← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 300

Sashe 212

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare Yusuf suka shigo parlon Abba da Sadeeq, Sadeeq yyi kasa da kai ya cire glasses din idonsa ya xauna saman rug ya gaishesu cikin sanyin murya, amsawa suka yi a tare suna kallonsa, Yusuf ya xauna shi ma yana duban Sadeeq da ya ki dago kai, calmly Abba yace "Hope all is well Abubakar?" Sadeeq bai ce komai ba kuma bai dago kansa ba, daga daddy har Abba kallonsa kawai suke, Yusuf ma haka, Can Sadeeq ya dago kansa ba tare da ya yarda sun hada ido da ko daya daga cikinsu ba a hankali yace "I am sorry I am saying this late, ina son don Allah ku min alfarma ayi hakuri da daurin auren nan yau saboda wasu dalilai...." Kallon mamaki Abba da Daddy suka shiga yi masa, Yusuf da ya xaro ido shi ma ya dinga kallonsa, Sadeeq ya shafa kansa murya can kasa yace "I think I am not ready for marriage now, I am sorry I am saying this at the die minute, but this is just d fact, ku yi hakuri...." Yusuf na masa wani kallo ya mike a mugun fusace yace "How dare you say such at this time, who do you think you can take for granted here...." Abba da gaba daya Sadeeq ya gama kulle masa kai cikin cool voice yace "What exactly are you trying to tell us here now Sadeeq.... What do you mean?" shiru Sadeeq yyi bai ce komai ba, can ya kallesu yace "I think it's good a fasa auren nan sai wani lkcn, ku min afuwa...." mikewa Daddy yyi cikin tsawa yace "You are very stupid...." Abba ya mike da sauri ya nufi d'an uwan nasa sanin xuciyarsa yana kallonsa a nutse yace "keep calm Abubakar, keep calm..." Mikewa Sadeeq yyi kansa a kasa yace "I am sorry..." Daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon, Yusuf ya bi sa da kallo da mugun mamaki, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shi ne kalmar da Abba ya dinga furtawa ya kasa tsaye waje daya, daddy ya koma ya xauna a hankali trying his best to be calm, Abba ma ya koma ya xauna har lkcn yana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, silent din kusan minti biyar ne ya biyo baya a parlon, kowa da tunanin da yake a ransa, can Abba ya daga kai ya kalli daddy, lkci daya wani tausayin d'an uwan nasa ya rufe sa, how will such thing happen to his only child, cikin sanyi Abba yace "Look Abubakar you need not to worry, haka Allah ya tsara kuma Alhmdllh, I am sending them their pride price immediately, sannan plss do not say anything to anybody about this yet...." Daddy dai bai ce komai ba ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe idonsa, Yusuf duk jikinsa yyi sanyi ya ma kasa kallon iyayen nasa ya rike kansa kawai, Abba ya mike walking round as if looking for a solution, sosai xaka ga damuwar dake tattare a fuskarsa, Daddy ya mike daga karshe calmly yace "Bani sadakinsu in mayar masu yanxu Barrister" sanin halin daddy yasa Abba yace "Xan maida da kaina Abubakar, ba sai ka je ba" duk ynda daddy yyi Abba ya basa sadakin kin basa yyi hakan yasa ya koma ya xauna xuciyarsa na tafarfasa, he just can't believe this is happening to his daughter, can Abba xauna ya dau wayarsa ya shiga kiran layin Alhaji Ahmad Bulasawa, sai da ya kusa katsewa ya daga, bayan sun gaisa Abba ya d'an yi shiru sai kuma a nutse ya shiga tambayar Bulasawa dalilin da yasa xa su yi masu abinda suka yi, Alhaji Ahmad Bulasawa dake sauraronsa keenly yace "I really don't get you Alhaji, me ke faruwa, anyi wani abu ne??" Mamaki ne ya cika Abba jin abinda Bulasawa ke cewa, bbu bata lkci ya shiga yi masa bayanin ynda suka yi da Sadeeq yanxun nan, cikin daga murya Bulasawa yace "He is seriously stupid, wato abinda ya xo yace maku kenan, to wllh ko ya ki ko ya so aure ba fashi, my reputation is above everything, ana saukowa masallaci dama daurin aure na nan bbu fashi in sha Allah, till we meet there...." Bai jira cewar Abba ba ya katse wayar, Abba ya kalli Daddy don wayar a hands free ya sa, Daddy ya girgixa kai yana murmushin karfin hali yace "I will never give out my daughters hand in marriage to that son of him, tunda har da kansa ya nuna baya auren that's the end, ba neman kai nake da Imaan ba, don't forget she is all I have got, da a cutar min ita gwara an cuceni ko wani irin cuta ne kuwa, we are returning their pride price and everything immediately, Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi, Allah yayi mata xabi na gari, bak'i da suka xo from far don taya ni farin ciki xan sallamesu ana saukowa masallaci in sanar masu bbu auren kuma, and I will forever be grateful coz they are all here bcos of my only child, in sha Allah xa mu je a daura auren Yusuf nata kuma Allah ya musanya mata da mafi alkhairi" daga haka daddy ya mike ya nufi kofa, Abba da duk jikinsa yyi sanyi sosai yace "Sadeeq" tsayawa daddy yyi amma bai juyo ba, Abba yace "Don't say anything about this to anybody, not even ur frnds, ka ji abinda nace" Daddy dai bai ce komai ba ya fita parlon kawai, Abba ya jinginar da kai so sad, Yusuf dai ya rasa abun cewa gaba daya he is just shocked, can Abba ya kallesa yace "Go nd get set Yusuf, it's almost time, and don't say anything to anybody yet" mikewa Yusuf yyi jiki ba kwari ya fita parlon Abba ya bi sa da kallo. Gida ana ta shagalullukan biki bbu abinda yasan me ke faruwa, Imaan dai tana bedroom dinta baccin da bata yi jiya ba duk ya dameta, daga karshe ta kwanta ta dinga bacci, bbu wanda ya tasheta cikin mutanen dake dakin don da ganin yanda take baccin ma kasan gaba daya she is restless sai juye juye take. Abba ya dau sadakin da su Bulasawa suka kawo ya tafi gidan da kansa don mayar masu don sosai ya gamsu da abinda d'an uwansa yace na cewar bbu xancen aure kuma tunda Sadeeq din ya fito da kansa ya nuna ya hakura to gwara kowa ma ya hakura ko don gudun kada ya jefa Imaan cikin wani hali, kuma hakan shine abu na karshe da xai so ma only child din d'an uwansa, ko kadan Bulasawa bai ji dadin kudin da Abba ya maido ba don kin karba yyi, Abba yayi masa bayani a nutse yanda xai fahimce me yasa suka yi haka ya kuma nuna masa dole su yi hakan don ceto imaan, ba irin kiran da Bulasawa bai ma Sadeeq a waya ba amma ya ki dagawa, Abba na murmushi yace "Toh kaga Alhaji, kawai Allah yyi masu xabi na gari, tunda kaga haka auren ba alkhairi bane garesu" Bulasawa dai ya kasa cewa komai amma gaba daya shi ma ransa ya sosu, Abba yyi masa sallama daga karshe ya bar parlon nasa bayan ya sanar masa xuwa gobe ko jibi xa a maido masu lefe, shi dai Bulasawa har Abba ya fita bai iya yace komai ba, can ya dau wayarsa ya shiga Kiran mahaifiyar Sadeeq, tana dagawa strictly yace "ki sameni parlona ynxu, kuma duk inda Abba yake I want him immediately, in sha Allahu kuma baxai kwanan min a gida ba yau, and he is returning all my asset that is with him today, I have nothing to do with him any longer" Bai jira cewarta ba ya katse wayarsa. Karfe daya saura Abba suka wuce masallaci tare da frnds dinsa da kawu Bala, sae kawu Audu, bayan ya samu waje yyi parking ya kira Daddy don ya ji yana iya, daddy ya sanar masa yana hanyar xuwa mosque..... Ana sakkowa masallaci aka daura auren Yusuf da Hafsat a kan sadaki dubu dari biyu, auren da jama'ah da dama suka shaida, sae kuma daurin aure na biyu da ake jiran waliyyan ango amma shiruu, wanda hakan yasa aka fara dago kila babu auren ne tun kafin su Abba su sanar da hakan, Abba na kallon daddy dake kusa da shi murya can kasa yace "Abubakar xan daura ma 'ya ta aure yanxu, auren da ina da tabbacin kowa xai yi alfahari da shi in sha Allah, ko ba ynxu ba kuwa, da raina baxan ta6a yarda ka ji kunya a idon duniya ba, kuma ikon da nake da shi a kan Imaan yasa xan daura mata auren huce takaici duk da banda ni da kai da Yusuf sai Bala bbu wanda yasan abinda ake ciki" Daddy dai sai kallonsa yake don tun idar da sllh ya ki cewa komai, Abba yace "Ka je a kai ne waliyyin ango, Bala kuma dama shine waliyyin amarya..." Yana fadin haka ya fiddo kudi a aljihunsa ya mika ma Daddy yace "This is 200k, sadakin da xaka bada...." Abba na fadin haka ya koma gun su kawu Bala da abokansa, ko kadan daddy bai yi welcoming idea din Abba ba, kwata kwata bai son ma imaan dole, bai son tashin hankalinta ya xama biyu, na rashin masoyi ga kuma aure without her consent, gashi bai san da wa Abba xai hadata ba idan kuma yace xai yi magana Abba sai yaga kamar ya nuna masa bashi da iko da imaan, gaba daya he was just confuse haka ya tafi dai don yin ynda Abba yace, Daddy bai taba xaton sunan da yaji an kira na angon ana daura auren, haka ya dinga kallon Abba ko kiftawa bbu, Yusuf kansa was more than shock ya kasa daina kallon iyayen nasa, can ya lumshe ido ya bude xuciyarsa na bugawa.... Abba ya sakar ma Daddy cool smile ganin kallon da yake masa, maimakon Daddy ya mayar masa sai ya dauke kai kawai. daga karshe dai Yusuf fita yyi to avoid gaisawa da frnds don gaba daya shock ya xame masa biyu..... Tun bayan call da Mariya tayi answering a dakin Imaan yanayinta ya sauya gaba daya, tafi minti
Chapter 212 · 0% Book details