya abun ba dadin ji, kuma ance sai ta cika maka parlor da jikoki, toh ni abinda ban gane a nan ba shine... Kyashin fidda kudi kake a nema ma tillon yar ka lafiya ko kuwa kudin ne baka da shi Bukar?" inna tace "A'a sai dai kyashi, amma yana da shi wllh, Toh wllh sai ma kin tafi bayan biki xa su xo su sameni shi da d'an uwan suce in rabu da ke ba hanyar kirki kike nuna min ba, Toh wai dama Allah ba yace mu tashi ya taimake mu ba??" Daddy ya kasa daga kai, ta rasulu ta saki salati tana tafe hannu tace "Sai su ce ki rabu da ni kuma?" Inna tace "Wllh kuwa tatas xa su min suce in raba kaina da ke, ai ga shi nan xaune da ransa ba sharri na masa ba kullum na kawo masu xancen sai su gwaleni suce karya ce inyi ta kaina, to ni ya xan yi da su??" Mujaheed ya sunkuyar da kai sai murmushi yake, imaan ta boye fuska bayan kujera tana dariya kasa kasa, Daddy dai ya kasa dago kai, Ta rasulu tace "Dago kanka ka kalle ni Bukar, wllh wannan 'yar taka idan ba a tashi tsaye kanta ba duk sai mun shiga uku a duniyan nan, idan ma xaka fiddo kudi ka fiddo kudi a nema mata magani ta xama mutum, tunda har kuka iya karyata ni kai da Ahmadu to xa ku iya karyata Asabe ma" Inna tace "Yo na nawa kuma? Ai sun ma karya ta ni, sai dai Allah ya shirye su, ni dai na yafe masu" Daddy dai kansa na kasa, Ta Rasulu tace "Yanxu bayan biki sai ka ba Asabe dubu dari, idan ma ya kama muje tare da ita da Imaan din ne sai duk mu tafi...." Inna tace "Haba sai kace xa ki cuce ni, ai kawai ki je ke daya ba komai wllh" Daddy yace "Toh Allah ya kai mu xa a bada" Mikewa yayi yace "Na gaisheku xan je in huta" a tare suka hada baki wajen cewa "Toh Allah maka albarka" yace "Ameen" sannan ya fita parlon yana girgixa kansa. Umma da duk ta hada xufa gaba daya jikinta tana murmushin karfin hali tace "Toh Inna ayi hakuri da wannan din don Allah, ni xan koma in ji da baki" Inna tace "Toh ai ya fi babu, Allah dai yayi albarka" tana murmushi tace "Ameen" ta fice parlon da sauri tana share xufar goshinta a ranta kuwa hamdala take da Allah ya bayyana mata Ta Rasulu. Washegari Thursday duk yan matan gidan na ta shirye shiryen fita saloon da yin lalle, ita dai Imaan sai kumbure kumbure take...