Sashe 14
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
"Toh likitan ta fa?" Daddy yace "Yayi tafiya ne" Abba yace "Toh tunda Muhammad na nan ba sai ya dinga dubata ba kafin likitan nata ya dawo, ko gwara a tafi asibitin?" Daddy yace "Noo in xai dubata shikenan, dama don likitan baya nan ne xa mu je asibitin" Abba yace "Let me give him a call, na barsa sashin inna, idan ma asibitin xa a sai ya kai ta kawai" Yana kokarin kiran Mujaheed suka hangosa yana tahowa, Abba ya maida wayarsa, har Mujaheed ya isa parking space da suke tsaye kallonsu kawai yake, Ya risina ya gaida Daddy, ya amsa masa da fara'a, Abba yace "Imaan xaka duba Mujaheed, bata jin dadi" Sosai gabansa ya fadi ya kalli Imaan dake jingine da mota duk ta wani langwabe.