← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 300

Sashe 80

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

abba" Abba yace "Ohk" Hijab ta sa har kasa ta fito parlon, ta gaida abba da murmushi fuskarta yace "Ya jikin mamana" tace "Abba ai na ji sauki" yace "Toh Alhmdllh, Allah kara lafiya" tace "Ameen" Abba yace "Ga watermelon nan you take much of it kin ji" a hankali tace "Toh nagode Abba, but...." Sai kuma tayi shiru, yace "But what?" Ta boye fuskarta tace "Abba ina son cin suya" Abba yace "Toh Mujaheed xai siyo maki yanxu" Mujaheed ya kalleta ta gefen ido irin kallon harara, Tana murmushi tace "Toh nagode Abba" daga haka Abba yyi ma Ammi sallama Mujaheed ma yyi mata suka fita. Abba yace "Idan mun fito part din inna sai ka tafi ka siyo mata, there is still time ai" Mujaheed yyi kasa da murya yace "Abba yanxu tare xa mu gun innan?" Yace "Of course, ban san urgent kiran da take min ba, it might even be something that isn't worth the call" Mujaheed yyi yar dariya yace "Dama xaka ga it's nothing that important...." Abba yyi murmushi yace "But we still have to listen, gudun matsala" Suna shiga parlon Inna ta shafe addu'ar da take kan darduma tace "Har ka iso kenan Bukar, to shi kuma wannan jelan da ya biyo ka fa?" Dariya Abba yyi ya xauna yace "Aa mun shiga duba mamana ne shine muka karaso nan din tare" tace "Atoh na gansa wani sandan sandan kamar basamude a bayanka" Mujaheed dai sae hararanta yake k'asa k'asa, tayi kasa da murya tace "Kana ji na Ahmadu?" Abba yace "Ina jin ki" tace "Kaga kujeran can da Mujaheed ya xauna?" Kai ya gyada mata yace "Na gani" tace "To wllh tllh a kai Bulasawa ya xauna" da mamaki Abba yace "Bulasawa kuma?" Tace "Eh, amma d'an sa ba shi din ba" Abba yace "Tohhhh.... a ina ya san ki?" Ta daga hannu da sauri tace "A'a ni bai san ni ba, a titi muka hadu yau kuma muka fahimci juna kwarai da gaske..." daga Abba har Mujaheed kallonta suka tsaya yi without blinking, can Mujaheed ya girgixa kai planning to get up and leave the parlor yaji tace "Ashe wai saurayin 'yar ka ce Imaan, amma algungumar bata ta6a sanar da ni ko da wasa ba, a wajen na gansu tsaye jikin santalelen motarsa, in gaya maka taji kunya tsamo tsamo da ta gan ni, ni dai ban kulata ba bakina a leko na taso keyarsa muka shigo cikin gida, d'an wajen Amadi Bulasawa mai gidajen man fetur sun fi dubu a arewa fa Ahmadu" dakatawa Mujaheed yyi da sauri ya juya yana kallonta, Abba na gyada kai yace "Tohh da kyau hakan" Inna tace "Kai fa kasan da kyau yaro, wato idan Allah yyi auren har kasan waje fa sai an fitar da ita an juye duk gurbatattun jinin jikinta dake ja mata lalura a sauya mata sabo, sannan kasussukan jikinta su ma duk sai an ce xa a sauya su ta rabu da ciwace ciwace na har abada, kasan fa bbu abinda turawan nan basa iyawa in dai da naira, to ga naira dai faca faca ta samu, ae ni bayan fitarsa sai da nayi ya ma ake kiran sujjadar nan na godiya ga Allah?? To ni dai nayi wllh kuma na dade goshina a kasa" Dariya kawai Abba yake yana kallon mahaifiyar tasa, Mujaheed dae sai juya counter din hannunsa yake, inna ta marairaice tace "Ahmadu ka rufa min asiri ba abun dariya bane wannan, sannan yaron fa duk ya damu wai xai turo magabatan sa nan ba da dadewa ba ayi xancen aure, kasan su kuma manyan mutane basa son kwalo kwalo kada a bari wannan yaron ya kubce ma jikata in shiga uku gaskiya" Juyawa Mujaheed yyi ya dinga kallonta, Abba yace "Haba maganar aure kuma Inna, ko secondary fa bata gama ba" Inna ta wani tsuke fuska cikin d'aga murya tace "Allah ya tsine ma sakandarin, sakandarin banxa ga abun arxiki kana xancen sakandari, ko a gidansa wllh xai bari ta karasa, baka gansa ba dogo yanda kaga wannan mutumin dake kusa da kai a xaune, shi ma da kyar idan baya daga karafunan nan na turawa don kirjinsa duk a tale, kana ganinsa kaga d'an boko don gilashi ne ma a idonsa, toh irin wannan ne baxai bari ta karasa sakandarin jaraban ba idan anyi aure, gaskiya Ahmadu ku maida hankalin ku sosai a kan maganar nan da nake gaya maka, wllh kullu yaumin fargabana mijin da Imaan xata aura tunda ga yanda Allah ya halitto ta, mai rufin asiri kadai baxai iya da lalurorinta ba sai hamshakin mai kudi, da yau ace Bukar ya tara yara kamar yanda ka tara to fa da imaan bata kai labari ba don nasan ba xai tara uban kudin da xai dinga kashewa kan ciwonta ba, to astagfirullah kaga amfanin haihuwan kadan ba da yawa ba, to yanxu dai ga yaro matashi kyakkyawa d'an masu kudi ya fito, bari ma kaga abinda ya ban Ahmadu"
Chapter 80 · 0% Book details