← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 300

Sashe 35

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

yi a gidan nan, ke dai magana magana magana baya kare maki, wanda ya kamata da wanda bai kamata ba haba don Allah, ni bana son irin wannan abun, ki shekara kina bada labarin kowa amma banda nawa, ba ruwanki da rayuwata da yanda aka haifeni ke kenan kowa kice xaki ba labari baki san bako ba, kawai ke dai kiyi ta magana babu naxari haba don Allah" sake baki tayi tana kallonsa, mikewa Imaan tayi tana hadiye dariyarta sum sum xata bar wajen inna tace "Ke dai wannan 'ya ta Bukar anyi munafuka wllh, to da kika gaya masa dukana xai yi ko ko, ina ce yarinyar da xai aura ce, kuma laifi ne don na bata labarinsa? Me yasa ban samu masu gadi na basu labarin ba? Saboda bai shafesu ba, komai fa da ku ke gani a rayuwar nan kamawa yake, yarinya ta xo gaisheni sai in xauna muna kallon kallo da ita??" Imaan ta turo baki tace "Ba wani nan, yaya har ce mata ta yi da yunwa aka haifo ka duniya kana ta ihu a asibiti, kuma saboda shan nono bakin ka ya xama d'an karami haka, wai sai kaje yawo ka dawo sai ce ma Umma nono sai ta baka ka sha, shi ma ya Yusuf sai na gaya masa tace an haifesa fiyot kamar kyanwa kamar bakwaini" Girgixa kai Mujaheed yyi ya bar wajen a mugun fusace Imaan ta bi bayansa da gudu tana kyalkyala dariya, Inna ta share kwallar idonta tace "Ni dai ba don gabana aka haifi muguwar yarinyar nan ba wllh sai ince ba jininmu bace, don gulmarta ya wuce hankali ya dauka, banda haka yaya xa ta dinga hada mutane fada a gida haka, shi kenan ni kuma bani da Ikon bada labari, ni daga yau ma kar ta sake xuwa min na yafe abincin, yarinya dai guda daya sai hada bala'i a gida, gashi ta hadani da Mujaheed xata tafi ta hada ni da isuhu kuma, ni dai bari Ahmadu ya dawo a ja mata kunne kar ta sake xuwa min, Bukar dai ya Haifi jaraba"
Chapter 35 · 0% Book details