← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 300

Sashe 158

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gefen Imaan dake bacci Mujaheed ya xauna a kan gadon Inna ya kai hannu forehead dinta yana kallonta, Bude ido tayi a hankali, ya ta6a jikinta xai yi magana Safeenah ta shigo dakin kamar an hankadota, rike kugu tayi tana kallonsu, duk da mamakin ganinta da Mujaheed yyi bai nuna ba ya dauke kai daga kallonta, Imaan ta mike xaune da kyar ta wani daure fuska, Mujaheed na kallonta murya can kasa yace "Wani maganin kika sha?" Magungunan da Sadeeq ya kawo mata daxu ta nuna masa, ya duka ya dau ledan ya fiddo drugs din yana kallonta yace "Wa ya kawo maki?" Shiru tayi ta ki cewa komai, ya hade rai yace "Am asking you" turo baki tayi ta koma ta kwanta, Safeenah dai sai kallonsu take rike da kugu, Inna ce ta shigo dakin tana kallon Safeenah tace "Safara'u kike ko wa, ba kya fita parlor ki bar su suyi sirri ba, kinsan fa komai nata ya sani, yanxu ganin ki sai ta ji kunyar gaya masa har da ciwon mara a abinda ya dameta, don Allah ki dan koma daga parlo" Safeenah dai bata ce komai ba sai murmushin karfin hali take tana sunkuyar da kai, Inna tace "Ae ba wani abu bane, bbu abinda Mujaheed bai sani ba na Imaan, yanda kika san Yaya mace haka ta mayar da shi tun bata kai haka ba...." Juyawa Safeenah tayi ta nufi kofa ta fice Inna ta bi bayanta tana waigo imaan tace "Dama ki rufa min asiri kar ki bata min xanin gado ki cuce ni, ba kowa gareni ba da xai wanke yanxu Mujaheed ba gidan yake ba" D'an murmushi Mujaheed yyi har inna ta fita, Can ya wani hade rai yana kallon Imaan yace "Wato kiran saurayin naki kika yi kika ce masa baki da lafiya koh?" Kamar xata yi kuka tace "Ni bani na kirasa ba yaya" fuska daure yace "Toh wa ya kirasa" a hankali tace "Inna" yace "Wa ya kira mata shi?" Imaan tace "Ni ban sani ba ina daki" Ya kara hade rai yace "Shine kika ce masa kina period koh?" Xaro ido tayi tace "Wllh ni ban ce masa ba Inna ce ta fada masa nima ai sai da naji kunya fa" tana magana tana turo baki, yace "Toh wa yayi maki alluran?" Shiru tayi, ya d'an mata tsawa yace "Answer me now" turo baki tayi tace "Inna ta min" sai kuma ta rufe fuskarta da sauri a pillow tana dariya a hankali, kallon ta ya dinga yi yana jin xuciyarsa na wani tukuki, a hankali ta dago tana kallonsa, ganin yanda ya daure fuska ba shiri ta shiga taitayinta strictly yace "Sai kika bude masa kaya ya maki allura yana kallon ki right?" Sosai ya bata dariya amma bata yi ba tana komawa baya a hankali tace "Ni a cinya nace ya min, kuma a nan ya min fa yaya, bari in nuna maka wajen ma" tana fadin haka ta dage gown din jikinta a hankali tana nuna masa lap dinta, a hankali ya sauke idonsa yana kallon fresh lap din nata, lkci daya yaji ransa yayi wani mugun baci xuciyarsa na tafarfasa, tayi murmushi ta rufe kafan tace "Kagani ai" fuska a tamke yace "When xa ku fara exams na first term?" Ta buda manyan idonta tace "Saura kusan four weeks ai Yaya" yace "Good ana gama saukan ku dama idan Inna xata taho gidana ku taho tare" ta xaro ido tace "Saboda me Yaya?" A tsawace yace "I am giving you instruction, don't question me" daga haka ya mike ya juya ya nufi kofa rai bace, ta bi sa da wani kallo bayan ya fita, murya can kasa tace "Tabb, waye xai je gidan ka, ni dai baxan je ba" Xaune ya tadda Inna kan tabarma ta daura kafa daya kan daya tana ba Safeenah labarin irin wahalan da tayi da Mujaheed tun daga ranan da aka haifo sa duniya.... Inna na kallon Safeenah da kyau tace "Ko ke baki ga bakin d'an tsut ba??" Duk da irin yanda Safeenah ta dinga dakewa coz at first she wasn't interested with the story gaba daya hankalinta na daki ganin Mujaheed bai fito ba har sannan, amma bata san lkcn da ta fashe da dariya ba har da sakkowa kasa tana kallon Inna, Inna ta hade rai tace "Ke Safara'u ba batun dariya ba wllh, ya tsotsi uwar ne ba kadan ba sai dai Allah ya bata lada, sai kin gansa wani narkeke da shi malam, don dama nonon Rukayya ba dai kyau ba gaskiya" Dariya kawai Safeenah take har da kyakyatawa, Inna ta tabe baki tace "Uhn ni dai ba ruwana" Mujaheed dai yayi still bakin kofar daki ya kasa karasowa cikin parlon, Inna tace "Toh wllh da ya dawo wajena yana da shekara uku sai...." Katse ta Mujaheed yyi fuska daure ta hanyar ce ma Safeenah "Tashi mu tafi" ita dai sai dariya take, Inna tace "Ya haka ina bata tarihi Mujaheed" Mujaheed yace "Toh sai ki jira idan an baki mai gadin gidan tarihi...." Inna tace "Meye laifina Mujaheed, matar ka ce fa kuma sai mu xauna tana kallona Ina kallonta kamar kishiyoyi" Mikewa Safeenah tayi tana dariya tace "Toh Inna mu xa mu koma xan xo ni kadai in sha Allah sai ki bani karshen labarin" Inna na washe baki tace "Toh Safara'u shiga ku yi sallama da Imaan din kiyi mata Allah ya sauwake" D'an dariyar dake fuskar Safeenah ya dauke bata dai ce komai ba ta shiga dakin, tsayawa tayi bakin kofa tana kallon Imaan dake xaune saman gado from head to toes, imaan ta wani daure fuska, Safeenah ta ja tsaki tana yatsine fuska ta fice daga dakin. Dai dai nan aka yi sallama bakin kofa, Inna ta mike da sauri tana amsawa tace "Bisimillah Bukar, Mujaheed ne kadai da amaryarsa, shigo" Sadeeq ya shigo parlon yana murmushi, hannu ya mika ma Mujaheed dake tsaye bakin kofa yana kallonsa, Mujaheed ya amsa still looking at him suka gaisa, Inna na washe baki tace "Toh xauna Bukar" Xaunawa Sadeeq yyi kan lallausan rug dake parlon, Inna na kallon Safeenah tace "Saurayin imaan kenan Safara'u, tana gama sakandari nan da wata daya xuwa biyu dama xa a fara maganar auren su, baki ga ba yaro mai kirki da sanin ya kamata wllh" Safeenah tana kallonsa tace "Sannu da xuwa" Sadeeq ya mata godiya yana murmushi, Safeenah ta nufi kofa tana kallon Mujaheed sannan ta kalli Inna tace "Toh Inna bari mu je sai na sake dawowa" Mujaheed yayi ma Inna sallama ya fita Safeenah na biye da shi, sai da suka d'an yi nisa ya tsaya yace "Ki tafi bangaren mu ki jira ni, I forgot i need to discuss something with grandma" da mamaki ta dinga kallonsa, can tace "Toh sai mu koma tare ai" ya wani hade rai yace "Wannan sirrinmu ne, do as I say plss" Bai jira cewarta ba ya juya ya koma parlon Inna, ta bi sa da kallo da mugun mamaki, Inna ta xubo ma Sadeeq abinci ta cika masa nama tam ta ajiye gabansa xata dauko ruwa kenan Mujaheed ya shiga, cike da damuwa tace "Naga abinda ya isheni.... mai ya dawo da ku kuma Mujaheed ba kun tafi ba, wllh shi kadai na ma girkin ban da ku...." Sadeeq bai san lkcn da ya fara dariya ba, Mujaheed ya wani hade rai yana kallonta, tace "Ni dai ba ruwana, mutane dai ba gaskiya meye kuma na dawowa bayan mun yi sallama kun tafi" Mujaheed bai fasa karasawa cikin parlon ba ya xauna, Inna ta ajiye ma Sadeeq ruwa da malt biyu tace "Toh ni ban san yanda xan yi da kai ba gaskiya Mujaheed, ko in jiko maka garin kwaki ina ma da gyada wllh" Sadeeq ya hadiye dariyarsa yace "Wllh Kaka ya min yawa xa mu ci wannan tare" Inna ta tsuke fuska tana kallon Mujaheed tace "Katon ba sai ya cinye gaba daya ba kana xaune Bukar...." Sadeeq na murmushi yana kallon Mujaheed da ya hade rai yace "Bismillah Dr" Mujaheed yace "Alhmdllh, I am okay" Inna tace "To maa sha Allah, maxa maida hankali ka cinye kayan ka Bukar, Ni dai nasan sai ka fita xai tsigaleni tass.... Toh wannan duk bai dameni ba tunda Allah ya ga xuciyata kai na ma girki, ban san da xuwansu ba" Sadeeq couldn't stop smiling ya dau spoon ya debi abincin ya kai baki bayan yayi Bismillah, Inna ta xauna tace "Ita ma imaan d'an kadan na debar mata gashi can rufe a kitchen, toh ni basu sanar min xa su xo ba da nayi girkin da su, meye a ciki don dai ka ba mutum abinci, kawai fa ganin mutumi nayi gantsantsan a kaina mata na tsaye bayansa, na ja bakina nayi shiru na basu hanya, shi sa na tafi kitchen na adana maka abincin ka kada su gani su tafi da ni a baki suce na masu rowa, kasan mutumin yau" Mujaheed dai bai tanka ta ba, ta gaji da xubanta tayi shiru, yana ta xaune har Sadeeq ya gama cin abinda xai ci, bayan Inna ta tabbata da gaske ya koshi ta kalli Mujaheed tace "Toh don Allah kayi hakuri ka ci sauran, kaga dai a nutse ya ci abincin irin na yan gayu" Sadeeq ya fara dariya ya kasa kallon Mujaheed dake kallon Inna ba yabo ba fallasa, Inna ta tabe baki ganin Mujaheed bai ce komai ba ta dauke abincinta ta wuce kitchen ta rufe, dawowa tayi tana kallon kofar daki tace "Toh imaan dakin xai bi ki fisabilillahi, ki fito mana" sai da Inna ta kara magana imaan ta fito da hijab, Sadeeq ya dinga kallonta, rakubewa tayi jikin kujera tana kallonsa a hankali tace "Ina yini" yayi murmushi yace "Lafiya lau, how are you feeling now" tace "Na ji sauki" yace "Maa sha Allah, hope you've eaten?" Ta gyada masa kai, Inna dai sai kallonsu take tana murmushi, imaan ta saci kallon Mujaheed dake kallonta fuska daure, Dauke kai tayi da sauri, Sadeeq yace "Toh shkkn kaka na cika alkawari tunda na dawo na ci abinci, ni xan koma" inna tace "Wllh na ji dadi Bukar Allah maka albarka, tashi ki raka sa ke" Kudi ya fiddo aljihunsa dubu
Chapter 158 · 0% Book details