Sashe 231
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Alhaji Bulasawa da wani frnd dinsa, Alhaji Bulasawa na tsaye kan Sadeeq sai kallonsa yake duk da bacci yake, kana ganin Alhaji kasan kasan damuwa ne sosai tare da shi, Can ya juya ya kalli Abba a karo na farko tun shigowarsu yace "Alhaji can you pls do something about this pls, I don't want anything to go wrong with my son, and yana da matsalar xuciya dama from the beginning, though it's not critical but the condition he is now can make it, don Allah ina bukatan taimakon ku ba wai don na isa ba, ku duba wannan lamarin" Da damuwa sosai yyi maganar, Abba dai kallonsa kawai yake ya kasa cewa komai, Daddy ya ja kujera ya xauna ya jinginar da kansa hade da lumshe ido, Abba ya sauke idonsa yace "In sha Allah xa a duba ka kwantar da hankalin ka Alhaji...." Alhaji Bulasawa yace "Toh na godiya" Mummy ce ta shigo ward din tare da Mum din Mariya, ganin Sadeeq ta fara kuka ta ki karasawa ciki, mum din Mariya ta karasa a sanyaye tana kallon Sadeeq din.... A haraban hospital din Abba ya kira layin Mujaheed to see if he can reach him, luckily kuwa ya shiga, Mujaheed na dagawa Abba yace "Muhd Ina son ganin ka a gida yanxu" Mujaheed ya d'an yi shiru sannan yace "Ina Zaria yanxu Abba, da Magrib xan shigo" Abba yace "Am expecting then" daga haka ya katse wayar ya xauna saman kujera yana kiran Allah a xuciyarsa, Mujaheed ya d'an yi murmushi ya ci gaba da abinda yake a office dinsa. Da daddare Imaan na parlor xaune ta sa pepper soup din da Aunty tayi mata a gaba amma ko spoon daya bata kai baki ba, Inna na bathroom dinta tana aikin wankewa tunda daxu da safe bata samu ta wanke ba, Bude kofar parlon aka yi Imaan ta daga kai da sauri Mujaheed ya shigo, tashi tayi kamar warce aka tsikara xata gudu yyi maxa ya rikota, ta fashe da kuka jikinta na rawa tace "Yaya don Allah ka bari bana so..." Ya juyo da ita yana kallonta, ganin yanda hawaye ke xuba idonta ya xaunar da ita ya xauna gefenta a hankali yace "Listen to me now Imaan..." Taki yarda ta kallesa har sannan jikinta rawa yake, murya can kasa yace "Kema kina son in sake ki koh?" Ta kallesa ta fashe da matsanancin kuka tana gyada masa kai, shiru yyi na kusan second goma, a hankali yace "Toh shikenan tunda haka kike so, but I don't have paper and pen here, mu je waje sai in dauka a mota in rubuta takardar in baki..." Daga haka ya mike, ita dai tayi shiru tana kallonsa amma hakan bai sa ta daina hawaye ba, ya kalleta yace "Toh mu je mana, ba dai haka kike so ba??" Mikewa tayi a hankali ta dau Hijab dinta ta saka sai kuma ta tsaya, yace "Mu je...." slowly ta fara tafiya ya bi bayanta yana murmushi, ita dai Imaan tafiya kawai take yana biye da ita yana kallonta har ta fita gate, satan kallon part din su yyi sannan ya fita gate din shi ma.....