Sashe 168
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe biyu imaan ta fito daga bedroom dinta bayan tayi wanka ta canxa kaya xuwa daya daga sabbin kayan da Daddy yayi mata har kala biyar na waliman, sosai lace din ya amsheta, Ammi ta gama jera abinci kan lallausan carpet dake parlor, Tana kallonta tace "Ga abincin ku ke da Daddy" Imaan ta karasa ta xauna kan carpet din tana bude warmers din tana murmushi, Daddy ya fito daga daki ya karaso cikin parlon ya xauna saman lallausan carpet din shi ma yana kallonta yace "I am proud of you sweetheart" Dariya tayi tace "Daddy bayan ni ba ku ban gift ba kai da Ammi" yace "Let lunch first" Plate ta dauka ta xuba masu abincin da daddyn nata, Ammi dai na xaune parlon har suka gama cikin abincin, daddy na kallonta yace "Hope you will also pass ur up coming exams with flying colors by the grace of God" Imaan tace "Sure daddy" Daddy yace "Maa sha Allah" Makullin mota ya fiddo aljihunsa ya ajiye kusa da ita yace "And this is my gift" Imaan ya wara ido ta dau makullin tana kallo yace "A car?" Ammi dai sai kallonsu take, cike da jin dadi Imaan ta rungume Daddyn nata tace "I love you Daddy, Allah ya bar min kai, ya kara girma" Murmushi yayi yace "Ameen, gobe xa a taho da motar but you won't ride anytime soon, may be after ur waec" Imaan da ta rasa inda xata sa kanta sbda murna tace "Toh daddy, Allah ya kai mu, nagode Sweet dad, Allah ya saka maka da alkhairi" Yace "Ameen, clear this plates now" Mikewa tayi ta kwashe duk warmers da plate din ta kai kitchen, ta fito daga kitchen kenan aka danna bell, Mikewa Ammi tayi ta wuce dakinta, Imaan ta tafi ta bude Kofar, still tayi ganin Sadeeq tsaye hannunsa rike da leda, sosai gabanta ya fadi lkci daya ta juya da sauri ta bar bakin kofar Daddy na kallonta yace "Who's there?" Kasa basa amsa tayi ta wuce dakinta, bayan few seconds Sadeeq ya shigo parlon da sallama murya can kasa, Daddy na ganinsa yace "Welcome son" Sadeeq na kirkiran murmushi ya karasa ya ajiye ledan hannunsa ya xauna kasa shi ma ya gaida Daddy da ladabi, daddy ya amsa da fara'a yana tambayarsa ya mutan gidan, yace "Alhmdllh Daddy" Ammi ce ta fito daki sanye da hijab, ganinsa ta sunkuyar da kai tace "Sannun da xuwa" ya kalleta yace "Ina yini Ammi" tace "Lafiya lau, ya gidan?" Yace "Alhmdllh, fatan an watse taro lafiya" Ammi tace "Alhmdllh, mun gode Allah" dakin imaan ta nufa ta bude kofar ta shiga ciki, xaune ta ganta can karshen gado ta wani hade rai, Ammi tace "Wa kika ce ma Sadeeq xai xo gidan nan?" Kamar xata yi kuka tace "Ammi ni wllh ban sani ba kawai ganinsa nayi" Ammi tace "Toh sai ki tashi ki tafi ki kai masa ruwa da drinks ki dibar masa snack" Ammi bata jira cewarta ba ta fita dakin ta wuce nata, Mikewa Imaan tayi ta dau hijab dinta fari har kasa ta saka sannan ta fito, ta wuce kitchen ta hada ruwa da drinks sai glass cup a tray, ta debi snack a wani plate ta daura a kan tray din ta fito, kanta a kasa ta iso parlon ta duka gefensa ta ajiye, Mikewa Daddy yayi ya dau wayarsa yana kallon Sadeeq yace "Let me make a call outside" Sadeeq yace "Toh sai ka dawo daddy" daga haka daddy ya fita parlon, Imaan xata tashi ya rike hijab dinta cike da damuwa murya can kasa yace "Plss listen to me Imaan, don Allah ba don ni ba ki tsaya ki saurareni, am begging you plss...." Kasa cewa komai tayi ta xaune wajen ta hade kai da gwiwa ta fara kuka a hankali, duk ya rikice mata ya duka on his kneels yace "Don Allah kiyi hakuri ki yafe min Imaan, it's a mistake that will neva repeat itself again, don Allah ki min rai kiyi hakuri, I have neva for once had the intention of making you angry" ita dai ta ki cewa komai kuma ta ki dago kanta bata kuma fasa kukan da take a hankali ba, cikin sanyin murya yace "Kin ji Fatima, ki yafe min don Allah, wllh bani da nufin cutar da ke, I love you with every breathe of mine, I am wishing u to be the mother of my kids, ban taba ma ya mace irin son da nake maki ba, I Neva knew what true love is sai a kan ki, ni ba fasiki bane Imaan you can ask Mariya, sure I do flex with friends and I am a player, but i am very selective when it comes to mingling with girls, and mind you... ni ba maxinaci bane I can swear to you by Allah who made me ban taba ba, I am a type of person that find my opposite gender so irritating in every aspect, don't forget where I was born and raised, sure it's strongly against the teaching of our religion but kema kinsan to hug or kiss someone is part of our lifestyle back there, a haka na taso cikin su, I tried my very best getting rid of that while here in Nigeria kuma Alhmdllh there is improvement, wllh Imaan ban maki haka da niyyar in cuce ki ko in 6ata ki ba, mata ma dake kawo min kansu ban bata su ba sai ke da nake son aure? Kuma yanayin da nake shiga idan muna tare is something that I have neva experience all my life, that's why kika ga ko xuwa wajen ki bana son yi duk irin son ganin ki da nake I try my best staying away from u, plss Imaan kiyi hakuri ki yafe min, sharrin shaidan ne, don Allah ba don ni ba ki dago kanki ki kalleni in baki hakuri, na kuma maki alkawarin daga this very moment har xuwa ranan da Allah xai sa a daura mana aure idan ke matata ce baxan sake xuwa gidan ku ba, baxa kuma inyi requesting mu hadu ba, xa dae mu dinga waya kawai...." sai a sannan ta dago kanta hawaye na xuba idonta, lkci daya idonsa ya kada shi ma cikin sanyin murya yace "Don Allah kiyi hakuri Imaan" a hankali tana goge idonta tace "Na ji?" Kamar xai mata kuka har lkcn yana durkushe kan kneels dinsa yace "Kin hakura" a hankali ta gyada masa kai, yayi murmushin karfin hali yace "Toh nagode Imaan, Allah maki albarka" sunkuyar da kanta tayi, ya dauko ledan da ya shigo parlon da shi ya ajiye gabanta yace "This is for you, I am very proud of you today, Allah ya baki ikon amfani da karatun ki" ta kasa cewa komai, ya mike yace "Ki ce ma Ammi na wuce, thanks much for forgiving me" Bata iya tace masa komai ba ya nufi kofa ta bi sa da kallo, yana bude kofa kafin ya fita murya can kasa tace "Nagode" ya juya ya kalleta yayi murmushi sannan ya fita ya kulle kofar parlon, Bude ledan tayi taga tsadaddun turarruka ne a cikin ledan har kala biyar. Daren ranan Imaan na dawowa part din Inna ta je kai mata abinci suka hadu da Mujaheed xa shi gun Innar, Ya katse wayar da yake yi yana kallonta, ta wara ido tace "Yaya baka tafi ba?" Yace "Ehh wait for me a parking space yanxu xan fito" tace "Parking space?" Yace "Ehh" tace "Tohm" wucewa tayi shi kuma ya karasa part din Inna, Parking space din nasu ta tafi gun motarsa ta tsaya ta jingina jikin motar, Bayan kusan minti bakwai sai gashi, yana kallonta yace "I saw ur video... reciting, kinyi kokari kadan, they are still some corrections in ur tajweed, so ban ma san amfanin kyautar da aka dinga baki ba, may be dai Muryar ki ne yayi masu dadi" on a serious note ya kare maganar, xaro ido Imaan tayi tana kallonsa a sanyaye, lkci daya ta bata fuska ta sunkuyar da kanta, ko kallonta bai yi ba yace "Matsa in bude motata" a hankali ta matsa masa daga jikin motar ya bude, ta fara tafiya xata koma part dinsu, bin ta yyi da ido yyi saurin jawota, kuka ta fara yi a hankali, ya dawo kusa da ita yana murmushi yana kallonta gently yace "I was only joking Lil sis, ur recitation was superb, I love it, and that was what I expected" turo baki tayi tana kallonsa ya ja hancinta yana kallon eyeballs dinta murya can kasa yace "My future kids will have no problem with recitation of the holy Qur'an" Bai yi xaton xata ji abinda ya fada ba coz his voice was so low, as if he just murmured the sentence, ya ga ta xaro ido tace "Ehh?? Ur future kids that their mother is already hating me from day one" sai kuma tayi murmushi tace "Ba ruwana, idan dai sun xo gida xan dinga koya masu in sha Allah..." Yyi murmushin sa mai kyau yana shafa kansa yana kallonta, Jan hancinta yyi bai dai ce komai ba ya bude back seat ya fiddo Laptop sabo dalll, ya mika mata yace "My promise 3 years ago" wara ido tayi ta rungume sa tightly tace "Waow... Nagode yayana, I love ittt, you kept to ur promise" Mujaheed ya ji gaba daya kafafuwansa sun kasa daukansa ya jingina da motarsa ya lumshe ido and hold her closely to himself, Saketa Mujaheed yyi da sauri jin an bude kofar apartment dinsu, Imaan ma ta ja baya tana kallon direction din, Umma ce ta fito tare da Hajiya Saude xata rakata, imaan na ganinta dama ta bar wajen da sauri ta dau hanyar apartment dinsu, Umma ce ta fara hangota sai kuma ta fara kalle kallen parking space din don ganin ita da waye tana ganin Mujaheed ta bi bayan imaan da mugun sauri Hajiya Saude na biye da ita, fixgota Umma tayi tace "Uban me kike yi gun Mujaheed, me ya kawo ki wajen sa, meye wannan a hannun ki??" Umma ta kwace laptop din tana xaro ido tace "Meye wannan din ya baki?" Mujaheed dama na ganin haka ya