Sashe 194
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mikewa Inna tayi ta bude baki tana kallon Umma tace "Rukayya ita imaan din ce wata a gidan Mujaheed?? Ita Imaan din?? Ehh lallai ba shakka kin xama mahaukaciya, to wllh tllh Imaan ta fiye ma Mujaheed Safara'u sau dubu dari, wacece kuma Safara'u Allah na tuba?? Sannan yaushe kika san Allah da kike kokarin min wa'azi wai kar ta shiga daki ta duba yayanta? Toh kwanciya tace maki xata yi a dakin idan ta je?? Ko ko ce maki tayi bata da kwakkwaro kamar ki ne?? Ni dai na ga abinda ya isheni, ba kunya ba tsoron Allah kin kwaso jiki xalalo xalalo kin xo gidan surka kina girki a kitchen ita kuma tana sama wajen miji, anya Rukayya?? A'a tunda uwata ta haifeni ban taba gani ko jin haka ba wllh, Toh ni duk ba wannan ba, don bai dameni ba... Babban magana a nan shine gaskiya ban gane kan ciwon jikana ba, don wannan ciwo ba na Allah bane, tunda ya auri wannan mata Safara'u yayi bankwana da lafiya, yau ciwo gobe lafiya, yau fari gobe tsumma, To a kan me? Ita Safara'un yar wace gari ce in ji tukun kafin in san abun yi" Umma ta dinga mata wani kallo tana jin kamar ta tanka ta amma wata xuciyar na bata hakuri, fuska daure Safeenah tayi wucewarta kitchen tana kas kas da cingam ta bar su nan tsaye, Inna ta gyada kai tace "Toh kya ci uban ki kuwa ba dai jikana ba don kurwarsa daci ne da ita yarinya, in sha Allahu sai dai ki ci uwarsa da ta jajibo ki ba shi ba, kuma xaman ki saura kiris a gidan nan" daga haka ta ja hannun Imaan dake tsaye gefenta suka wuce sama tana huci, Umma ta bi su da wani kallo xuciyarta na tafarfasa tasan dai ko hauka take baxata tanka Inna ba, Inna ta bude kofar parlon dake sama ta shiga, Ganin Imaan ta ki shigowa ta fixgota a fusace ta nufi dakin Mujaheed da ita, Imaan dai sai bin ta take, kwance Mujaheed yake saman gado idonsa rufe, Inna na kallon empty robber din drip dake sakale ta rike ha6a tace "Ka ji jarababbu mayu, wai an sa masa ruwa yana daki, alhalin ga ruwa ya kare..." Bude ido Mujaheed yyi, Inna ta fashe da kuka a hankali ta nufesa tace "Sannu Mujaheed, in sha Allahu babu abinda xai sameka in dai ina da rai, asiri dai ya gama tonuwa na gano komai" shi dai gaba daya hankalinsa na kan Imaan da tayi tsaye bakin kofa ta ki shigowa kuma ta ki yarda su hada ido sai wasa da fingers dinta take, Inna ta xauna gefen gadon tana goge guntun hawayen idonta tace "Kwana nawa da aurenta ka fara jin canji a jikin ka??" Shi dai bai ce mata komai ba har sannan yana kallon imaan, Inna ta juya ta kalleta tace "Ke dai baki da kirki wllh, halin ki abun tsoro ne gaskiya, baxa ki karaso ki gaida sa ba" sai a sannan imaan ta kalli Mujaheed, suna hada ido tayi saurin dauke kai ta karasa cikin dakin ta duka kasa kusa da gadon a hankali tace "Ya jikin Yaya?" Bai tanka ta ba, Inna tace "Atoh, abinda ma da kyar ta biyoni Mujaheed, wllh Imaan bata da imaani, har fa ce min tayi toh ita ce bata da lafiya da xance a fasa kawo kayan aurenta yau sai wani satin sabida baka da lafiya...." Mujaheed dai ya kasa daina kallonta, imaan ta wani hade rai tana kallon Inna, bude kofar dakin aka yi sai ga Safeenah ta shigo da warmer a rufe da plate a hannunta, ko kallonsu bata yi ba ta karasa ciki ta ajiye ta xauna kusa da kansa tana wani yauki tace "Baby ka tashi ka ci ko kadan ne sai ka sha drugs dinka plss, bacci ma ya kamata kayi ka huta bayan ka gama cin abincin tunda sai ltr xa a sa wani drip din" Imaan ta dinga hararanta ta gefen ido, Inna ta tsuke fuska ta rungume hannu tana karanto addu'a a xuciyarta tana tofawa a duk angles din dakin, Mujaheed ya mike xaune ya cire duvet din jikinsa yana kallon Safeenah yace "You don't worry anjima xan ci, na sha tea yanxu" tace "Toh ayi maka pepper soup din ko appetite dinka xae dawo?" Da kamar baxai ce mata komai ba sai kuma yace "Ohk" Ta mike tana wani cat walking ta nufi kofar fita tana karkada jiki, Imaan ta wani tabe baki ta dauke kai fuska daure, Safeenah na fita Inna ta mike ta dau abincin ta bude window ta xaxxage gaba daya downstairs ta juyo tana kallon Mujaheed murya can kasa tace "Mayya ce Mujaheed...." Bude baki yayi yana kallonta da mamaki, ta kyabe baki ta cire Hijab dinta ta linke tace "Jira in je in soya maka wani gaskiya, Allah ba batun wasa ba an gano mayya ce amma kada kace mata komai tukun, a hankali ake kama barawo, anjima ta Rasulu tace min xata xo nan....." Bai san lkcn da yyi murmushi ba bai dai ce mata komai ba, kofa Inna ta nufa fuska daure ta fita xata kitchen ta masa girki, Imaan na ganin haka ta mike da sauri ta nufi kofa yace "Fatima" tsayawa tayi sai dai bata juyo ba, jin bai ce komai ba a hankali ta juyo tana kallonsa, taga kallonta yake, sosai gabanta ya fadi, kamar xata yi kuka tace "Na'am" jin yyi shiru ta karasa kusa da gadon ta durkusa tace "Ga ni" ya sauke idonsa daga kallonta yace "Ya preparation na exams?" A hankali tace "Lafiya lau, how are you feeling now?" Yana kallonta yace "Dama kin san bani da lafiya ashe?" Tace "Aa ni Inna ce ta gaya min daxu Allah ban sani ba" Bai ce komai ba hakan yasa tace "Xan je in taya Inna" yace "Promise me baxa ki wuce gida ba daga nan" murmushi tayi ta boye fuskarta da gado don abinda ke ranta kenan, ji tayi ya kamo hannunta ta dago da sauri yace "Kar ki tafi yanxu Imaan" ta turo baki tace "Bayan Umma tana nan, kuma matar ka sai wani hararana take yi, ni dai wucewa xan yi" yace "Toh kiyi xamanki a nan" ta xaro ido tace "Kaga Inna ta wuce fa, salon idan matarka ta shigo ta xageni ko" yace "Kina dai son wucewa kawai" tana murmushi tace "Toh naji baxan wuce ba, amma me ke damun ka Yaya? Ji fa ka rame sosai" Ya jinginar da kansa da gado murya can kasa yace "Ban sani ba" ta langwabar da kai tace "Kana likita kuma baka sani ba, or is about our last talk, I mean about the lady..." Shiru yyi yana kallon Ac dake aiki a dakin, murya can kasa yace "Yau xa a kawo kayan ki koh?" Dariya tayi ta boye fuskarta tace "Uhm nima ban sani ba" jin bai ce komai ba ta dago tana kallonsa, kallonta taga yana yi da manyan idanuwansa, ta sunkuyar da kai tana murmushi tace "Ehh yau ne" yace "And u are happy" ta turo baki ta ki cewa komai, sauke kafafuwansa yyi daga saman gadon ya nufi press dinsa ya fiddo gogaggen shirt xai saka a kan singlet da 3 qtr din jikinsa, Bude kofar dakin aka yi sai ga Safeenah, da wani expression ta dinga kallonsa sai kuma ta kalli Imaan a nutse tace "Malama tashi ki fitar min dakin miji, naga alama karuwancin naki ba iya waje ya tsaya ba har gida" Imaan na mata wani kallo tace "Karuwanci kuma? To sai dai in kece karuwa....." Bata rufe baki ba Safeenah ta sauke mata mari tana wani huci tace "Ni kike ce ma karuwa a dakin..." ita ma bata kai karshe ba taji saukan wani wawan mari da yasa ta ji dumm a kunnenta, da kyar ta juya tana ganin stars ta kallesa cikin rawar murya tace "Mujaheed. .." ya kuma wanke ta da wani mahaukacin marin ya fixgota yana huci yace "Kinsan warce kika mara Safeenah??" Safeenah ta xaro ido a tsorace tana kallonsa, sai kuma ta rushe da kuka cikin tashin hankali tace "Yanxu a kan wannan matsiyaciyar ka mareni Mujaheed, a kan wannan sauran ciwon....." Hankada ta yyi iya karfinsa don har sai da ta fadi kasa timm, Yana nuna ta calmly yace "Kece matsiyaciya ba ita ba" Safeenah ta mike da sauri ta fice dakin da gudu tana kuka, Imaan da hankalinta yyi mugun tashi tana kallonsa cikin rawan murya tace "Yaya me yasa ka mareta, ai xan iya ramawa da kai na, why did you slap her, you shouldn't have, beside umma fa na gidan" Mujaheed ya rikota cikin daga murya yace "Did you know what I felt da ta mare ki imaan?? Kinsan abinda naji?? Me yasa xata daga filthy hand dinta ta daura a fuskarki??" Ta dinga kallonsa da manyan idanuwanta ko kiftawa babu, yyi kasa da murya yana sauke numfashi a hankali yace "Wlh da ni ta mara baxan ko daga kai in kalleta ba, why will she slap you Imaan???" Kallonsa kawai imaan take ganin yanda idanuwansa suka kada sosai, lkci daya ya rungume ta ya lumshe ido, a hankali ta kwantar da kanta kirjinsa tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa tana shakan daddadan kamshinsa, gently ya dinga tafiya tana jikinsa har ya isa kofa ya sa makulli. Inna na kitchen tana aikin suyan dankali da kwai, Umma ma na kitchen din fuska daure tana dauraye kayan miya da xa ayi ma Mujaheed pepper soup, lkci lkci take xabga ma Inna harara ta dinga addu'ar da ma man gyadan dake kan gas din ya kware a jikinta kowa ya hutu a duniyar, Inna ta kwashe dankalin karshe a mai tana tabe baki tace "Ba ruwana, ni sai in sa Ahmadu ya tattaro min kayana ma in dawo nan gaba daya, don dai in masa girkin abincin da xai ci ransa kadai kar a cucesa, ni a ma kira min Ahmadun in gaya masa jikin Mujaheed ba sauki masu kawo lefen nan su dakata kawai lefe bai fi jikana ba gaskiya" Umma ta kalleta da sauri, sai kuma tayi kasa da murya tace "Lallai kam, ace duk yanda suke da Imaan baya nan