Sashe 233
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Imaan ta tsaya jikin motar sai dai bata yarda ta kallesa ba, ta gefen ido ya dinga kallonta ya bude driver seat ya dauko takarda da biro, jinginar da takardar yyi jikin motar ya fara rubutu a kai, satan kallansa tayi ganin rubutu yake kan takardar ta ji gabanta ya fadi, lkci daya ta sunkuyar da kanta tana jan fingers dinta, ya gama rubutu a takarda ya linke yana kallonta yace "Hope you are now happy?" Bata yarda ta kallesa ba ta gyada masa kai kawai, ya d'an yi shiru sannan yace "But I want to let you know one thing Imaan before handing this paper over to you" ita dai kanta na kasa, jin yyi shiru bai fadi one thing din da yace xai gaya mata ba ta kallesa taga kallonta yake, da sauri ta sauke kanta kasa xuciyarta na bugawa, ya bude motar ya shiga a hankali yace "Xagaya ki shigo ki ji abinda xan gaya maki..." Ta girgixa kai tace "Ka gaya min a nan" yace "I want to say it while looking at u in the eyes, so that baxai yi fading memory din ki da wuri ba, ko da ba ma tare you won't forget it Imaan, it's almost a piece of advice..." Ta hade rai tace "Ni dai ka bani takardar in wuce" ya girgixa kai yace "Baxan baki ba idan baki shigo kin saurareni ba, I assure you wannan maganan da xan maki wataran xai maki amfani" Kallonsa tayi sai dai bata ce komai ba, kuma bata xaga ta shiga motar ba, yace "Duk lkcn da kika shirya jin abinda xan gaya maki I will give you ur divorce content, but not today anymore..." Daga haka ya ja kofar motar xae rufe, ta fashe da kuka ta rike kofar da sauri tace "Toh ka rubuta min abinda xaka gaya min a wani takardan ka bani gaba daya mana" Ya wani hade rai yace "Cinye ki xan yi idan kika shigo motar? Kinsan Allah baxan baki takardan nn ba idan baki shigo kin saurareni ba" Dauke kai tayi kamar me naxari sai kuma ta xaga a hankali ta isa daya side din, d'an murmushi yyi ya rufe side dinsa ya jinginar da kansa da kujera, tana xagayowa ta bude front seat ta shiga ta xauna ta d'an saci kallonsa taga murmushi yake, still tayi da farko, sai kuma ta sake kallonsa, lkci daya ta yunkura xata sauka motar ya wani fixgota ya jawota ya rufe kofar gbam ya sa ma motar lock, a mugun tsorace ta dinga jijjiga kofar tana cewa "Meye haka Yaya??" Bai ko kalleta ba ya tada motarsa ya bar layin, kuka ta dinga yi tana kallonsa a rikice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yaya don Allah ka bari, where are you taking me to, plss ka tsaya ka bude min mota in sauka, wayyo innaa...." Driving kawai yake bai ko kalleta ba, ta fixgosa cikin kuka tana jijjigasa tace "Don Allah ka bude min in sauka Yaya, ina xaka kai ni??" da hannu daya ya mayar da ita kan kujera ya wani hade rai ba tare da ya kalleta ba idonsa a kan titi yace "Kika sake rikeni sai na falla maki mari..." Ba karamin tsorata tayi ba jin babu wasa tattare da shi, hakan yasa bata sake rikesa ba ta dinga kuka tana kiran Inna tana bubbuga kujeran motar, Sun yi nisa sosai ya daura mata well folded takardan hannunsa kan cinyarta yace "As I promised, here is it...." Kuka kawai take tana kallonsa kamar ranta xai fita, yace "Dauki takardan ki bude ki karanta, ba saki kike so ba, to gashi na rubuta maki" kin ta6a takardarn tayi, ya juya ya kalleta fuskar daure, da sauri ta dau takardan hawaye na xuba idonta tana shessheka, yace "Open it now" hannunta na rawa ta fara warware takardan tana kallon abinda ya rubuta kamar hakw.... "Xan sake ki on one condition, the condition is... Xa ki haifa min yara guda biyar duk masu kama da ke, duk yaron da yyi kama da ni bbu shi a cikin lissafin, just 5 of ur look alike...." Ji tayi gabanta yyi wani mugun faduwa ta sake takardar tana kallonsa, wani murmushi yyi yana kallon titin gabansa yace "Yes... Sai ki shirya conceiving daga daren yau" ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka da karfi tana kiran Inna, driving kawai yake yana murmushi, wani hotel ya kai su, yana parking harabar hotel din ya juya yana kallonta, har lkcn kuka take sosai, ya bude motar ya fita ya xagayo ta inda take ya bude seat din yana kallonta yace "Come down..." Kin dago kanta tayi bata kuma fasa kukan da take ba, xaro ido tayi ta dago da sauri jin daukarta xai yi ta hadiye kukan da take cikin rawar murya tace "Wllh xan sakko Yaya, wllh xan sakko" Ya daure fuska yace "To sakko" ta hadiye abu da kyar ta fito motar tana shessheka tana bin haraban hotel din da kallo gabanta na bugawa tayi kasa da murya pleadingly tace "Don't Forget from the beginning kai ka koya min daukan ka matsayin yayana, kar ka manta a matsayin Yaya na dauke ka tun ban san kai na ba, why will u bring me to a hotel all of a sudden plss?" Yace "To show u ni ba yayanki bane, and after today I don't think xa ki kara kirana yayan ki" xaro ido tayi tana kallonsa, ya kulle motar xai kama hannunta ta fixge da sauri ta kara fashewa da kuka, kallonta ya tsaya yi sai kuma yace "Daukar ki kike son inyi kenan koh?" Ta girgixa masa kai cikin tashin hankali tace "A'a yace "To mu je" tafiya ta fara yi toward direction din entrance din hotel din yana biye da ita, tana waigowa, he couldn't just stop smiling, amma da ta juyo sai ya hade rai, kujera ya nuna mata bayan sun shiga reception din hotel din yace "Sit" kin xaunawa tayi tana hawaye, ya kama hannunta ya tafi da ita gun kujerar ya xaunar da ita yana kallonta, hade kai da gwiwa tayi tana jin kamar ta kurma ihu ko xata ji dadi, ya juya ya koma gun ma'aikatan babban hotel din, bayan kusan minti goma ya dawo inda take ya duka dai dai kanta yace "Tashi mu je...." Ta daga kai da sauri cikin rawar murya tace "Don Allah Yaya kayi hakuri ka mayar da ni gida Ina rokon ka don Allah ba don ni ba" D'aga ta yyi ya kama hannunta suka wuce sama xuwa room din da aka basa don kar ma ta ja masa attention din mutane, a door ta tsaya bayan sun shiga ciki, ya kulle kofar ya cire makullin jiki yana kallonta calmly yace "Ke da gida kuma sai deal din mu ya tabbata, I mean 5 kids...." Durkusawa tayi on her kneels tana kuka sosai tace "Don Allah ba don ni ba ka mayar da ni gida Yaya xa a dinga nemana fa" Ya durkusa gabanta shi ma a hankali yace "A neme ki bayan kina tare da mijin ki??" Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu kamar yanda shi ma yake kallonta... Inna ce xaune parlon Daddy ta yafa xaninta a kai, kai kace bayerabiya ce, fuskar nan nata a tsuke, Daddy da shigowarta parlon tana rafka uban sallama ya sa ya fito daga daki ya xauna yana kallonta yace "Ina yini Inna?" Ta kallesa tace "Lafiya lau Bukar... Kana ji na??" Daddy yace "Ina jin ki?" Tace "Toh... Ka san dai ni na haife ka, kai kuma ka haifi Imaan koh??" Shiru Daddy yyi bai ce komai ba, a fusace tace "Ka min shiru Bukar ko ba haka bane?" Yace "Haka ne" tace "To madalla, Bukar yau da ba don kai ba wllh ba bbu uwar da na hada da wannan yarinya Imaan, kawai ni dai nasan na haifeka kai kuma Allah ya baka ita, to ya xan yi tunda d'an da na haifa ya haifeta, ya xan yi nace??" Shi dai Daddy kallonta kawai yake, Rai bace ta ci gaba "Yanxu ace Imaan xata bar bangarena baxata jira in gama tsafatace bandakina in fito ba tace min to Inna ni na tafi? sbda walakanci sai ta tsallake kamar tababbiya tayi wucewarta ga farfesun da wannan mata Amina tayi mata ta bar min shi a bude a parlor duk dattin duniya ya fada kai, sannan ta bar min kofa a bude domin ba ma sauro daman shigowa su cuce ni, wllh raina yyi mugun bacewa don ni ba haka na ma Iyayena ba kai ma kuma ba haka ka min ba, to wacece kuma imaan fisabilillahi xata min haka, a wangale fa ta bar min kofar Bukar kaji abinda yafi min ciwo kenan, ni nace lallai dole sai Imaan ta xauna bangarena dama?? To wllh ta fito ta tafi ta kwashe tsummokaranta dake kwambodi na kada in watsa su titi ba ruwana, ni xata kawo ma raini ta walakanta, dama tun da yamma naga take takenta, Banda Ahmadu da ya jaza mana wnn bala'i na aura mata katon d'an sa uban me dama xan ci da ita a sashina??" Daddy dake ta kallonta yace "To ai bata xo nan ba..." Inna tayi shiru ta kalli kofar dakinta, sai kuma tace "Bata nan kuma?" Daddy yace "Bata xo nan ba" mikewa Inna tayi da mamaki ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, part din Abba ta wuce, tana daga tsaye bakin kofa tana kallon Aunty da ta mike ganinta tace "Amina yarinyar nan bata yo nan ba?" Aunty tace "Wai imaan?" Inna tace "ita" Aunty tace "A'a bata xo nan ba gaskiya" Inna ta gwalo ido ta shigo parlon da sauri tace "Bata xo ba kuma Amina?" Jin muryar Inna Abba ya fito daga parlonsa, Inna ta nufe sa da sauri tace "Ahmadu ban ga imaan ba tun daxu wllh" Abba yace "Imaan kuma?" Inna da har jikinta ya fara rawa tace "Ehh na shiga wanke bandaki na fito naga babu ita a parlor sai farfesu" Su Maimoon suka fito tare da Maryam da tayi hijira bangaren Inna tun ran Friday, Aunty na kallonsu Maimoon tace "Ku tafi can apartment dinsu ku duba ko tana