Sashe 284
Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
hijab dinta to gain access to her body, a fusace tace "Stop it Yaya" juyo da ita yyi ya fara kissing dinta gently yana daga hijab din, ta fara turasa amma ya ki sakinta, sun dau lkci sosai a haka amma gaba daya ta ki sakar masa jiki sai kukan take masa tana son kwace kanta, ya saketa daga karshe ya mike ya xauna gefen gado da idanuwansa da suka sauya kala, sauka take son yi daga saman gadon ya fixgota yace "You are only good at show casing unnecessary kishi, to warce kike kishi a kanta 6ata ta6a hana ni hakkina ba, ko da kuwa sau goma ne a rana.. I know what I am saying" Imaan tace "Sai kaje ta baka yanxu ai" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin, sannan ya gyada kai. Washegari gaba daya Mujaheed bai shigo dakinta ba yanda ya saba da safe, ita dai ta gama duk abinda take, ta fita xuwa kitchen ta hada shayi ta dawo parlor ta xauna, sakkowa yyi downstairs kasancewar ranan Friday ne sanye yake cikin milk shadda da yyi masa kyau sosai, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai, ya shigo parlon ya dau makullin motarsa yana kallonta don har snn kayan bacci ne jikinta yace "Sai yanxu kika tashi kenan?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ehh" yace "Ohk, xan je gida sai na dawo after Juma'at prayer" tace "Nima xan je gida" yace "A'a ki jira next week xan kai ki" ta wani hade rai ta kallesa, yyi murmushi yana shafa kansa ya dawo kusa da ita ya xauna yana kallon fresh legs dinta don kayan iyakar sa kneels yace "In sha Allah next week xa ki je ae" Bata ce komai ba ya amshi shayin hannunta ya jawota jikinsa ta fixge ta matsa daga wajen ta dau cup din shayin ta, mikewa yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallo, lkci daya ya juyo tayi saurin dauke kanta, yace "What will you be taking for lunch?" Ba tare da ta kallesa ba yace "I will sort that out" dawowa parlon yyi ya ajiye makullin hannunsa da waya ya koma sama, ta bi sa da kallo gefen ido, sai da taji budewar kofar parlonsa sannan ta mike da sauri ta dau wayarsa ta ga ya sa lock, kallon wayar ta dinga yi da mamaki kafin ta kashe ta ajiye ta koma da sauri ta xauna, ya sauko downstairs rike da Atm card dinsa ya dau waya da makulli ya nufi kofa yace "Sai na dawo" Bata ce komai ba har ya fita, ta ajiye shayin hannunta don gaba daya ji tayi ya fita ranta, imagining ta dinga yi wai gun Safeenah xai je, lkci daya taji hawaye ya kawo idonta ta jinginar da kanta da kujera tana jin xafi a xuciyarta. Sai kusan la'asar Mujaheed ya dawo gidan, sai bayan kusan minti talatin ya shiga dakinta ya ganta kwance idonta rufe ya karasa kusa da ita ya xauna yana shafa fuskarta a hankali yace "Lil sis" kin bude ido tayi yyi murmushi don yasan ba bacci take ba, ya kai lips dinsa nata ta bude ido da sauri ta dauke kai, shafa cikinta yyi yace "Ga abinci Inna ta bada a a kawo maki downstairs" ta mike xaune ta koma can karshen gado on a serious note tace "Bana son kana ta6a ni Yaya, I don't like it" shiru yyi yana kallonta, can yace "Kar na ta6a ki sbda me?" A takaice tace "Saboda bana so" yace "Ohk" daga haka ya nufi kofa yace "Farida ta kira daxu tana gaishe ki" daga haka ya fita ta bi sa da harara, sai kuma ta 6ata fuska xata yi kuka. Haka nan suka ci gaba da rayuwa gidan da gaske kuma ya daina ta6a ta iyaka ya siyo mata abinci da drinks ya ajiye mata, wani lkcn ya hada da gasasshen kaza wani lkcn kuma fruits, a ko da yaushe tana daki ita kadai, shi kuma yawanci yana parlonsa, duk dare dai xai shigo to make sure ta sha drugs dinta sannan ya wuce dakinsa yyi kwanciyarsa. A haka har yayi resuming aiki ranan Monday, karfe takwas saura ya shigo daki ya ganta kwance tana bacci sbda dadewa da tayi tana azkar bayan sllhn asuba, ya isa gabanta yana kallon skin dinta dake wani sheki, ya durkusa kusa da ita, ya fi minti biyu yana kallonta kafin a hankali yace "Imaan" Bude ido tayi, sai kuma ta mike xaune ta koma baya, ya mike yace "Xan wuce aiki, akwai kayan shayi downstairs with bread, I don't know ko xa ki ci egg ki soya yanxu kafin in tafi" ta girgixa kai tace "Baxan ci ba" yace "Ohk..." Daya wayarsa ya mika mata yace "If you need anything you call me, but don't call anybody with the phone" tace "Ni dai xan kira Ammi na" juyawa yyi ya fita dakin ya kulle mata kofa. Sai kusan karfe hudu da rabi ya dawo gidan yana haurawa sama ya bude dakinta daga kai tayi ta kallesa daga xaunen da tayi gaban mirror tana tsefe kitson kanta, yace "Kin ci abinci kuwa?" Ta ci gaba da abinda take tace "Na ci" yace "Me kika ci?" Tace "Ni dai na ci" yace "Gobe xa a kawo maki house maid sai ki dinga monitoring dinta tana girki" ta kallesa tace "A'a bana so, xan iya" yace "Ai ba ni na fada ba, daddy ne ya fada" daga haka ya fita dakin nata. Ta gama tsefe gashinta ta dau abubuwan wanke gashi ta shiga bandaki ta wanke gashin nata sannan ta fito ta busar. Kwanciya tayi saman gado maganganun da Ammi tayi mata daxu ya dinga dawo mata, ji tayi kamar ta fashe da kuka tunawa da tayi Ammi fa ce mata tayi bbu ruwanta dole yana da hakkin kula da Safeenah da cikin da tace tana da shi, ita ko kadan bata yadda Safeenah na da ciki ba ta rasa dalili, gashi duk hanyar da xata san ko suna waya ynxu bbu don tun ranan bata sake shiga dakinsa ba. Bayan isha Mujaheed na dawowa masallaci ya shigo bedroom dinta da ledan abinci, kamar ko da yaushe a dai dai wannan lkcn yau ma ta fito wanka ne, da sauri ta koma bathroom, ya ajiye mata ledan abincin ya fita dakin, ta gama shirin kwanciyarta har ta kwanta sai kuma ta mike ta dau ledan ta fita da shi, xaune ta gansa parlor ya bi ta da kallo ganin kitchen xata shiga yace "Kin ci abincin?" Tace "Am not hungry" mikewa yyi ya bi bayanta, ta ajiye ledan xata juyo suka kusa cin karo, komawa baya tayi da sauri ya dau ledan da plate sai cup ya kamo hannunta yace "You must eat, baxa ki kwanta haka ba" da mamaki tace "Ka ta6a ce min I must eat a gidan nan?" Bai tanka ta ba ya xaunar da ita ya debar mata abincin ya ajiye mata sannan ya xuba mata drink din ya ajiye yace "ki cinye yanxun nan Ina kallon ki" da mamaki take kallonsa, can tace "Ni dai nace maka na koshi" yace "I am not joking imaan, ki ci abincin nan ko kuma ki sha drink" shiru tayi tana kallonsa, can ta turo baki ta dau spoon ta fara cin abincin yana kallonta ko kiftawa bbu, da kyar take hadiyewa daga karshe ta ajiye cokalin ta mike tace "Ni dai na koshi" rikota yyi yace "Drink din fa?" ta xaro ido tace "Ni bana shan drink da daddare" ya hade rai yace "Take it now Imaan" dariya ya bata ganin how serious he is tace "Ni ka ta6a ganin na sha drink da daddare haka?" Yace "Ehh ki sha ko kadan ne" kamar xata yi kuka tace "Ni Yaya fa baxan iya Sha ba" ya dauka cup din ya kai five alive din bakinta yace "Bude bakin my friend" karba tayi a hannunsa kamar xata yi kuka ta kai bakinta ta fara sha, ya dinga kallonta har tayi rabi sannan ya saketa ya mike yyi wucewarsa sama ta bi sa da kallo ta ajiye sauran drink din.