← Book details Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 261 OF 300

Sashe 261

Eemaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*Imaan isn't for free* it's 300 via

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788

Mama Hadiza xata fito parlor suka kusa cin karo da Umma bakin kofa, Bin ta da kallo Mama Hadiza tayi ganin saurin da take yi kanta a kasa har ta shige parlor, Mama Hadiza ta tabe baki ta fito compound din, imaan dai ta kasa kallon direction dinsu kamar mara laka ta nufi apartment din su xuciyarta na bugawa, Mujaheed ya gaishe su, Hajiya Khadijah ta amsa a takaice, bai kara kallonsu ba ya wuce ciki walking slowly, Mama Hadiza na kallonsa ta amsa gaisuwar da yake mata, bai tsaya ba ya shiga parlor ya rufe kofar, Mama Hadiza ta nufi su Hajiya Khadijah tana masu sannu da xuwa duk da bata san su ba tace "Toh ku shiga ciki mana" Hajiya Khadijah tace "Mai gidan mu ke nema, Allah ya sa dai yana nan" Mama Hadiza tace "In ji dai lafiya Hajiya?" Hajiya Khadijah tace "Lafiyar kenan dai, wajen sa muka xo" Mama Hadiza tace "Ai kam bai nan...." Hajiya Khadijah ta d'an yi shiru sannan tace "Kaninsa fa?" Mama Hadiza tace "Wai lafiya Hajiya? I am their sister" Hajiya Khadijah tace "Sorry I didn't introduce my self, ni mahaifiyar Sadeeq ce, kin gane yanxu kuwa?" Mama Hadiza ta bude ido tace "Ohh Allah sarki sannu da xuwa Hajiya, to mu shiga daga ciki mana, sannun ku da xuwa" Hajiya Khadijah tace "Yauwa mun gode, amma tunda basa nan da mun tafi gun kakar Imaan din koh?" Mama Hadiza tace "Ehh toh mu je can din, ai tana nan" Hajiya Khadijah tace "Toh nagode" a tare suka tafi part din Inna da frnds dinta da Mama Hadixa dake gaba suna biye da ita, Mama Hadiza ce ta fara shiga parlon Inna da sallama, sannan su ma suka shiga, Inna ta fito daki rike da tsintsiya ta dinga bin su da kallo, sannu suka shiga yi mata gaba daya, bata tanka su ba ta nufi bakin kofa bayan sun shigo ta duka ta dau doormat tana kakkabewa a waje tace "Sannu kuma sai kace me ciwo ni patuu" Mama Hadiza tace "Inna mahaifiyar Sadeeq ce..." Mikewa Inna tayi da sauri tana kallon Hadiza tace "Wacece mahaifiyar tasa?" Mama Hadiza ta nuna mata, inna ta saki kabbara tace "Sannu baiwar Allah, lallai kin iya haihuwa, ynxu ke ce mahaifiyar wnn yaro me kirki da mutunta babba? Eh lallai Allah ya baki..." Hajiya Khadijah ta gaida ta with respect, frnds dinta ma duk suka gaisheta, Inna ta amsa tana washe baki tace "sannun ku da xuwa bari in debo maku ruwa" daga haka ta wuce kitchen ta dau faranti ta daura lemo biyu da ruwa biyu ta kawo ta ajiye masu tace "Gashi ku dau daddaya ku sha, Allah ya maku albarka" Hajiya Khadijah tace "Toh mun gode Kaka, dama gun mai gidan na xo bai nan, shi ma mahaifin Imaan din yana Abuja aka ce min" Inna ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Lafiya kuke nemansu?? Ba an mayar maku da kaya kunce a bar shi ba, to gasu can dai a daki ko tsinke ba a ta6a ba har ynxu a ciki" Hajiya Khadijah tace "A'a ba wannan ya kawo mu ba Kaka" Inna ta sake fuska tana murmushi tace "Toh madallah, me ya kawo ku kenan?" Hajiya Khadijah tace "Xuwa nayi, ga ni ga matar gidan nan, ga Mai gidan, ga mahaifin Imaan da mahaifiyarta su tambayar min ita ko mai ni da Sadeeq muka ta6a mata xata shiga ta fita ta hana aurensa da Imaan, idan kuwa tace babu... to Billahil Azeem xan dau mummunan mataki a kanta, in dai ina numfashi maganan nan baxai tafi a haka ba sai ta san ita ce silan bakin cikin d'a na, kafin in dau mataki nace bari dai in xo ku tambayar min ita ko Sadeeq ya ta6a mata wani abun ne...." Inna dake wurga ido tace "Ban fahimce ki ba 'yar nan? Wace matar gidan a ciki kike nufi??" A takaice Hajiya Khadijah tace "Uwargidan wan mahaifin Imaan, ita nake nufi" Inna tayi wani dariya murya can kasa tace "Toh Alhmdllh, ke ma dai an gano maki ita ta raba auren d'an ki da Imaan kenan? To na ji dadin xuwan ki gidan nan, na kuma ji dadin yanda kika tsaya kan d'an ki ba wasa, yanxu abinda xai faru 'yar nan hakuri xa ki yi har xuwa ranan lahadi duk inda uban Imaan yake dama xan kirasa ya dawo don a kan idonsa xa ayi komai, sannan Ahmadu ma bbu inda xai je ranan, duk xa mu hadu, ga ni, ga ki, ga autata Hadiza, ga uban Imaan, ga bafillatana uwar Imaan, ga ita matar da ku ka xo nema ga kishiyar ta, to sai ayi magana me ma'ana gaban kowa, da kanta xata bude baki ta fadi me tayi har yasa aka fasa wannan aure mai albarka kaca kaca..." Hajiya Khadijah tace "Toh nagode Kaka, Allah ya kara girma" Inna tace "Ameen yar nan" mikewa Hajiya Khadijah tayi ta ma Inna da Mama Hadiza da ta kasa cewa komai sallama ta nufi kofar, frnds dinta ma suka masu sallama duk suka fita, Inna na murmushi tana kallon Mama Hadixa tace "Toh Alhmdllh ba a bakina aka fara jin wannan xancen ba, Rukayya dai ta shiga uku ta lalace in matar nan ta fallasa ta gaban kowa har shi Bukar, sai kuma in xuba ido in ga matakin da Ahmadu xai dauka, shi kuma Bukar xan ga da wani bakin xai yi magana idan ya ji wannan abun al-ajabin" sai kuma Inna ta fashe da kuka sosai tace "Rukayya dai ta cuce mu, ta cuce mu, ta cuci jikata yanxu wannan mata da ta fita da ita ce surkar Imaan fa" Mama Hadixa ta sauke ajiyar xuciya ta dai kasa cewa komai duk jikinta yyi sanyi, a nan ta gane dalilin da yasa Umma ke ta sauri daxu. Tun da Umma ta shiga daki take kuka kamar ranta xai fita banda bugawa babu abinda xuciyarta ke yi, ta leka compound daga windown dakinta ya fi a kirga amma bata ga alamar mahaifiyar Sadeeq da Mama Hadiza ba, tasan kila suna can bangaren Inna, tunanin hakan yasa cikinta ya kara hautsinewa, don tasan shkkn mahaifiyar Sadeeq ta gama fada masu har gida ta je ta sameta ta 6ata Imaan da mahaifiyarta, sai xaga dakin take tana salati hawaye na bin idonta, da ta tuna ai sai dai su Abba su ji a bakin Inna ba dai directly daga bakin uwar Sadeeq din ba sai hankalinta ya d'an kwanta, gwara innan ta fada masu da bakinta, sun kuma santa da karin xance ko xa su yarda ba duka ba... Ammi ta dinga kallon Imaan bayan ta shigo parlor da mamaki tace "Daga Ina kike?" Imaan ta karasa da sauri ta rungumeta tana murmushi tace "Daga gida Ammi, Ina yini" Ammi ta daga kanta tana kallonta tace "Ina Mujaheed din?" Imaan tace "Tare muke, ya shiga gida" Ammi ta dinga kallonta sannan ta saketa tace "Toh sannu da xuwa" Imaan ta xauna saman kujera still smiling tace "Nayi missing din ki Ammi, Daddy yana Abuja koh" Ammi tace "Ehh yana can, bari in sauke abinci" daga haka ta koma kitchen, mikewa Imaan tayi a hankali ta nufi dakinta. Bayan Magrib Imaan na xaune tana cin abinci sai dai gaba daya hankalinta yayi kan Mujaheed ta rasa dalilin da yasa hakan, may be don ta san he is still sad ne and there will be no one to console him, a hankali ta dinga cin abincin duk da yanda tayi missing girkin Ammi amma turawa kawai take bbu appetite, Ammi ce ta fito parlor daga dakinta rike da wayarta tana kallonta ta karaso cikin parlon ta xauna tace "Imaan what's happening?" Imaan ta kalleta da sauri tace "Na me Ammi?" Ammi tace "Me yasa ku ka taho gida?" Imaan ta d'an Bude ido tace "Ya kawo ni ne kawai Ammi fa" Ammi tace "Ya kawo ki kiyi me?" Imaan tace "Ba komai, anjima xa mu koma" Ammi tace "Yanxu daddy ya kirani wai Inna ta kirasa ya taho gida ranan lahadi" Shiru Imaan tayi tana kallonta, dai dai shigowar Mujaheed parlon da sallama Imaan ta kallesa, ya karaso parlon yana kallon Ammi ya xauna kansa a kasa yace "Ina yini Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau, sannu da xuwa" yace "Ya gida" tace "Alhmdllh" Yace "Abba yana Abuja" tace "Ehh ya tafi" yace "Toh Allah ya dawo da shi lafiya" Ammi tace "Ameen" daga haka Ammi ta mike ta koma cikin daki, Mujaheed ya kalli Imaan dake ta kallonsa, sunkuyar da kanta tayi tace "Have you eaten?" A hankali yace "Yeah" ta kallesa tace "Nasan baka ci ba" ya d'an yi murmushi yana shafa kansa yace "Na ci mana" kallonsa ta dinga yi, ya mike yace "Dama Ammi na shigo gaidawa" Imaan tace "Xa kaje wajen Inna ne?" Girgixa mata kai yayi ya nufi kofa, ta d'an saci kofar dakin Ammi sannan ta mike da sauri ta bi bayansa. Har ya sauka balcony tace "Yaya" juyawa yayi ya kalleta, ta isa kusa da shi tana kallonsa, a hankali tace "Plss in debo maka abinci ka ci??" Ya matso da ita kusa da shi ya ja hancinta yace "Wanda na ci fa?" 6ata fuska tayi tace "Wllh baka ci ba, ni dai ka jira in debo maka" murmushi yayi a hankali yace "Toh debo min" Da sauri ta juya ta koma ciki, ya bi ta da kallo, direct kitchen ta shiga ta bude warmer din da Ammi ta xuba shinkafar da ta dafa, duk da bashi da yawa sosai haka ta debar masa ta sa masa stew da nama hudu, ta rufe warmer din ta juya xata fito taga Ammi tsaye bakin kofar kitchen din, ji tayi kamar ta nutse kasa kawai ta huta, Ta kasa kallon Ammi ta fara kame kame bakinta na rawa tace "Dama, dama abinci xan kai masa, Ammi shi ya tambayeni" Ammi bata ce komai ba ta karasa cikin kitchen din, Imaan bata yarda ta kalleta ba har ta fita kitchen din da sauri, tana shigowa parlor ta duka kusa da plate din abincinta ta dau nama biyu ta kara a nasa tana satan kallon kofar kitchen din sannan ta mike ta fita, bata gansa a waje ba, ta dinga bin compound din da kallo amma babu alamar sa, part din su ta nufa kamar me counting step dinta ta shiga parlon da sallama murya can ciki, babu kowa sai Tv dake aiki, taji dadin hakan sosai, sama ta wuce ta nufi dakinsa tana kalle kalle ta bude kofar, xaune ta samesa gefen gado yana danna wayarsa, daga kai yayi yana kallonta, ta shiga ta kulle kofar dakin ta karasa kusa da shi ta ajiye masa abincin ta hade rai tace "Shine ka wuce koh?" Jawota yyi jikinsa a hankali yace "Ba gashi kin kawo min har daki ba" Tana kokarin mikewa tace "Xan tafi kar Ammi ta dinga nemana" ya ki saketa yace "Ai a nan xaki kwana" xaro ido tayi ta kallesa sai kuma tayi dariya tace "Tabdi, ni dai ka sakeni in wuce Yaya" yace "Toh wuce da abincin ki baxan ci ba" shiru tayi tana kallonsa, sai kuma ta 6ata fuska tace "Ni wllh sai ka ci" yace "In dai ba nan xaki kwana ba kuma ki bani abincin a baki to baxan ci ba" xaro ido tayi tace "Toh babu spoon din bari in je in dauko a kitchen" ya matseta yace "Guduwa xa ki yi" tace "Ae nasan idan na gudu baxa ka ci ba, spoon xan je in dauko in dawo" yace "Toh je ki dauko" mikewa tayi ta nufi kofa sannan ta juya ta kallesa ta wara masa manyan idonta tana dariya tace "Kai ma ka xo part dinmu ka kwana mana" daga haka ta fice dakin.
Chapter 261 · 0% Book details