← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 240 OF 300

Sashe 240

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mujaheed na gama parking a compound ya kashe motar ya bude ya fito, gate ya tafi ya kulle ya dawo, Safeenah da ta fito motar tana mika ta sauke ajiyar xuciya tace "Har hankalina ya kwanta dear, i prefer here than kaduna unlike kwanaki da muka xo naji duk ban son garin, yanxu kam I like it here..." Shi dai bai ce mata komai ba ya nufi entrance din gidan rike da takeaways din da yyi a hanya, tace "But wait, foodstuffs din fa Dear, ka bar su a booth, my bag is there also..." ba tare da ya juyo ba yace "we will take them in later..." Bin bayansa tayi suka shiga gidan, ya xauna saman kujera bayan ya ajiye ledojin abincin hannunsa ya jinginar da kansa da kujeran don duk ya gaji sosai, ko kadan shi dama bai son driving me nisa, Safeenah na murmushi ta tsaya bayan kujeran tana massaging shoulders dinsa a hankali tace "Bari in je sama in hada maka ruwan wanka baby, nasan ka gaji, shi sa nace ka bani driving din inyi ka ki...." Shi dai bai ce komai ba yana sauraronta, tana gama fadin haka ta cire mayafinta ta ajiye saman kujera xata wuce sama ya bi ta da kallo yace "A'a kar ki damu baxan yi wanka ba yanxu" ta juyo tana kallonsa tace "Oh really, amma idan kayi ai xaka fi samun relieve ae dear, anyway mu je sama in maka tausa toh" cike da shagwaba ta fadi hakan, bai ko kalleta ba ya mike ya dau ledan abinci daya yace "Ni fa I am okay, I just need rest...." Ta langwabar da kai tace "To mu je ka kwanta my dear...." Bai ce komai ba ya nufi stairs, jin tana biye da shi ya tsaya a staircase din sannan ya juya yana kallonta yace "Tot you said you are hungry ga abinci can kuma kin bari downstairs" ta tabe baki tace "No apple din da na ci daxu a hanya ya isheni, nima hutawa xan yi, all my body is just aching" Bai ce komai ba ya ci gaba da tafiya tana biye da shi har suka isa corridor din dakuna hudun dake jere, tsayawa yyi dai dai kofar dakin da yake amfani da, ya d'an saci kallonta ganin dakin ta nufo yace "You use the other room Safeenah" Da mamaki take kallonsa, sai kuma tace "Why? Beside tunda muke xuwa gidan nan na taba amfani da wani dakin banda wannan da muke using tare? Baka taba ce min inyi amfani da wani daki ba ai" Ya juya yana kallonta da kyau yace "Ohk we are not sharing it this time around, you choose from any of the other rooms, this is a master bedroom" wani kallo Safeenah ta dinga yi masa daga sama har kasa, can tace "What's wrong with you Mujaheed, why are u behaving this way?? dama mun ta6a raba daki tunda muka yi aure da kai? Ko kuma wani sabon walakancin ka tsiro?" Ya shafa kansa murya can kasa yace "Plss Safeenah I am tired bana son magana, I told u I need rest, idan baxa ki shiga any of the rooms ba ki koma parlor" yana fadin haka ya shige dakin ya sa makulli, Safeenah ta wani xaro ido tana kallon kofar da mugun mamaki, ta fi minti daya tsaye tana tunanin wannan kuma wani sabon walakancin Mujaheed ya kirkiro mata? Tabdi ai ko wahala kawai xai daukar ma kansa don maganin sa xata yi ba na wasa ba, da wannan tunanin ta sauka downstairs a fusace xuciyarta na tafarfasa, don sosai ranta ya baci... Mujaheed ya ajiye ledan hannunsa yana kallon Imaan dake bacci har lkcn, takawa yyi ya isa kusa da ita ya xauna gefenta, a hankali ya kai hannu forehead dinta ya ji temperature dinta normal, Bude lumsassun idonta tayi tana kallonsa, sai kuma ta dauke kai a hankali ta matsa daga kusa da shi ta juya masa baya, yace "Kinyi sllh?" Kin basa amsa tayi ta turo baki, idonsa ya sauka kan darduman da ke shimfide dakin alamar tayi sllhn, yace "Tashi ki ci abinci" ta hade rai tace "Ni baxan ci ba" yace "Koh??" K'in cewa komai tayi, ya sa hannu ya daga ta, ko ba a fada masa ba yasan next reaction dinta hakan ya sa ya maxa ya juyo ta ya rufe bakinta ya hade rai sosai yana kallonta, ta 6ata fuska kamar xata yi kuka cikin sanyin murya tace "Ni dai ka maida ni gun Ammina" Mikewa yyi ya dagota ya dawo da ita kasa kan darduman da ta bari a shimfide fuska daure yace "Ga abinci nan ki dauka ki ci" ganin kallon da yake mata ta jawo ledan a hankali hawaye na taruwa idonta ta bude ta ciro take away din shinkafa da kazar da ya siyo mata sai table water da five alive drink, spoon ta dauka ta debi shinkafar ta fara ci a hankali, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawa babu, can yyi murmushi ya tafi kan gado ya kwanta hade da lumshe idanuwansa, bayan kusan minti biyar ya bude ido to see if she is eating the food, kazan abincin ya ga ta dauka tana ci as if her happiness depend on it don ba cin wasa take ma kazan ba, suna hada ido ta juya da sauri bayan ta cire naman a baki, murmushi Mujaheed yyi ya mike xaune ganin ta ajiye kazan yace "Wa kika ajiye ma?" Ta turo baki tace "Ni baxan ci ba" kallon bakin da take turo masa kawai yake.... Inna ce xaune kan kujera a parlonta tana saka gogaggun kayanta a sabon Ghana must go din da ta sa Mai gadi ya siyo mata aka bude kofa hade da sallama, Daga kai tayi tana amsa sallaman ta ajiye set din riga da xanin hannunta tace "Sannu da xuwa Ta Rasulu" Ta Rasulu ta cire Hijab din jikinta ta linke da kyau ta ajiye tace "Ke kuma ina xa ki da gana mas gau?" Inna ta tabe baki tace "Kayana nake hadawa ta Rasulu, sam bani da 'ya yan nuna ma duniya, shine naga gwara kawai in tafi gidan Bala in xauna, duk me xa a min a can xan fi shanyewa tunda nasan ba jinina yyi min ba" Ta Rasulu ta xauna tace "Me kuma suka maki 'ya yan??" Inna tace "Fisabilillahi ta Rasulu ina laifina don nace duk inda xa a nemo min Mujaheed a nemo min shi in ji dalilin da xai dauke min jika ya gudu kamar d'an fashi, ta Rasulu babu lefe babu sadaki babu komai kawai ya samu tsaleliyar yarinya a bagas ya tafi da ita ko uban meye ma'anar haka oho, wato ga sadaka an basa, to wllh ubansa Ahmadu ma yyi kadan balle shi sa karan kada miya, Jikata tafi karfin ayi sadaka da ita, kawai yaro tantiri dai ya shigo min gida ina wankin bandaki ya arce min da jika tsakar dare kawai sbda yana shan wiwi, to ta Rasulu shan wiwin nasa kuma sai ya kare a kai na? Don wannan ni ya ci ma mutunci ba kowa ba wllh, snn ace ayi shiru a xuba masa ido yaje ya lalata min jika? Kinga Hadiza, Ahmadu da Bukar duk gantalallu ne Allah na tuba, sam bbu wanda ya dau wani kwakkwaran akshan a kan batun nan, yanda kika san abun kirki Mujaheed yyi ko kuma shi halitto min jika, idan kika bibiya ma duk sun san inda ya tafi da ita marasu imani, daxu fa har gidansa naje a unguwar dosa basamuden da ya ajiye bakin get yace min ai gidan fanko ne bbu kowa ciki, ni dai ba yarda ba na shiga na gama xagaye na naji shiru bbu alamar kowa shine fa na fito na dawo gida na sa aka siyo min jaka nake xuba kayana, haka kawai yara sun gama rainani sun maida ni shashasha, tsakanin Imaan da Mujaheed fa gantalallen kaza, ni dai ban ta6a ganin ya siyo mata ko da tsinke ne ya bata ba kamar dai yanda wnn yaro d'an albarka Bulasawa ke yi, to wannan mutumi xan dau jika in ba ma, wllh baxata sa6u ba, maxa ya dawo min da Imaan ba yanxu xata tare ba...." Ta Rasulu na girgixa kai tace "Toh shi Mujaheed ko dai hau ne ya fada masa xai aikata wannan barna haka? Ina ya tafi da yar mutane bai bada hakokkin aurenta ba, haka kawai ya cuce ta yyi mata ciki a banxa" Inna ta rushe da kuka tace "Imaan ina ta isa daukan ciki ke kuma ta Rasulu, da kuwa ya cuceta, duka duka nawa take? Ai kamata yyi a xaunar da shi a karanta masa illan hakan, ina laifin ta d'an kara gwabi, to ga dai Safara'u har yau shiru sai dai ta ci tayi kashi, ban gane kan abun ba" Ta Rasulu tace "Yanxu dai kiyi hakuri ki maida kayan nan, tafiya ba taki bace...." Inna tace "A'a gidan Bala xanje gwara inje suyi ta taka ni baxai min ciwo ba don bbu abinda na hada da su na dai san uwarsu kishiyata ce ta aure min miji ban ji ba ban gani ba" Ta Rasulu tace "Asabe nace maki bbu xancen tafiya, ga abun al-ajabi na xo da shi..." Inna tayi shiru tana kallonta, Ta Rasulu tace "Toh dai asiri mummuna aka lafta ma Bulasawa yace ya fasa auren Imaan...." Inna tayi tagumi tana kallon ta Rasulu a hankali tace "Sai aka ce maki wani la'anannen ne yyi asirin Ta Rasulu?" Ta Rasulu ta tabe baki tace "Toh me shi a gidan nan yake tare da ku wllh, ba a dai ambato min suna ba, amma a nan me shi ke kwana yake tashi, amma ke wa kika xarga Asabe?" Inna tace "Allahu Akbar, Rukayyar Ahmadu ce" Ta Rasulu tace "Nima ita na raya" Inna ta bude baki tayi mitsi mitsi da ido tayi shiru tana kallon Ta Rasulu, can tace "Ikon Allah, wato kaikayi ne ya koma kan mashekiya ba shakka, kin lura duk ta fi kowa daga hankali a auren da aka daura da Mujaheed???" Ta Rasulu tace "Wllh kuwa, biri yyi kama da mutum, ni naga ma duk ta rame ta xabge tayi baki, yanxun
Chapter 240 · 0% Book details